Chapter 13
Chapter 13
nan ko ? ...ya taba kirjinshi yana mata murmushi .. Bakinta ta gumtse kafin ta fara kyafta idanu tana kallonshi ..... Oh Sorry ...Taso muje kiyi wanka kici abinci...mu dawo na baki labarin Abunda Yaya Sa'armu tace na gaya maki ... Da gaske ? ...ta fada tare da fito da idanu .. Kai ya daga mata yana fadin ..."Yes ...muje "...... Ya mika mata hannu ta sauko .. Hanne dake tsaye tana kallon ikon Allah tace .."Wae Wacece wannan ? ... Kallonta yayi a fizge yana fadin . ".Hanne bara nayi wanka zamuyi magana kinji ko ..." Binshi tayi da kallon har suka shige part dinshi .... " Kutmar Uba...ban taba shiga part dinshi ba amma ya shiga da wancan ... " ..ta dafe kai tare da fadin ..."to ko dae kanwar uwarshi ce " Dae dae zai fito ya baro Huda tana wanka yaji tana fadin Kanwar uwarshi .... Shigowa yayi Falon yana fadin .."No Hanne ba kanwar Uwata bace ...Marainiya ce ta wuce duk yarda kike tunanin" Wani Uban tsalle tayi tare da mikewa .."Kuma dan Iskanci anan gidan ? A fizge ya kalleta yana murmushi yace " Ki rushe in da kika gina man !!! "Wallahi bata yiyuwa Yaya ...bamu gidan marayu " ...ta fada tare da zama kusa dashi Look Hanne !! ..kina son zama dani ? .. Gyad'a kai tayi tana kallonshi ... "Good ...to ki so wancan yarinyar ...." "kwana nawa zatayi ?...ta tambaya a hankali ... "Abadan da'iman".....shima ya fada a hankali .. "Amma ai nan da shekara 8 idan tayi aure shikenan ko yaya ? .. Kallon da ya sake mata ne ya sata yin lakwas ...tashi yayi ya shiga dakin ...Hudana Zaune bisa kujera da alama lokacin ta fito daga wanka ... "Come on ...kin yi alwala ? ....ya fada tare da fito da t shirt daga drawer shi ...red mai dogon hannu ya mika mata ... "Tashi ki saka kafin anjima mu je Super market a sayo maki naki ko ?.... Karba tayi ta sanya ...tazo mata iya guiwa ta mata kyau sossae ...ya kalleta yana murmushi .. "Ayehhh Hudata ..kinga yarda kikayi kyau ...come on ...na maki photo ? ... Uhm Uhm ...ka fada man abunda Yaya Sa'an tace ....tayi rau rau da idanu ... Hannunta ya kama ...tare da dukar da kanshi saitin fuskarta yana fadin ..."Sae kinci abinci sannan "...yaja hannunta suka fito falon ... Feedohm💞 💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_* 🍁 *_HASKE WRITER'S ASSO💡_* ( _Home of expert & perfect writers_ ) Na Feedohm💞 *_DEDICATED TO_* _EXCLUSIVE WRITERS...._ _*37 to 38*_ Still Hanne na zaune inda ya barta .... " Me kika hada mana lunch ?...ya fada tare da kallon Hanne ... "Lah Yaya bana fada maka ba tun shekaran jiya kaina ke ciwo .". .. "Good"...ya fada tare da fadawa kitchen ...yana janye da hannun Huda .. Zaunar da ita yayi bisa table din dake cikin din.....sannan ya kunna gas .... "Me kike so ki ci "...ya fada dauke da murmushi tare da kura mata ido ... Lumshe idonta tayi ba tare da tace komae ba ....Tabbas yasan Har yanzu Yaya Sa'a na ranta ....hannunta ya kamo ... "Hudallah ...zaki ci Indomie ? ... Girgiza mashi kai tayi alamar aa ..... "To me kike so ? ... Cous cous ..? nan ma girgiza kanta tayi ... Dago kanta yayi yana kallonta ..."Su kadae na iya Huda ...ya fada a hankali ...ko na soya maki Dankali? ... Bude idonta tayi da ya ciko da kwalla tana kallonshi ...Ganin zatayi kuka ne ya sakashi juya mata baya tare da kurawa Tagar kitchen din ido ...wanda a zahiri hankalinshi na kan yarinyar ...!! Da sauri ya juyi yana fadin ...Yaya Sa'a tace idan har Hudallah na kuka to barata taba samun sauki ba a ranta .... Share hawayen tayi da sauri tana fadin .." To idan na daina fa ? .. Idonshi ya lumshe ...."Allah zai sakata aljanna taji dadi sossae ",.. "To na daina kaji ...kace mata na daina kukan ...taji dadi sossae dan Allah ...kuma kaji kace har yanzu ina sonta ....!!! Idonta ya ciko da kwalla tayi saurin maidasu tana kakaro murmushin dole ... Rungumeta yayi tare da mata peck a goshi ...sannan ya daura tukunya ya zuba ruwan zafi tare da kayan miyan leda ya bata albasa ta yanka mashi ....cikin mintin kadan ya dafa masu indo mie da kwae ...ya juye masu a plate... Hanne ya kalla yace ..."Come and enjoy your lunch ...ya aika mata wani mugun kallo ... Tana son taci amma babu fuska duk da an mata tayin ....!!! ••°°•• Satin Huda Biyu gidan ta fara warwarewa ...Sae dae matsalan idan ya fita hanne ta sakata a gaba ...da zagi ... Tana zaune a falo ita kadae sae game take abunta tana dariya ....Hanne ta shigo tare da fizge game din ta wurga saman kujera ... Kunnenta ta murde ta zauna kusa da ita tana hararanta ... Da sauri Huda ta dafe kunnen tana ihu .... Bakin hanne ta buge tana fadin "wae ke dan ubanki idan Yaya ya shiga dake daki me kike ce mashi da kuke dadewa a ciki kuna dariya" Cikin jin zafi Huda tace ..."Fada mashi nake ke muguwa ce kullun idan kina zaune kiyi ta man tusa ..sannan bakya wanka !!! Wani uban rankwashi ta kai mata akae ...ihu ta sake da karfi .. Dae dae lokacin Mahmoud ya shigo falon ...jin Ihun Huda ya hanashi karasa sallamar ya shigo da gudu yana fadin... Hudah ...lafiya ....tsaye yayi yana kallon Hanne dake shafa kan Huda tana murmushi tare da fadin "Kai baby don na maki ci uku shine zaki man wannan ihu ".. Kallonshi Huda tayi kafin ta sake murmushi ta ruga da gudu ta fada jikinshi ...dagota yayi yana fadin.. "Hudah Game kuke ? .. Hanne ta kalla sannan tace "Eh Uncle Game muke irin na aunty muguwa ...Dan Allah Uncle' banda mugunta irin ta Aunty Hanne sae ta murde man kunne da karfi ? Hanne ya kalla duk tayi fiki fiki ...kafin ya maida idonshi kan Huda ... "Me kika mata? .. Feedohm💞 💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_* 🍁 *_HASKE WRITER'S ASSO_*💡 ( _Home of expert & perfect writers_ ) Na Feedohm💞 *_DEDICATED TO_* _EXCLUSIVE WRITERS..._ *_39 to 40_* Hanne tayi karaf tace .."Amma Hudah ke munafuka ce ...daga wasa ? ... Murmushi yayi kasa kasa ....sannan ya mikawa Huda ledar da ya shigo da ita ..."Jeki dauko littafin da na kawo maki jiya ..." Babu musu ta karba ta shige dakinshi da gudu ... Bai cema Hannen Komae ba ya koma ya zauna tare da lumshe ido ...ita da kanta tazo tana bashi hakuri ...sae dae yayi murmushi ba tare da ya bude idonshi ba ... Fad'uwar Hudah jikinshi ya sakashi bude idonshi yana murmushi ...Sossae ta zauna jikinshi ..ya karbi novel din yana karantawa .... ••°°•• Barister Shehu na zaune gida kusa da Hajiyarshi ..phone din shi ta dauki kara .... Kamar bara ya dauka ba ...ganin babban yaronshi dake kular mashi da kasuwar zinaranshi ce ya sashi dauka wayar .. "Hello ...Bello ya akai ",..ya fada tare da saka wayar handsfree ya daura saman hannun kujeran ... daga dayan bangaren akace "Oga wallahi wata mata ce tazo ta sayar mana da gold
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30