Skip to content

Chapter 17

Chapter 17

A Dalilin Yayata Complete Hausa Novel 1,145 words 0 views Progress saved
Download Book

kirji tana kallon hajiyar ... Katse wayar tayi tare da amsa sallamar tana murmushi ...hajiya dama irin mutannan ne masu son mutun mai kyau ... "Bak'owa shigo mana "...ta fada dauke da faraa don ta tabbata da ganin Huda ba diyar karamin mutun bace .. Dan murmushi ta sake mai burgewa tare da dukawa kusa da hajiyar tana fadin ... "Mummy ina wuni " ...ta fada kamar tana rada .. "Lafiya lau ..yarinya ...Tubarakallah ..daga ina haka ?,zauna sossae mana".hajiya ta fada tare da fadada fara'arta .. Hudah ta dan dukar da kai tana fadin.."Ayyah Mummyn mu baki sanni ba ..ai kawar Zahra ce ...tana ma nan kuwa ? Zahra. ...?...hajiya ta tambaya tana murmushi .."ae ko nan gidan ba zahra kila dae baa baki adress din dae dae ba ... Barister Shehu ya shigo tare da sallama...sallamar ta katse mashine ya tsaya cak tare da kurawa Hudah ido yana murmushi ... Ta gefen ido ta kalleshi ..sannan ta saka hannunta tsakiyar cinyoyinta tare da matsetsu tana bubbuga kafanta a hankali .."Oh Mummy ..wallahi na wahala sossae ,tun dazu fa nake neman gidan duk inda na shiga ba nan bane ..gashi phone dinta a rufe....OMG ..what should i do ? ..ta dan wurga idonta tana bata fuska kamar mai shirin kuka.... Barister Shehu yayi saurin shigowa falon tare da zama kujeran dake kallon ta Hudah yana fadin .."Mom bakuwa mukayine ? Murmushi Hajiyar tayi tare da fadin .."Wallahi kuwa Shehu gashi sae wahala suke bata har yanzu bata samu gidan ba !! Mikewa Hudah tayi tare da dage kafada tana fadin "anyway!! ..nagode mummy bara na tafi tunda banan bane .." Hajiya tace "Ki tsaya ko ruwa na kawo maki mana " Dan juyowa tayi tana kallonsu tare da lumshe ido ..."thanks ...." ta fada tare da juyawa ta fita da dan gudu gudunta ... Har tuntube Barister Shehu keyi gurin binta ...gabanta yasha yana fadin.." "Excuse please" Tsayawa tayi tare da kura mashi fararen idanuwanta .. "Please wa kika ce ma kike nema " Murmushi ta sake mashi tana fadin "Zahra Abdullahi ".. "To ko zaki bani phone numberki idan na nemo maki ita nan unguwar din sae na tura maki housenumber dinsu please !!...ya karashe maganar cikin ky'arma ... Kura mashi ido tayi ...ba laifi ya dan manyanta ra fada a ranshi ..."thanks ...ka barsa" ...ta fada tare da cigaba da tafiya ... "Please na rokeki da girman Allah .." ya fada kamar zaiyi kuka ... Cak ta tsaya tare da sakin murmushi ...takowa yayi har inda take ..ya mika mata phone dinshi ..hannunta da yasha jan lalle ta saka ta karbi wayar ta sa mashi numberta ... "Thank you so much beauty" ...ya fada cike da murna .... gaba tayi abunda ..da karfi yace .."please me zan sa " .. *_DAMSEL SA'ADAH.._* Ta bashi amsa kai tsaye tana tafiyarta ... Feedohm💞 💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_* 🍁 *_HASKE WRITER'S ASSO💡_* ( _Home of expert & perfect writers_ ) *Na Feedohm💞* *_DEDICATED TO_* _EXCLUSIVE WRITERS..._ *_51 to 52_* Sanin ta dade ne ya sakata bude kofar falon a hankali ...Tana sanda ....Mahmoud din ta gani zaune bisa doguwar kujera idonshi a lumshe ...san sadawa tayi a hankali zata shigr daki ... "Hudah ....ya kira sunan can kasan makoshi ... Juyowa tayi tana murmushin rashin gaskia tare da fadan ..."Uncle Allah mamansu lubna ta tsayar dani ..." "Su waye suka fita a motar lubna yanzu ? ...ya jeho mata tambaya.. "Uncle aikenmu tayi central market muka sawo mata salad...Allah kuwa" ... Bai kuma ce mata komae ba ...ya maida idonshi ya rufe ...ta dade a tsaye kafin ta shige dakinta ta canza kaya sannan ta fito ta wuce dakin Hanne ...isketa tayi tana gyaran gado ... "Aunty Hanne na dawo ".... "Ina kika je ne " .... Sae da ta kalli kofa sannan ta matsa kusa da ita tare da rada mata a kunne !! Dariya hanne tayi sannan ta daga mata hannu alamun jinjina tana fadin ..."Ki dae kular mana da kanki " .. Hararan wasa Hudah ta mata kafin tace .."Me zaa dafa yanzu ",.. "Ki dafa komae ...bara na ida gyaran dakin sae na fito nima "... Kitchen ta shiga ....ta bude fridge ta fito da kaza ta aje ..sannan ta dauko markadaddun kaya miya da sukayi kankara ta aje gefe guda ....electric gas ta kunna tare da a daura tukunya ta zuba man gyada tare da albasa sannan ta juye kayan miyan ...garlic ta bare ta saka tare da dakakkiyar citta da kanunfari .....ta rufe tukunyar ... Wata tukunyar ta daura ta saka kazan ciki da dan ruwa kadan tare da albasa da citta da spices ta rufe ....cabbage ta dauko ta yanka da carrot ....tukunyar da kayan miyan suke ta koma ...lokacin ruwan cikin kayan miyan sun tsane ..ta kara mai kadan tare da spices ...bata zuba gishiri ba don yana da site effect bare ma na buhu ...bayan mintina kadan kitchen din ya dauki kamshi ....stv fish ta dauko ta gyara sannan ta zuba cikin miyar tare da cabbage da carrot din da ta yanka...ta rage wutan ta koma gurin kazanta ...tana zuwa taga ta dahu sossae ...da yake kazan yana da mai ...ta zuba kuli kulinta a kai tana motsawa a hankali tare da albasa ...sae da kuli kulin ya bi kazar sossae sanna ta sauke ta juye a foodflask ....ruwa ta zuba ta dafa spaghetti tare da peas zallah ....komawa gurin miyar tayi ta sauketa tare da juyewa a flask ... Carrots ta wanke sossae tare da gurje bayanshi ..sannan ta yankashi kanana ta zuba a blender ta markadata ta tace sannan ta zuba sugar kadan tare da madara peak ta ruwa ...ta zuba vanilla ginger ...ta hada ...ta saka a fridge ta rufe ... Daki ta koma still Hanne na wanka ....Itama wankan ta yi ta shirya cikin pakistan riga da wando red ta fito ... Ganin Uncle Mahmoud baya falon ya sakata jera komae a dining sannan ta shiga ta ma hanne magana suka fito ... Hannen ta shiga dakin Mahmoud din ta iske ya fito daga wanka yana shiryawa ... "Looking good yaya"...ta fada tana murmushi ... Shima murmushin yayi kafin su fito falon tare ...lokacin Huda na zaune tana jiransu ...kujeran kusa sa Huda yaja ya zauna ba tare da ya kalleta ba .... Serving Huda ta masu sannan suka fara ci ....shi kanshi so yake ya kalleta amma baya so ta fahimci wani abu ...ga kamshin turarenta ya gama cika mashi hanci ....Kadan kadan Hanne da Hudah suke taba fira ... Abinci yaci sossae kafin ya mike ya barsu gurin ...site din da Hudah take ya juya lokacin da yake kokarin tashi ....itama shi take kallo ....Murmushi suka saki lokaci guda kafin tayi saurin dauke idonta a kanshi ....kadan ya dan taka kafarta ..sannan ya juya yacigaba da tafiyar ... ••°°•• twenty missed call ....ta fada tare da waro ido ... New Number ne ...ko baa fada mata ba tasan me ita ...tana kokarin aje wayan aka sake kira .... Sae da ta kusa katsewa sannan ta dauka tare da langwashe murya tayi sallama ... Tana jin lokacin da ya sake ajiyar zuciya sannan yace .."Haba damsel kin san yarda Hankalina yayi masifar tashi tun dazu nake

Table of Contents

Chapters

30 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30