Skip to content

Chapter 16

Chapter 16

A Dalilin Yayata Complete Hausa Novel 1,134 words 0 views Progress saved
Download Book

"Me naki Hudahta ...fada man kinji ko ..? ...ya fada cikin lallashi .. "Kaine ka rikewa Aunty Hanne Hannu mana !! ...tayi rau rau da ido .. Ido ya fito cike da mamaki yana kallonta ...kafin yace .. "Hudah Dan na rike hannun Auntynki shine kike fushi ..matata face ?.. "Nima din ai matarka ce !!! ...ta bashi amsa tare da kura mashi ido .. Murmushi yayi kasa kasa ..."Huda ke ba matata ce ...ke rayuwata ce kinji ko!!.. "Ba wani ! ...ni din matarkace ...tunda tare da aunty hanne muke tsare maka gida idan ka fita" ....ta fada tana hararanshi.. Feedohm💞. 💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_* 🍁 *_HASKE WRITER'S ASSO💡_* ( _Home of expert & perfect writers_ ) *_Na Feedohm💞_* *_DEDICATED TO_* _EXCLUSIVE WRITERS..._ *_47 to 48_* To wayace maki tsare gida shine aure!! Bata ce mashi komae ba ta mike ta fita daga dakin ....kitchen ta nufa ..insa yake aje mata dabino da biscuit tare da sweet ...ta debo sannan ta dawo lokacin yana shafawa kanshi mai .. " Karba kaci Uncle "...ta fada a hankali tare da mika mashi dabino daya .. Babu musu ya karba ya cinye ..sannan ta bare sweet ta mika mashi ..itama karba yayi ya shanye yana kallonta ...sae da ta bashi biscuit sannan ta duba aljihun rigarshi ta fito sa naira dubu ta hankade pillownshi ta aje ...sannan ta dawo kusa dashi tana dariya ... "Hudallah na me.. Hannunta ta daura saman bakinshi ... "Yi shiru Uncle ..dama nasan dan ban baka dabino da sweet ba shi yasa kace ni ba matarka bace ...to yanzu na baka ..har kudin da ake bawa amare kaga na dauko ko ...To dan Allah Uncle yanzu ban zama cikakkiyar matar Uncle dina ba ? ...ta langwabe kai tana kyafta idanu ...ita ala dole fari zata mashi yarda taga hanne nayi idan suna zaune a falo .. Dariya sossae yakeyi ...har sae da yaga ta fara bata rai sannan ya dan rage dariyar ..rasa abunda zai ce mata yayi ... Ya juya ya shiga distrnt dinshi ya canza kaya ...still yana dariyar ...fesa turare yayi sannan ya fesa mata tare da jan hannunta suka fita... Ko hanne bai ma bankwana ba ya fita da ita . Wani katon Moll suka je ya saya mata kaya sossae sannan suka fito yana janye da hannunta...sae da ya bude mata motar ya rufe sannan ya zagaya zaya shiga ... Har ta zauna sossae ..kafin ya kai ga shiga, ta fito da sauri tana fadin ... "Uncle yaya Sa'ata !!!..idanuwanta suka ciko da kwallah .. Barister Shehu ya gani dauke da safina zasu shiga moll din sae dariya yake yana gaisawa da wasu ... Da sauri yaja hannunta ya suka shiga motar tare ...gurin driver suka zauna su duka biyun ...tana lafe jikinshi tana hawaye ....baiyi kokarin tursasata tabar kukan ba ...sae dae hannunshi dake jikinta yana bubbugata a hankali ... ••°°•• Hanne me kike so maki dan Allah ? ...ya fada a fusace ... Haba yaya...me yasaka baka kulani ne ...ko hugging dinka nayi ka fara ja da baya kenan ...3yrs da aurenmu amma ko so daya baka taba sauke hakkin dake kanka ba !! Murmushin takaici ya sake kafin yace ." Me zan maki bayan halittar dake jikina ita ke tattare dake ..? Amma Yaya duk da nake maza mata ai akwae abunda ya dace kaman naji dadi nima " "Mace ya kamata ki nema ! ...ya bata amsa tare da barin daki ...!! °°••°° Shekaru nata tafiya ...sam Huda bata da matsala gidan Mahmoud ...idan tafiyar nesa ta kamashi zai dauketa ya kaiWa mamanshi har sae ya dawo sannan ya daukota ...wani sa'in ma cewa take gurin maman zata zauna don tafi jin dadin zama nan ...amma baya iya barinta ko kadan bai kaunar yin nesa da ita ko na second biyu ...ji yake kamar yayi loosing Something very important a jikinshi .....haka zaita lallabata har ya samu ta biyoshi ... Cikin ikon Allah Huda ta gama secondary school dinta ...lokacin duk wanda ya ganta bara ya taba tunanin Hudalliyar da bace ...Fatarta tayi fresh da ita ...cikar yan mata tayi ...kamar ita tayi kanta ...a lokacin shi kanshi Mahmoud tsoron zama da ita yake su biyu ....yayi baya sossae da ita ...haka itama ta shiga taitayinta ...!! ••°°•• "Uncle please dan Allah ,yanzu zan dawo wallahi ...please ka ji ? ...ta fada cike da shagwaba ... Kallonta yayi tun daga sama har kasa ...tana sanye da gown black ...sannan ta yane kanta da black gyale ...kaf jikinta ba inda ake gani ...kamar wata balarabiya ...kafarta sanye da plat shoes black ...sae yar jikkar dake hannuta black itama ... Feedohm💞 💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_* 🍁 *_HASKE WRITER'S ASSO💡_* ( _Home of expert & perfect writers_ ) *Na Feedohm💞* *_DEDICATED TO_* _EXCLUSIVE WRITERS.._ *_49 to 50_* Ganin ya tsaya yana kalllonta ya sakata hade hannuwata guri guda tare da dan dukawa kadan "please uncle " ...na tafi ?,... Da kai ya bata amsa tare da lumshe ido ...wani tsalle ta daka. tana dariya sannan ta fice da gudu ....ya bita da kallo.. Gidansu kawarta Lubna dake makwabtansu ta shiga ....ganin ba kowa a falon ya sakata shigewa part din su lubna ...lubna na kwance tana karanta wani book na Ummy A'isha *_WANI HASKE_* ...Awayanta ...taji kamshin turaren Hudah baki kofa... Da sauri ta juyo tana dariya ..."Zuwa ba alert "...ta fada cike da zolaya "Duba phone dinki daga CBN na turo maki shi tun daxu ..." Uhm ...ta Uncle Mahmoud ina zuwa wannan irin kwalliya nasan dai hakanan bara ki man irin wannan kyaun ba ... Baki Huda ta tabe tana kokarin cire gown din dake jikinta ...tare da jefawa saman gadon ... Lubna ta bude baki tana kalllonta kafin tace ... "amma wallahi Damsel kin cuci Uncle ...don munafunci shine kika sanyo wata gown a saman wannan shedanun kayan .." ina zaki ? Riga da wandone matsatstsu ...rigar iya karta guiwa mai gajeran hannu pink ...sae wando pencil black .... Tabe baki tayi tana fadin ... "dallah ban san gulma ni ki taso ki rakani ..". XIna ? ..lubna ta tambayi Hudah cike da mamakinta .. "Bana son wulakanci ..zan sayar dakene? ...ki taso mana ...bawae dan kina da mota ba ki tsaya ja man aji ...nasan mama batta nan har mun dawo bata dawo ba ...taso please ..!!! ...ta karashe maganar tare da yin gaba abunta ... Da hannu ta dingawa Lubna kwatance har suka isa tsohuwar unguwarsu ...ta gaban gidansu suka wuce ...sae da gabanta ya fadi ...inda yaya sa'a ke zama tana awara ta kalla ...yara zaune gurin sae wasa suke ...take idonta ya ciko da kwalla tayi saurin juyawa ta goge ba tare da lubna ta lura ba .. Gidansu ta kalla an rusheshe an hade da gidansu barister Shehu ..baki ta tabe ta kauda kai tana kallon waje .. Nesa da gidansu barister Shehu tace suyi parking ...sannan ta duba agogon dake makale a hannunta tare da fita da sauri tana fadin .. Excuse me please lubna !!!... Gidan ta fada cikin sauri ...direct part din hajiyar ta nufa ...sae da tayi gyaran murya sannan ta shiga ...hajiya na zaune bisa doguwar kujera..tana amsa waya .. Sallama tayi a hankali ta harde hannayenta a

Table of Contents

Chapters

30 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30