Skip to content

Chapter 12

Chapter 12

A Dalilin Yayata Complete Hausa Novel 1,138 words 0 views Progress saved
Download Book

tana kokarin tashi ya saka liman din riketa gam a jikinshi .... Kamar mai bacci take fadin.. "kace kar su tafi man da yayata!!...ina sonta ita kadae gareni ...Liman kaga ko Lauya shine ya ma Yaya Sa'ata Hard'e! ...mukaje gurinsu suka kara yankar naman jikinta ...sannan suka wullota ...Mamana ta rasu saboda Hard'e ...yaya Sa'ata ma ta rasu sabodashi ...Liman nima din ina so in masu Hard'e ...da lauya da babanshi da hajiyarshi ..zaka rakani ? Ganin ba cikin Hankalinta take ba ...sannan idonta a rufe yake ! ya sashi ..cewa "Zan rakaki kinji Huda !! .."Yaushe zamuje ..? Yanzu !!!...ta bashi amsa tare da rufe idonta ..bai kara ce mata komae ba sae addu'a da ya dinga tofa mata... *_JUST THE BEGINNING....😘_* Feedohm💞 💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_* 🍁 *_HASKE WRITER'S ASSO ...💡_* ( _Home of expert & perfect writers_ ) Na Feedohm💞 *_DEDICATED TO_* _EXCLUSIVE WRITERS..._ _*33 to 34*_ Tun daga lokacin Huda bata kuma magana ba ...kukan da takeyi ma ya tsaya cak ...sae ajiyar zuciya da take saki lokaci zuwa lokaci ...da marece Liman ya tafi da ita gidansu bayan kowa ya watse .... Bata iya bacci ba .. ta riga ta saba a jikin yaya Sa'a take bacci kulun amma yau ita kadae bisa katifa ...juyi ta dinga yi ...da ta rufe idonta barister Shehu take gani yana kallonta ...sae ta kai hannu zata kamashi sae ya sille mata ... Ranar ta Hudu ce bayan an dawo daga masallacin juma'a aka tsaya za'ayi addu'ar bakwae ... Lokacin Barister Mahmoud shima daga masallacin ya biyo ta gidansu Huda yaga yarda suke ....mutane sun taro sae addu'a ake .. Huda kuwa na zaune gefe guda ta daura kanta saman guiwarta ...yana gama parking ko fitowa baiyi ba ya kura mata ido tare da kiran sunanta .. Hudallah!!!!! Hankalinta baya duniyar gaba daya bata man san da zuwanshi ba bare ta san yana kiranta .....ganin bata da niyar kallonshi yada shi fitowa daga motar . .. Har yazo gabanta ya tsugunna bata sani ba ...sae da ya tallabo kanta sannan takalleshi da idanuwanta da sukayi jawur ... " Hudah ....menene ? ..idonki ke ciwo?...ya tambayeta a hankali .. Kamar jira take ta fada jikinshi tare da sakin kuka ....duk ya rude yana tambayarta ... Lafiya Huda? ...menene? fada man kinji ?...wani abu ya sami yayarki ?...Shiii yi shiru mana ki man magana please ..!!..ya fada a rude ... Ba tare da ta bashi amsa ba tacigaba da kukanta ....shafa bayanta yake a hankali ..yana so ta mashi magana amma ta kasa ..sae uban kukan da take ... Liman ya taso ya dafa bayanshi tare da yi mashi bayanin komae ... A tsorace ya kalleta da idanuwanshi da sukayi jawur ...kafin ya sakw rungumeta sossae yana bubbuga bayanta .... Suna nan tsugunne har aka gama addu'ar sannan aka fara shawarar wanda zai tafi da Huda gidanshi ...don babu wanda yasan dangin babanta bare a kai masu ita... Liman yace "Har ga Allah ina son daukar Hudallah amma ina tsoron uwar dakina ? ...sam bata kaunar taga wani ya rabeni sae ta dinga azabtar dashi ...kuma rikon Huda ba zai yiyo haka ba ...domin ita marainiya ce ta sha banban da sauran yaran da ake rikewa kara zube ....dole wanda zai dauketa .. ya guji kukanta da bacin ranta ...sannan kuma bazai saketa hakanan ba ....Saboda marainiya Mutun na iya shiga wuta !! ...Na tabbata uwar dakina bazata taimaka man ba mu riketa tsakani da Allah ba tare da cuta ba ..."..Amma dan Allah cikin ku idan akwae wanda ya tabbata zata iya zama gidanshi cikin farinciki ...wallahi nayi alkwarin duk wata zan bashi buhun shinkafa da taliya da jarkar mai da kudun cefane ...dan Allah wani ya taimaka !!! Mahmoud dake tsugunne yana jin duk abunda suka fada ....ya dago Huda daga jikinshi tare da share mata hawayen da suka wanke mata fuska .. "In je na dawo ko Huda ? ...zauna kinji ...!!! ..ya zaunar da ita sossae sannan ya tashi ya matsa gurin Yace "Malan za'a iya bani Hudallah ....na maka alkwarin riketa kamar uwa da diyarta ...sannan in Sha Allah barata taba kuka ba ta sanadiyata ....Dan Allah ku bani ita .." Liman ya dade yana kallonshi kafin yace "Wane unguwa kake Yaro ? ...kuma dama kasan su ne ? .. Cikin Sauri yace ..."na sansu wallahi ba tun yau ba ....nan take ya fadawa liman din address din gidansu .. Liman Yace "Alhamdulillah Mahmoud ai nasan mahaifinka ...duk wata yana kawo mana taimako ...na tabbata zata ji dadi gurinku !!! Godiya sossae yayi kafin ya koma gurin da Huda ke zaune .... "Zaki bini ko Huda ..zan baki rayuwa mai cike da jin dadi ..zan maye maki gurbin Yaya Sa'anki ...Muje ko? ..ya fada a hankali tare da tsugunnawa kusa da ita dagowa tayi a hankali tana kallonshi ...bakinta ya motsa ahankali sae dae bai ji abunda take fada ba ....gurin da su liman yake tsaye ta nuna mashi da hannu..... Tare da fadin ... .."Lauya" Feedohm💞 💧💧 _*A DALILIN YAYATA🍁🍁*_ 🍁 *_HASKE WRITER'S ASSO💡_* Na Feedohm💞 *_DEDICATED TO_* _EXCLUSIVE WRITERS....._ _*35 to 36*_ A hankali ya juya yana kallonsu ...Barister Shehu ya gani rike da wata takadda yana nunawa liman din rai a bace ... Da sauri ya mike ta rike mashi hannu tare da binshi suka isa gurin ... Cikin fada barister Shehu yake fadin "Dakata malan me ka sani dangane da wannan gida ...in jin nine lauyan ubansu tun kafin ya rasu ....to wannan gidan da kake wani hakilo akan basu sayar dashi ba ....to tun kafin uwarsu ta rasu ta sayar man dashi kuma ga shaidata nan"...ya mikawa Liman Takardar gida Barister Mahmoud ya karbi takardar ba tare da ya kalleshi ba ...ya budeta yana karantawa ...tabbas takardar gidan ce amma ya tabbata karya yake ba sayar mashi da ita akai ba !! Dan Murmushi ya saki kafin ya kamo hannun Barister Shehu ya damka mashi takardar yana fadin .. "Malan ku bar mashi ya tafi ....Barister har kayan dake cikin gidan ya kamata ka yi takarda don babu abunda zatayi da su ....A juri zuwa rafi "..... Ya juya tare da jan hannun Huda suka tafi ba tare da ya juyo ba ...Huda kuma tafiya take amma Barister Shehu take kallo ta kasa dauke idonta akanshi har suka isa bakin kofar .... Gaba ya bude mata ya sakata sannan ya koma ya shiga suka tafi !!! Falo suka iske hakima Hanne kwance saman kujera tana kallo ... Suna shiga ta mike da sauri tana dariya ..ganin Huda ya sakata matsawa da sauri tana fadin ... "Tsaya tsaya ...karki shigo ....yaya ina ka samo wannan yarinyar duk datti ...!!!...karki shigo bara na miko maki towel kiyi wanka a wancan tap din sannan ki shigo ...yaya yar aiki ce? .. Bai saurareta ba ya janyo Huda Har tsakiyar falon ...tare da dagata sama yana dariya ya zaunar da ita saman hannun kujera .... Juyowa yayi gurin Hanne yana fadin "Hudallah .. _Daugter ta ...Best friend dita .... Little sister ta ....Heart cherry ... My Queen _ ......Kin fahimta ? .. Ta gurin Mamanka kuka hadu ? ...ta tambaya a dakile Huda ya kalla yana fadin ... Hudah ta ina muka hadu ? ...ta

Table of Contents

Chapters

30 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30