Chapter 6
Chapter 6
ya daketa sabuwar zuwa ce ..... Huda kuwa girgije girgije take tana fadin ...yaya saa barshi ya tabani bai san Hudalliya bace ...yaro kaje unguwarmu ka tambayi yarda nake kada katti kasa ina duka ... Yaya Saa tacewa malamin ...dan girman Allah kayi hakuri ka barta tana da matsalar aljanu ne shiyasa bata ji.. Ido ta waro tana karkade kunne ....zuki ....Kai yaya saa dan dae kece da sae ince ...Mamanki ta saka man su ....amma kiyi hakuri kinji ko ... Bata ce mata komae ba taci gaba da bawa malamin hakuri wanda yace ...idan duk duniyace gatanta sae ya daketa tunda bata da kunya..... Ganin yaya saa na kuka ya saka malamin kyale Hudar .... Feedohm馃挒 馃挧馃挧 _*A DALILIN YAYATA馃崄馃崄*_ 馃崄 *_HASKE WRITERS ASSOCIATION馃挕_* Na Feedohm馃挒 *_DEDICATED TO_* _EXCLUSIVE WRITERS.._ _*Thank you so much sweet HAJJA....YAS鉂�..komae naki daban yake da na saura .....!..I Hhp am the first to wish you Happy birthday ASMY馃憚 ....WULLNP.....!..Best wishes UMMI A'YSHA..Kdeey ..Ayusher..Kubrieh CIE...billy galadanchi..Maman Khadija ...Asy darling ...khadeeja chafe ...Khadija candy ...jeedah Aliyu ..Billy BB...Nafee Anker.. Amnoor ... Queen Mermue ...IRSY馃槝*_ *17 to 18* Zaman Yaya saa gidansu barister Shehu ...Sae ya fara kawo mata salo daban daban .. Idan tana zaune inda take wanki sae barister shehu ya dinga zuwar mata da zancen banza ....tun bata kula shi har ta fara jin tsoronshi ...don tana zaune sae taji mutun ya shafa bayanta ...... bata taba fadawa kowa ba sae dae tayi ta kuka ....don kwata kwata bata jin dadin aikin yanzu ...Sae tana zaune sae Shehu ya dinga kokarin taba mata kirji ....Sae tayi niyar Barin aikin sae ta tuna da Huda dake makaranta .... Yau ma bayan ta gama wankin tana tsaye tana shanya kayan ...Shehu yazo ta bayanta ya rungumeta ....ta fara kokarin kwace kanta tana kuka ...yaki sakinta sae ma kokarin sakamata hannu yayi a cikin riga ....hajiyarshi ta leko tana fadin ... "Shehu wane irin shashanci ne wannan"...! ya juyo a firgice yana kallonta ....Yaya saa kuwa wani sanyi taji a ranta ta saka bayan hannunta zata goge hawayen ....cak ! ta tsaya lokacin da hajiyar ke fadin ...! "Idan sha'awarta kake bara ka jata daki ba sae ka tsaya waje salan uwarta ta fito ta ganka kuma ka ja mana tsegumi ".....! Bai jira komae ba ya fizgeta da karfi ya shiga da ita dakin dake kusa dashi ...wani ihu ta saki tana turje turje tare da hadashi da Allah ya barta amma sam yaki barinta ...sae da ya rabata da darajarta ta ya mace ....sannan ya janyota kamar kayan wanki ya wurgota waje inda take wankin ya koma daki..... Hajiyarshi kuwa tana shiga ta iske mamarsu Huda na goge goge ....tace mata.." ta tafi gida zata fita unguwa"..... Mama tace mata ...."To bara na kira Saadatu tana baya tana wanki ".... Hajiya tace ..."aa ki barta na aiketa nan makwabta ta karbo man sako" ... Mama tace ..."to Na tafi hajiya Allah ya kiyaye ".....! Yaya Saa lokacin da hankalinta ya dawo ta hade kai da guiwa tana kuka kamar ranta zai fita ....ga uban radadin da ke damunta ....haka ta ja jikinta ta fice daga gidan tana kuka ...... Zata shiga gida ta ga Huda ta dawo daga makaranta rataye da jikka .....baya ta koma ta lafe jikin bango gudun kada Hudar ta ganta tana kuka hankalinta ya tashi ...har sae da hudar ta shige gida sannan itama ta share hawayenta ta shiga gidan ... Bata bari Mama ta gane halin da take ciki ba ...sae dae Huda da ta kamata tana kuka bayan ta gama sallah isha'i ...! " Yaya Saa me aka maki ."...ta tabe baki ...nan da nan idonta ya kawo ruwa ... Jikin Hudar ta fada tare da sakin kuka ....Hudar ke girgizata tana kuka ...."Yaya Saa dan Allah kiyu shiru ...me aka maki dan Allah ....waya tabaki Yaya ...Yaya Saa dan Allah ki fada man ". Girgiza mata kai take tana kokarin tsaida kukan amma sam ta kasa ....ita da Hudar ke kuka kamar ransu zai fita ....Yaya Saa ta kasa fadawa Hudar asalin damuwarta ....tama rasa bakin da zata mata magana ...bata so Hudar taji abunda ya faru da ita saboda tasan Huda sarae zata iya rike abun a ranta har abada ... Mama ta shigo ta iskesu haka ...tambayarsu take meke faruwa amma babu wanda ya bata amsa ...da taga abun bana karewa bane ta zauna ta zagesu tsaf tace su mata shiru ko su fitar mata daga daki ...idan bara su fada mata damuwarsu ba ......Yaya Saa ta fara shiru sannan ta lallashi Huda da kyar ta samu tayi shiru ... 鈥⑩€⒙奥扳€⑩€� Karfe 3 na rana su Barister Mahmoud suka isa kauyen ....Kawu ya masu tarba mai kyau aka kawo masu madarar shanu da dambu ....Mahmoud kasa ci yayi sae dae yasha madarar kadae ... shi kuwa dady zama yayi yaci ya koshi. ...Inno ta shigo suka gaisa sannan ta fita ..Kawu yace "a kira Hanne "... *_Feedohm馃挒_* 💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_* 🍁 *_HASKE WRITERS ASSOCIATION💡_* Na Feedohm💞 *_DEDICATED TO_* _EXCLUSIVE WRITERS_ *_Nagode sossae da addu'o'in Ku Allah ya saka da Khairan💞_* *19 to 20* Kaninta ya fita da gudu ya kirata dandali.....Ko minti 10 baayi ba sae gata da tawwagar Yara sunzo ga nin mijin da zata aura daga birni .... Gaban Mahmoud din ta zube tare da kura mashi ido tana dariya .. sannan ta juya gurin kawayen tana fadin ....Kun ganshi nan irin mutumin nan na jikin Rigar dan mai gari ....!!..Wohoho no Hanne Duk kauyen nan albarka !! Hanne diyar kawu nalado ...irin mutanan nan ne masu shegiyar karya da iyayi .....bata cin abincin gidansu ta gwammace ta sayi malak'i ....saboda inno bata sanya masu kayan miya kamar yarda gidan maigari suke nasu girkin .!!...Irin yaran nan ne masu hange hange ..baka da gashin wacce kace sae kayi kitson wance ....!! Doguwace Jawur tana da kugu sossae da tsawon gashi ...amma kirjinta ba wani cikakke bane ....tun lokacin da kawu nalado ya fadawa Hanne cewa zata auri Mahmoud take ta murna don bata kaunar rayuwar kauye duk da acikinta ta tashi .....!! Sae ma ta daina hudd'a da yaran da take hudd'a dasu ya'yan talakawa kalarta... ta koma sae Ya'yan gidan Maigari da masu kudin kauyen take hudda ...!! Su Mahmoud basu tafi kauyen ba sae da aka daura aurenshi da Hanne .!!...duk da dama ba da shirin aure suka zo ba ...amma kawu Nalado yace ba abunda zasu jira ayi komae a gama su tafi da ita ....nan take suka bada sadaki aka daura ....su hanne sae murna ake ....Bangaran Mahmous kuwa tunda ya sadda kai bai kuma dagowa ba ...zufa ke biyo mashi ta ko 'ina ..."Innalillahi wa inna illaihir raji'un" kawae yake ..."Allahumma Ajir ni fi musibati "...kuwa ya furta ta tafi dari.!! ... wannan wace irin masifa ce ..!!!.abunda yake fada a ranshi kenan .....har aka gama daurin auren ....!! Ko a mota bai iya furta koda kalma daya ba ...sae Hanne dake ta karadi Abbah na biye mata ....!! Gidansu Mahmoud din ta zauna kafin ya ida gyara nashi ....Momy ba ta iya cewa komae ba sae fatan alkhairi data mashi .... ••°°•• Tunda Shehu ya ma Yaya Saa fyad'e bata kuma zuwa gidan ba ...haka mamanta kuma
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30