Skip to content

Chapter 26

Chapter 26

A Dalilin Yayata Complete Hausa Novel 1,146 words 0 views Progress saved
Download Book

farincikin da zata gani a idon yayar tata ... .... *FEEDOHM💞* 💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_* 🍁 *_HASKE WRITER'S ASSO💡_* ( _Home pf expert & perfect writers_ ) *Na Feedohm💞* *_DEDICATED TO_* _EXCLUSIVE WRITERS.._ *_79 to 80_* Wani sabon kuka ya zo mata ..yayin da ta sa hannu tana kokarin rufe bakinta gudun kada drivern yaji ta .... Ji tayi an janyota tare da kwantar da ita ...kamshin da tajine ya hanata firgita don har ga Allah bata dauka akwae wani a cikin motar ba bayan driver ... A kan kirjinsa ya kwantar da ita tare da bubbuga bayanta a hankali alamun lallashi ...ba tare da yace komae ba .... Lafewa tayi tana kuka kasa kasa ....Hannunshi ya kai tare da lalubar bakinta ya tura yatsunshi a ciki yana wasa dasu a bakinta .... Kukan ya tsaya cak sae dae ajiyar zuciya da take saki tare da kananan kwallah ...... Jin zaa bude motar ne ya sata tashi daga jikinshi tana gyara Saree dita .... Bude motar akayi tare da fito ta ...sannan Aunty hanne ta matso ta kama hannunta ...Uncle Mahmoud dinne ya zagayo tare da rike gudan hannun nata .... Pictures aka dinga dauka kala kala ....ga dandazon mutanen da sukazo taran amarya ...Ba gidan barister Mahmoud din bane aka kaita ...gidan iyayenshine ....zuwa gobe idan anyi walima su wuce gida .... Tare suka jera su duka ukun har tsakiyar babban falon Gidan ...sannan aka zaunar da Hudah din a kasan tuntu ...Shima barister Mahmoud din zama yayi gefenta ...har lokacin fuskarta na nannade da Saree .... Falon ya dauki haske ta ko 'ina ....yana zagaye da dangin Abba da kuma na mamanshi sae su biyu a tsakiya ... Yayar Mamanshi ce _Aunty Husy_ ta taso tare da aje yan kunne da sakar gold wanda ya kai naira million 15 ...kusa da Mahmoud ...na sayan fuskar amarya ... Gurin ya dauki tafi ganin Mahmoud din ya tura mata sarkar yana girgiza kai ...alamun bai sayar da fuskar Hudah haka ba ... Wata kanwar mamanshi _Aunty Zuby_ ta taso tare da cire tata sarkar da yan kunne ta hada mashi ta tura ...still tura masu yayi yana girgiza kai ...alamun bai yarda ba ... Gurin ya kara daukar tafi lokacin da mamanshi ta taso ta cire tata sakar da yan kunne ta daura mashi a saman tasu ... Sannan ya saka hannu ya dafa sarkokin tare da fara bude Fuskar Hudah Ahankali ..har sae ya kusa budewa sannan ya kalli kanwar mamanshi yana fadin "Gaskia Aunty Zuby ku karo wani abu tukun ..." Aunty Husy ta mashi dakuwa tare da watsa mashi harara .. Sannan ya bude fuskar duka yana murmushi ..... Kanta na a kasa tana kallon carpet din gurin .... "Masha Allah ...tubarakallah ..Alhamdulillah amarya ta hadu ta ko'ina ....fatan mu Allah ya bada Zaman lafiya!! ....Babbar yayar mamanshi ta fada tare da daukar su photo ....kamar an bude gidan photo haka flash light ke tashi gurin .... Sae da aka gama photo sannan gurin ya sake yin shiru ...Mahmoud dinne ya saka hannunshi na dama tare da dago fuskarta ...sannan ya goga hancinsa a lips dinsa yana lumshe ido ....duk uwayen mutanen dake zagaye da falon.. "Mahmoud baka da kunya ni wallahi ban ma san haka kake ba dae yau .."..kanwar Mamanshi ta fada tare da jehoshi da pillow ....Hudah kuwa yarda kasan ta nutse gurin haka take ji .. .. Murmushi yayi kasa kasa sannan kama hannun Hudah ..tare da rarrafawa kusa da kafar Mamanshi ... "Hudallah ki gaishe da Mama "...ya fada dae dae saitin fuskarta ... Dukawa tayi kusa da kafar maman ba tare da ta iya cewa komae ba ...bayanta maman ta dafa ..tana fadin .. "Allah ya maki Albarka Hudah ....! Kowa na falon sae da suka rarrafa ya na rike da hannunta yana fada mata sunanshi tare da matsayinshi ....ita kuma tana dukar da kanta a hankali ...suna sa mata albarka sannan suka dawo inda suke zaune ...duk abunda ake idon hudah na kasa bata dago ta kalli kowa ba ..... Bayan sun zauna ne babbar yayar mamanshi _Aunty Husy_ ta kama hannunta tare da kaita part din hajiya ta zaunar da ita saman gado ta fita .... kamar jira Mahmoud yake ta fita ya fado dakin tare da saka key kamar munafuki _nidae feedohm nace munafuncinne man_...ya zauna kusa da ita ya janyo ta jikinshi yana fadin ... "Hudah sun man bakinciki wae anan zaki kwana ....dan kada ace nayi rashi kunya wallahi dana saceki mun koma gida ko ? ... Banza ta mashi tare da sakin kuka ....kanta ya dago yana lallashinta tayi shiru amma sam taki yin shiru ....sae da ya fara kokarin cire mata Saree da aka lillibuta dashi sannan tayi shiru ... *FEEDOHM💞* 💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_* 🍁 *_HASKE WRITER'S ASSO💡_* ( _Home of Expert & Perfect Writers_ ) *Na Feedohm💞* *_DEDICATED TO_* _EXCLUSIVE WRITERS.._ *_81 to 82_* "Uncle ka fita dan Allah !!....ta fada tana kokarin tsayar da kuka ... Cikin sauri yace .."Idan na fita zaki bar kukan Hudah ...? Daga mashi kai tayi tare da sadda kanta kasa ....dan kiss ya mata a lips tare da jan hancinta sannan ya fita yana waigenta .....duk da yayan mamarshi tace anan zata kwana hakan bai hana Mahmoud ja mata Allah ya isa ba ... Allah ya soshi ba wanda ya ganshi lokacin sa yake fitowa don suna can suns kokarin hada mata abincin da zata ci wanda zai kara mata lafiya ... Su biyu suka shigo da abinci tare da zame malullubinta ...Aunty Husy ce ta bata abincin a baki ...tare da daura fuska ...don farko cewa tayi bara taci ba ...sae da ta daure mata fuska sannan ta amsa ... Bayan ta gama cin abunci yayar mamanshi ta hada mata ruwan wanka masu uban kamshi tace ta shiga tayi ...tana fitowa ta bata less red tare da head baki tace ta sanya ...da katuwar sakar gold ...sannan ta saka mata takalma hills bakake ...ta rufa mata bakin mayafi a kai ..tare da kama hannunta ..suka shiga part din Abbah ...yana zaune sanye fa farin glass suna shigowa ya mike dauke da fara'a yana fadin ... "Marhaban Hudallah" ....hannunta Abbah ya karba daga hannun Aunty Husy ya zaunar da ita bisa tuntu .... Aunty Husy ta miko mashi plate dauke da saubatussamina .......kadan ya diba a hannunshi sannan ya saka mata a baki...ta daukesu photo ....Fita tayi ta ta barsu su biyu .... Wa'azi ya mata mai ratsa jiki wanda ta tattaba ko mahaifinta na nan iya abunda zai mata kenan ...bata da abun ce masu shi da liman sae dae fatan Allah ya saka masu da alkhairi .. 12:30 .. Masu decoration suka iso ....kujeru suka fara fitowa suna jerawa a harabar gidan ... .sannan suka fara decorating din da yadi blue da fari ....gurin yayi masifar kyau kamar baa cikin gida ba .... Tana zaune Aunty hanne suka shigo ita da Aunty Husy suka bata Saree blue colour ....kaf jikinta sae da aka nannade idanuwanta kawai ake iya hanguwa ..... Fita da ita akayi falo ...acan taji muryar Uncle Mahmoud yana mayarwa da abokan wasanshi magana ..."wae duk family dinsu babu mai kyaun amaryarshi ......!! Gabanta ya fadi lokacin da taji tattausan hannunshi

Table of Contents

Chapters

30 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30