Skip to content

Chapter 2

Chapter 2

A Dalilin Yayata Complete Hausa Novel 1,166 words 0 views Progress saved
Download Book

da hannayensa a kirji ... Cikin borin kunya yace ...so what dan naci amanarta kanwar babata ce ...kai Mahmud zan iya komae akan kudi ... Ni kuma Barister Mahmud nace indae har ina raye bara ka taba wannan cin amanar ba .... Wae me ya shafeka ne da rayuwata ....kaga ka fita wannan maganar ...meyasaka tunda mijin nata ya rasu baka je ka taimakesu ba sae yanzu zaka zo kana man wani waazi ... Sabida ta yarda da mutumin da bai kamata ta yarda dashi ba....yana gama fadar haka ya matso kusa da table din shi ya dauki takardun da zai dauka tare da briefcast dinshi ya fita ... Tsaki Barister shehu ya sake kafin shima ya tattara nashi nashi ya bar office din ....daga nan gidansu Huda ya nufa kai tsaye ... Cikin lungun ya hango ana dambe da huda ...ta haye ruwan cikinshi sae jibgarshi take yara sae kara zugata suke ....yayi kwafa ...yana tunanin da itace ake duka haka to babu abunda zai kaishi rabasu ...yafi kaunar a kasheta kowa ya huta don da alamun yarinyar tana neman shigar mashi hanci ....da wannan tunanin ne ya isa gurin ...tare da fincikota ya dagata daga yaron da karfi sannan ya dauketa mari ....... Marin ya shigeta sossae ta dago tare da zuba mashi ido kafin ta dauki katon dutse ta jefawa glass din motarshi ta gama ......nan take glass din ya fashe ...ya juyo da azama amma kamar walkiya ta bace .....yayi kwafa tare da sake murmushin mugunta yayi sallama gidan ...da yake baida katanga da gidan ya fada ciki ba tare da shamaki ba .... Bayan sun gaisa yake fadawa mamanta cewa ....kudin sallamar aikin babansu Huda malan Ibrahim sun fito ...yanzu haka gobe yake shirye shiryen fito dasu banki sae ya kawo masu zuwa jibi ... Tace ...ka barsu hannunka lauya ...idan ka kawo mana ina zamu ajesu ...na tabbata bara ka cucemu ba ...don haka ka barsu hannunka ..sae dae ka dan bamu abunda zamu kara jari dashi dan Allah .. Murmushi yayi yace ...aa hajiya zan kawo maki su ki gani bayan kwana biyu sae nazo na karba ...don yanzu haka ina shirye shiryen saya maku da gida wanda zaa zuba yan haya a ciki duk shekara sae su dunga baku kudin ...idan na kawo kudin jibi to wanshekare zanzo da mutanen da zaku sayi gidan gurinsu sae a karbi kudin a basu .... To Amma ina tunanin inda zamu aje su Lauya ... Murmushi yayi yana fadin ...Allah zai karesu Umma ....ya mike yana fadin zan tafi idan huda ta dawo a ja mata kunne bata jin,magana yanzu daga rabasu fada ta fasa man glass din mota ... Ta hau sallallami tana bashi hakuri tare da fadin idan kudin sun fito dan Allah ya sayi glass din dasu ... Yace mata to ...tunda dama haka yakeso ..... 鈥⑩€⒙奥扳€⑩€� Barister Mahmud indae kana bukatar wani abu cikin kudin ka fada man bawae ka dinga man wani waazi ba na daban .... Wani kalan murmushi ya sake yana fadin ...nawa ne kudin nasu ... Yauwa dan gari ...10m ...ne ...zan baka 1m .....shikenan ko ... Dariya ya sake mai cike da maanuni daban sannan yace ...zan baka 10m ka bar masu nasu please Barister Shehu ya sake dariya yana fadin ....Am not a kid Barister baran taba cin kudinka na zauna lafiya ba ....nasanka sossae ...don haka kabar wannan uwar watsin ... Suma wannan sae ka basu kayansu ... Dariya yayi yana fadin gobe karfe biyar na marece zan kiraka na basu agabanka barister ....ya juya ya shige motarshi ... 鈥⑩€⒙奥扳€⑩€� Karfe biyar dae dae ya kira Mahmud ya mashi kwatancen gidansu Huda sossae yace yazo lungun gidan ya iskesu ...ko minti talatin bai cika ba ya shigo lungun .... Feedohm馃挒 馃挧馃挧 *_A DALILIN YAYATA馃崄馃崄_* 馃崄 *_HASKE WRITERS ASSOCIATION馃挕_* Na Feedohm馃挒 _*DEDICATED TO*_ _EXCLUSIVE WRITERS.._ 5 to 6 Motar Barister shehu da ya gani ya tabbatar mashi da yana gurin ...ya fito ya jingina da motarshi tare da harde hannaye ....kafin ya ciro wayarsa ...ya hango Huda janye da tunkiya da gudu ....yana gani ta shiga wani lungu sannan ta fito babu tunkiyar ta cire dan kwalinta ta daure a kugu ..... Wata tsohuwa ta shigo lungun da sauri janye da hannun wani karamin yaro .... Ke diyarnan yanzu akan naira shabiyar zaki kwanto man tunkiyar dubu sha biyar dan rashin mutunci.....tsohuwar ta fada tare nuna huda da Hannu .. Me ya saka da nace ki biyani kudina baki bayar ba ....idan kina son tunkiyarki wallahi sae kin bani kudina ...idan ba haka naje na sayar da ita na baki canjinki ....ta fada cike da tsiwa ... Tsohuwar ta kwantar da murya ...Haba Hudalliya ....na rantse maki da Allah da fatse ta dawo daga talla zan bashi ya kawo maki kudinki ..dan Allah karki sayar man da tunkiya .. Ta juya baya tare da dage kitsonta tana fito keya ...Nifa Innarsu Fatse dan karki ga na maki rashin kirki amma gaskia sae kin biyani kudina tukun na bada ... a ranta tace ...rashin mutunci kuma har nawa Hudalliya.....amma a fili cewa tayi ...iyakar mutunci kin man shi Hudalliya yanzu dae alfarma nake nema yar albarka ... Barister Mahmud dake kallonsu yana dariya har da rike ciki ya matso ya kama hannun Huda yana fadin ...nawa ne kudin naki .. Sarkin neman suna zaka biya mata ne ...ta bashi amsa tare da mashi kuri da ido .....sannan tace ...hala ba nan unguwar kake ba don ban taba ganinka waccen majalisar ba ta sa ido .... Naira Ashirin ya fito ya mika mata yana fadin ...karba ki sakar mata tunkiya ... Tsohuwar ta kalla tace ...Allah ya soki da na maki rashin mutunci .. Da dae taga an biya kudin sae cewa tayi .....rashin mutunci har na wana shegiyarnan ...... Oho dae ...huda ta fada tare da shigewa lungun ta janyo mata tunkiyarta ta koma .... Barister Shehu ya kira ya fito daga cikin gidan suka shiga tare ....gabanshi ya mikawa Mamansu Huda duka dukiyarsu a cikin jikka sannan ya mika mata makullen suka tafi akan gobe zai dawo da masu gidan da zaa saya .. da Suka fitone Mahmud ya mika mashi hannu cikin jin dadi da bai ci amanarsu ba sannan suka rabu ..... Wajen karfe goma na dare Wayar Barister mahmud ta fara kara ...lokacin suna zaune da family dinsu suna dinner ...ganin number barister Shehu ce ya saka ya dauka tare da sallama .... Barister Shehu yace ...Please ka sameni gurin gidansu wannan yarinyar akwae matsalane yanzu please .... okey ...ya fada tare da daukar keys ya fita da sauri ....yana isa lungun gidan yaga ba motar Shehu ya kira wayarshi ringing daya ya dauka sannan yace gashi nan ....da yake lokacin sanyine mutane duk sun shige gidajensu ....kofar gidan su Huda ya matsa ya zauna saman dakalin dake wajen .... Kaya yaga an watso mashi a jiki ....yayi saurin mikewa tare da daga tsumman da aka jeho mashi ....bindiga ya gani a ciki nannade ...da saurin ya daga cikin rashin fahimta ....ba dae wani abu akawa wadannan mutanen ba .. ya fada da karfi tare da kara daga bingidar ..... Flashlight din da ta dinga haskashi tare da karar daukar hoto ya

Table of Contents

Chapters

30 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30