Skip to content

Chapter 11

Chapter 11

A Dalilin Yayata Complete Hausa Novel 1,151 words 0 views Progress saved
Download Book

....sannan bata gaza ba gurin neman kudin da zata biyawa Huda Makaranta ba .... Barister Mahmoud kuwa kullun kokarinshi na yarda zai taimaka masu amma duk a banza ...don da Yaya saa ta ganshi zata tura Huda daki ta rufo ta dawo tana hadashi da Allah ya tafi ya barsu ....bama shi kadae ba duk wani namiji bata kaunar taga ko kallon Huda yanayi ... ••°°•• Feedohm💞 💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_* 🍁 *_HASKE WRITER'S ASSO💡_* ( _Home of expert & perfect writers_ ) Na Feedohm💞 *_DEDICATED TO_* _EXCLUSIVE WRITERS.._ *_Assalamu Alaikum ...wadanda suka man magana da dadewa akan na bude masu GRP nace masu banda ra'ayin haka ...to Alhmd na bude maku saboda wasu dalilai ...idan har yanzu you're interested sae Ku sake man magana👌🏻👌🏻_* *_Jaane kahan Keene pehesr zyada ..QUEEN MERMUE..NAFEE ANKER ...AMNOOR ...FEEDOH CLASSIC...AUNTY SIS ..MUM FATEEY ..SALAMATUN INNA ...AOH😘_* *_31 to 32_* Huda ..!!! Ya Kwala mata kira dae dae lokacin da yayi parking a bakin gidansu ... Ta juyo tana kallonshi kafin ta koma da gudu ta janyo kofar gidansu ta saka dankwalinta ta kulle kofar ta dawo gurinshi tana hararanshi .. "Wae kai ina zuciyarka take ? Kirjinshi ya dafa yana murmushi ..."Tana nan Huda !! baki ta tabe tana fadin .."ni na dauka baka da ita ...banda k'wak'wa kullun yaya Saa na fada maka ka daina zuwa gidanmu amma sae ka janyo wata motarka kazo kana washe baki ..." Murmushi yayi ba tare da yace mata komae ba ... "bara kayi magana ba ...to Na rantse maka da Allah duk ranar da ka kara zuwa ka saka Yayata kuka sae naje har gidanku na saka Yayarka kuka itama .... Zagayowa tayi tare da bude Marfin motar tana fadin..."Zo ka shige ka tafi ko na maka rashin mutunci ....!! zuwa yayi kamar zaya shiga sae kuma ya hade hannayenta guri guda ya dagata ya daurata saman motar tare da dungure mata kai yana fadin ... "Bakya da kunya ko Huda ..? ..ni zakiwa rashin mutunci ? ...ya hade fuska Daga kasan kafafuwanshi ta fara kallo har zuwa kanshi ..saman ta hadiyi miyau da kyar tana kallonshi ...ganin tsoro ya bayyana a fuskarta ya sashi sake daure fuska yana kallonta ... "Ni zaki wa rashin mutunci nace maki ? "Allahu" ...ta juyar da kai kamar saliha ...dariya taso bashi yarda take zare idanu ga fuskar bayin Allah da ta koma ..amma ya dake yana kallonta . "Oya ...yiman rashin Mutuncin nace !! "To dan Allah idan nace kayi Hakuri fa ? ...ba sae ka saukeni ba na tafi gida ...sannan kullun kazo ni kuma na dinga gaidaka ....saukeni ka gani yarda zan dinga maka ..." Sake mata hannu Yaya tare da ja da baya ...tsalle tayi ta dira kasa tana washe baki ...sannan ta hade hannayenta guri guda .. "Kafana ma k'aikayi take man ....bara na sosa kaji ? ...ta fada tana kalloshi tare da murmushi .. Dukawa tayi tana sosa kafar tata ...ta dago a hankali ta kalleshi taga hannusa a harde kamar ba ita yake kallo ba ...da sauri ta rarumi kafarshi da niyar ta kadashi kasa ...amma sae ji tayi kamar icce ko alamun yasan abunda take baiyi ba .... Ta dago tana hararenshi suna hada ido ta washe baki tana kakkabe hannu ."Har ga Allah ni bama niyar kadaka nayi ba " ... kafin ya bata amsa ta ...ta bar gurin da gudu ....dariya yayi ya bude boot din motarshi ya fito da kayan abincin da ya zo dasu ...sannan yayi waya ...wasu mutane guda Uku sukazo mata...ya basu kayan abincin sannan ya shiga motarshi ya tafi ... Matan suka saka yara tare da daukar masu kayan abincin suka kai cikin Gidansu Huda ...yaya Saa na zaune tsakar gida taga yaran suna ta shigowa da buhunna ...bude baki tayi tana mamaki ...kafin tayi magana taji Huda na fadin .. "Wallahi yaya Sa'a ko kayan waye wannan bara mu bashi ba ...tashi mu kaisu Daki mu boye tun kafin maisu ya shigo nema ...Dan Allah Yaya Sa'a tunda muma an taba yi mana fashi ba sae mu rama ba mu dauke kayan .... Kafin ta rufe baki Matan sun shigo ..tsalle daya Huda tayi tare da tara hannu tana kange kayan tana fadin .. "ba Wanda ya isa ya daukesu tunda bamu mukace a shigo mana dasu gida ba ..." Wata daga cikinsu tayi murmushi tana fadin ...dama ai naku ne Diyata ...daga gidan marayu muke aka baku Taimakon da ake yiwa Marayu ... Murna kamar me gurin Yaya Sa'a ...godiya ta dinga masu har da kuka ...bayan sun tafine Huda ke cewa ... "Yaya Sa'a mu dafashi duka idan mun ci sai mu aje sauran ...yarda ko wadannan barayin sun zo bara su iya dauka ba ...kinji .." Yaya Sa'a tace ...Huda ba yarda za'ai mu dafa shi duk kinji ko ...idan ma sun zo sun dauka Allah da ya bamu wannan zai sake bamu wani !!!! ••°°•• Huda na JS2 ..cikin Yaya Sa'a ya cika wata tara ...ranar kasa bacci sukayi ...Tun cikin dare take nakuda ..Huda ke ta mata fita tare da Sannu ....ana kiran asuba ta fita da gudu ta kira liman tace yayanta bata lafiya ... Tare suka dawo cikin gidan ..lokacin Yata Sa'a ta wahala sossae ko Bude ido bata yi ....Banda Kuka babu abunda Huda ke yi ...har aka dauketa aka tafi da ita asibiti ... Basu isa asibitin ba Yaya Sa'a ta rasu saboda deep labour din da tayi sannan jininta duk ya fita sossae ... Tana ganin an juyo zaa dawo ta rike hannun liman din tana fadin "Dan Allah karmu koma ...bata lafiya sossae ko magana bata iya man ...duba liman yayata idonta ya rufe ...dan Allah mu tafi asibiti ...ina sonta ...karmu koma liman ..wallahi da munje asibiti zan fita nayi bara na samo kudin sae na bayar da kudin ...ni bana so tasha wahala .!!!...ta fada jikin yaya saa tare da fashewa da kuka ... Duk wanda ke motar sae da yayi mata kuka ...ko da suka isa zaa fitar da yaya saa daga mota kin sauka tayi daga jikinta sae dae aka daukesu tare ... Bayan an aje ta ne Zaa Mata wanka liman ya rugumota jikinsa ...ya ma rasa me zai ce mata ...ya tabbata duk wanda ya hana Huda kuka ya cuceta !!! Tana jin wani na fadin Ta Rasu ne ...tayi sauri fizge kanta daga jikin liman tana fadin ...Ta rasu kamar Mamata????..Barata dawo ba?. Da Sauri Liman din yace ...bata rasu ba Huda !!! .. Hannushi ta kama tare da daurawa jikin Yaya Saa tana fadin ... "Yauwa Liman ...to tadata ...kace mata Hudanta na kuka..bata son kukana fa ...nasan zata tashi .liman ka tadata Dan Alllah !!...yaya Sa'a tace fa ...kace ta tashi' ko kukan ta ma naji zanji dadi ...Dan Allah ki tashi ...!! Da kyar liman din ya fita da ita daga dakin yana kuka .....babban tashin Hankalinsu yarda zasu fitar da gawar daga gidan ba tare da Huda ta gani ba ...!!! ... NO WAY OUT ...Haka suka dauko gawar Yaya sa'a ..lokacin Huda na jikin Liman a waje tana kuka...kowa ya tabbata da tayi rashi ...RASHI BABBA !! ...wanda babu wani mahalukin da zai maye mata gurbin Yaya Sa'arta !!!! Ganin

Table of Contents

Chapters

30 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30