Chapter 7
Chapter 7
bata takura mata...sae dae tayi tambayar duniyar nan ta fada mata me ke damunta .....! Bayan wata daya ne Yaya Saa ta fahimci tana da ciki ...domin har lokacin menstruation din yazo bata ganshi ba ...sannan ga wani canji da take ji a jikinta .... Hankalinta yayi bala'in tashi sam bata da sukuni duk ta bi ta rame kullun cikin kuka take ...ga bala'in tashin zuciya da take ...abun kadan zaya sakata amai ... Tana tsugunne a kewaye tana amai gidan ba kowa ....Taji an dafa mata baya ...ta juyo a firgice tana kallonta ...ganin Huda ce ya saka ta sake a jiyar zuciya tare da janyo buta ta wanke bakinta ta mike ... Daki suka shiga Huda na rike da hannunta ta zauna saman gado tare da kara janyo Hannunta tana fadin ..! "Me ya sameki Yaya Saa ...sannu kinji" ...cikinki ya kumbura ?....ta fada tare da kura mata ido... Hawayen dake fuskar yaya saa suka samu damar gangarowa ....tana girgixa kai ... "Kiyi Shiru mana Yaya Saa ...me kika ci ya kumbura maki ciki...bara naje gidansu Fatse na karbo maki maganin kumburin cikin kinji ko ...sannu" .....ta mike da niyar fita ...! Yaya Saa tayi saurin kamo hannunta tana fadin ..."Hudallah ! ... " Na'am Yaya saa" ...menene ko tafasar jiya ta bata maki ciki ...?. Girgiza mata kai tayi tace ..."Huda maganin da kike kokarin karbowa bara ya iya man magani ba !!... Dariya tayi ..."haka zaki ce Yaya saa bawae ki rikeni ba ! .."to bara na kira mama gidansu lauya sae mu kaiko asibiti su baki magani ...sae su rubuta sunana idan na gama makaranta na fara aiki sae na biyasu ko? ....ta mike da sauri ... "Tsaya Hudallah "....ta fada a hankali ..."karki fadawa Mama hankalinta zai tashi kinji ko ...ki barshi tsakaninmu karki fadawa kowa ina amai" .. "Sirri Yaya Saa ..!!....ta fada tare da dafe baki tana waro ido ...! "Sirri Hudallah!! ...ta bata amsa.. ""Sirrin Amai !!!...ta kara tambaya cike da mamaki ...! "Bara ki iya rike sirrin yayarki ba Huda ?... "Zan iya mana Yaya Saa ...ko mama baran fada mawa ba ..sae ma nacewa mutane Yaya Yar baiwa ce bata amai ....Sannu kinji Yaya saa ..Allah ya baki lafiya ...Allah ya isarmu mai tafasar nan da ta sayar mana ...muguwa shi yasa naga tana kallona ...kila ma ni taso cikin nawa ya kumbura."..!! Bata ce mata komae ba ta mike ...surfen da aka kawo mata ne ...ta dauka tayi ...sannan ta bawa Huda kudin ta saka Jikkarta ta makaranta gobe tayi kudin Tara...!! Feedohm💞 💧💧 *_A DALILIN YAAYATA🍁🍁_* 🍁 *_HASKE WRITERS ASSOCIATION💡_* Na Feedohm💞 *_DEDICATED TO_* _EXCLUSIVE WRITERS.._ *_21 to 22_* Hanne!!!...irin matannanne masu shegen kilbibi da karya ....watanta biyu gidansu Mahmoud ta waye ta goge kamar ba ita ba ...kafin kace me tayi kawa makobtan gidan ....mai suna Saly ...haduwarta da Saly sae idonta ya sake budewa ...don kullun saly na gidansu Mahmoud tana kara budewa Hanne Ido ...kadan kadan sae ta fara zabgawa Maman Mahmoud Rashin kunya ....sannan idan an dafa abinci bai mata ba sae ta saka a sake dafa wani a zubar da wancan ... Abun ya fara damun Momy gashi bata son ta fara kai karar Hanne gurin Abba ...sae yaga kamar bata son zama da ita .... Momy na zaune ta rabka uban Tagumi ...Abba ya shigo tare da Mahmoud suna fira kadan kadan ....Hanne ta sauko daga upstair ta tsuke da riga da wando three quarter .....tana ganin Mahmoud ta sake fuska tare da tahowa tana murmushi .. Babu kunya tayi niyar fadawa jikinshi ...wani kallon ya sake mata babu shiri ta sulale kasa tana gaida Abba .... Abba yace " Hanne ki shirya zamuje kauye an kirani babanki baya jin dadi .." Ta hade Fuska tana Fadin "ni gaskia Abba baran je ...idan kunje ku gaidashi .." Akan me? ...Abba ya tambaya cike da Mamaki ... Gaskia Abba yanzu lokacin damina ne ...nasan gidan duk ya kazance da kashin goat da cow da chickenks ...kuma inno ba iya gyarawa zatayi ba ...ni kuma baran je wari ya isheni ba ... daga Momy har Mahmoud sakin baki sukayi suna kallonta ...Abba kuwa dariya ta bashi ..wae Goat da cow da chickenks . .. Hanne Manya...!! ...ya fada lokacin da yake kallonta ... Mahmoud yace " Abba da yaushe zaa tafi ?...fuska daure Gobe Mahmoud ....ya bashi amsa ... Ke !! ...ki shirya gobe da safe zamuje kauyenku!!!,...ya mike ba tare da ha sauri kowa ba ya shige daki ... Momy kuwa cewa tayi ." Allah ya kyauta .." ..sannan ta mike ta fada kitchen itama ... ••°°•• Maman Huda na tsaye tana goge goge .. Barister Shehu ya fito daga daki fuska daure ....ya zauna bisa kujeran da take kallonta ... Malama ...daga yau karki kuma zuwa aiki nan gidan an sallameki !!!!...ya fada tare da daukar remote yana latsawa .. Maman Huda tayi sararo tana kallonshi cike da mamaki kafin ta danyi murmushi tace .,." Lauya wani abu ya faru kuma ?... Lokacin da nace kizo ki dinga taimakawa Hajiya kin tambayeni dalili? ...ya bata amsa yana kallonta ... "To ....Me yayi zafi Haka lauya ? ..."bara na samu Hajiyar idan wani abu nayi mata sae na bata Hakuri "... Ba sai kinzo ba ...!!..gani nan fitowa ....hajiya ta fada lokacin da take fitowa da part dinta ... Sannan ta ci gaba ..." Da kike son zuwa gurina ...dama ni daukeki aikin ? ...ina jin Shehu ne .. kuma yace ya sallameki to meye na sauran magana ? ... Maman Huda tayi tsaye rike da tsumma tana kallonsu ...a iya saninta babu wani abun da ta aikata ba dae dae ba ...ta ko don Saadatu ta daina zuwa ne? ...ta tambayi kanta arai... Tace "Kuyi Hakuri Hajiya idan dan saadatu ne wallahi har ga Allah bani na hanata zuwa ba ..!! ... Wake maganar sakaran yarinyarki yar iska...!!! ...Hajiya ta katseta tare da zabga mata uwar harara ... Yar iska ....?...ta fada lokacin da idonta ya ciko da kwalla ... Eh Yar 'iska matsiyata ...barister Shehu ya bata amsa ... Wallahi diyata ba yar'iska bace sae dae kaine dan iska ...arziki da talauci duk na Allah ne ...!!!ta basu amsa a fusace ... Bata rufe baki ba Hajiya ta dauketa da Mari tana fadin .."Allah ya mana katanga da talauci ...fice mana daga gida tun kafin na saka a futa dake ...bara kizo har gida ba kina kiran dana dan'iska na zuba maki ido ba ....kama hanyar akurkunki tun kafin na sakashi ya maki shegen duka gurinnan... Allah ya baku Hakuri ...Abunda ta fada kenan tare da fitowa daga gidan ....ko gabanta bata gani sossae har ta isa gida ... Ganin yanayinta ya saka Yaya Saa tayi saurin kamota tana tambayarta lafiya.. Lafiya mama ...me ya faru ?..me suka maki..?...ta tambaya a rude ... bata boye mata komae ba ta fada mata duk irin wulakancin da Barister Shehu da hajiyarshi suka mata ...daga saa har Maman kuka suke kamar ransu zai fita .. Huda dake tsaye jikin kofa tana jinsu ....ta fita da gudu .. Feedohm💞 💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_* 🍁 *_HASKE WRITERS ASSOCIATION💡_* Na Feedohm💞 *_DEDICATED TO_* _EXCLUSIVE WRITERS..._ *_23 to 24_* Ta fitaa da gudu daga gidan ... ..bata
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30