Skip to content

Chapter 21

Chapter 21

A Dalilin Yayata Complete Hausa Novel 1,127 words 0 views Progress saved
Download Book

magana da dad ...yace zaa turo gidanku ...!! Ba tare da tace mashi komae ba sae juyawa da tayi tana daga mashi hannu .... Dakin Lubna ta fada tare da fashewa da kuka ... "Damsel menene ? ...wani abu ya maki ...ko cewa yayi baya sonki ....please kiyi magana mana !!! ..ta fada a rude tare da rike kafadarta ... "Uncle Lubna ...Uncle ya ganni da mutumin da ya fi tsana a duniya ....!!! ..ta fada cikin kuka ... " Ina ya sanshi Damsel ? ...ya akai kika san baya kaunarshi ...? ..shin uncle din ya maki magana ne ? ... "I know everything a tsakaninsu lubna ...wanda shi kanshi uncle din bai san na sani ba ...!!! "Kinga damsel kije kiyi magana da Uncle din mana ...may be ma shi bai dauka da wata manufa ba ....!! Ba tare da tace komae ba ta dauki zunbulelen Hijab dinta ta saka sannan ta fita cikin sanyin jiki ...yarda taga yayi parking din motar sae da gabanta ya fadi .... Tana shiga falon ta iskeni tsaye hanne na tsugunne sae uban bala'i yake mata .....fuskarnan tashi jawur kamar an saka mashi ruwan zafi . ... bai bari ta shigo sossae ba ya shakareta tare da wurga ta saman kujera ...kafarshi yasa ya take mata ciki ...Uban ihu ta sake tana hawaye ... "Kinsan Uban waye kike tare dashi !!! ...ya fada cikin tsawa ... ihu ta sake ta kasa magana saboda wuyanta da ya shake ...hanne ta taho tana rikeshi tare da kuka .. "Dan Allah ka barta " ...kar ka kashe masu yarinya " ...haba ya....Wani uban mari ya sake mata tare da hankadata gefe guda ...!! "Bansan baki da hankali ba sae Yau Hudah ...kin san da uban wakike tare ...fada man tun yaushe kike soyayya da wannan banzan ....!! Batace komae ba sae uban kukan ta take mashi .....dukanta ya fara yi yana tambayarta ...amma bata masa magana ba ... Ganin kamar kara haukacewa yake yana sabbatu ya sata kokarin kwatar kanka ....fa kyar ta mike daga inda take ....da gudu ta ruga zata shige daki ...kafa ya saka ya tadiyeta ta fadi kasa da karfi ...bakinta ya fara fitar da jini ...still fizgarta yayi da karfi ta mike tsaye ya hadeta da karfi ...Hanne kuwa Kuka take iya ranta ...gani take kamar yazauce .... "Wane irin so kake mata Yaya ...wanda yasa zaka iya kasheta don ta tsaya da wani namiji ? ...Hanne ta fada tare da rike mashi hannu tana kuka ... ita da Hudah ya hade guri Guda ....Kamar garwashi haka Hudah ke ji a ranta ...barata iya daukar wannan dukan ba anymore ....bata san tana da karfi ba sae yau ....Hannun Uncle Mahmoud din ta rike tana kallonshi tare da angazashi baya da karfi ... "ka daina Uncle !!! ....ta fada cikin tsawa ...tuni idonta ya bar zubar da kwalla ya bushe tare da sauya kala ... Yarda tayi tsawar ya sakashi kallonta shima ... "Ka dauka ban san Waye Barister Shehu ba ? ...to na sanshi ...sanin da shi kanshi wawan bai wa kanshi ba ...ko ka dauka soyayya nake dashi ...!!! ...ta kareshe maganar cikin tsawa ... Daga Uncle Mahmoud din har Hanne tsayawa sukayi suna kallonta ... "Mutumin da yayi sanadiyar rabani da Mahaifiyata ya rabani da yaya sa'ata ...a tunaninka shi zan so uncle ? ...Juyar da kanta tayi ga barin kallonshi . ..."ya ma yayata Fyad'e ..mukaje gidan Ubanshi yace ya sake mata idan yaso....a gaba suka wulakanta ta ...Anan Mamarmu ta rasu tsakar titi Uncle ...yaya Sa'a ta samu cutar HIV..shin kasan wacece yaya sa'atah? ..sannan kake tunanin ya ci bulus Kenan ? .. *_A DALILIN YAYATA_* na ke tare dashi ...hakan yasa na rasa Mamata ...Uncle shine ya kawo mana dukiyarmu ta gado sannan ya biyo dare da yan fashi suka sace *Harda kai ciki Uncle*!! .....ta fada tare da nunoshi da karfi.... *FEEDOHM💞* 💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_* 🍁 *_HASKE WRITER'S ASSO💡_* ( _Home of expert & perfect writers_ ) *Na Feedohm💞* *_DEDICATED TO_* _EXCLUSIVE WRITERS.._ *_65 to 66_* Baya yayi tare da fadawa saman kujera yana kallonta ... "Hudah ...!!... ya fada a firgice .. "Quite Uncle !!! .....ko zan manta idon kowa baran mata idon mutumin da na fada jikinshi ba lokacin da Shehu ke kokarin dauki jikkar kudin ... .Da zoben dake hannunka na kara tabbatarwa lokacin da kazo gidanmu da safe Uncle ..idan har zaka lura har zoben na taba lokacin da ka daura hannunka saman jikina..!!! ... Har inda yake ta tako tare da dukawa kasan kujeran hannunta saka ta dago hannunshi ta zare zoben dake jikinshi tare da sakawa cikin dusbin ....sannan ta dago fuskarshi ... "Uncle aka pictures kadae ? ...ka shiga gidan marayu? ...haba Uncle ...na sani kana son Abbanka amma Uncle bai kamata kaso naka ka tarwatsa wasu ba ...kowa Uncle idan shi aka ma haka na tabbata hakan zai aikata ..Uncle na goge pictures din duka....!! ..Nagode sossae Uncle har yanzu baka canza ba a raina !!! "Hudallah" ....ya fada ahankali ... Hannunta ta daura saman lips dinshi tare da mikewa taja Hannun Hanne da tayi mutuwar tsaye tana kallonsu .... ••°°•• Soyayya kuma da mutanen bata fasa ba ...sae dae bata kara yarda wani yazo gurinta ba cikinsu .... Kusan kwana uku bata ganshi ba .. .. tana so taje taga ko lafiya amma tana kunyarshi. . yarda ta dinga mashi tsawa ranar da abun ya faru sae take ganin kamar bata mashi halacci ba ... A hankali ta dan kalli Hanne dake cin abincinta hankali kwance..... "Aunty Hanne wae Uncle baya garin ne ko baya lafiya ? ...ta fada tare da dan goge hawayen da suka zubo mata da bayan hannu... Ta dade tana kallonta kafin ta girgiza kai tace .. "amma dae Hudah baki da zuciya mutumin da ya dakeki kamar jaka shine kike tambayarshi ...cab wallahi ni ko magana bana mashi ..." Aunty baki san waye Uncle ba ko?.. ...ta tambayeta tana kallonta ..."Dan Allah ki yafe mashi kinji!!! "Ke ai kin sanshi.. sakara mara zuciya anan falon ya gama cin ubanmu amma dan kina banza shine zakice na yafe mashi..." ...ta mike tare da shigewa daki abunta ... Ita kam bara ta iya fushi da Uncle dinta ba..kwana biyun nan ma da bata ganshi ba Allah kadae yasan yarda take ji ...Uncle dinta ya riga ya zama wani sirri azuciyarta wanda ba kowa ne zai fahimta ba .. ... mikewa tayi ta nufi dakinshi tare da turawa a hankali dauke da sallama..... Zaune yake ya hade kai da guiwa ...kneeldown tayi kusa dashi tare da dafa kafarshi da hannunta ... Ko bai dago ba kamshinta ya sanar dashi wacece ... "Uncle "...ta kira sunanshi a hankali .. Dagowa yayi yana kallonta ....da alama kuka yayi yarda idanuwanshi suka canza kala ...itama kukan ke niyar kwace mata ... "Uncle me ke damunka ? ..ta fada a hankali .. "Am sorry Hudah ...dan Allah ki yafe m"... saurin toshe mashi baki tayi da hannunta tana girgiza mashi kai .... "Dan Allah ka bar fadin haka uncle..wallahi baka da wani bashin yafiya da kake bani ..ni ce nake dauke da bashin alkhairinka a tare dani ...!!! "Tashi muje Uncle ..please kawae ka biyoni Uncle am

Table of Contents

Chapters

30 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30