Skip to content

Chapter 5

Chapter 5

A Dalilin Yayata Complete Hausa Novel 1,172 words 0 views Progress saved
Download Book

masu ...mutane sun dan tara masu taimako...sannan duk abunda ta samu sae ta sanarwa da Barister Shehun ...Daga baya sae komae ya tsaya masu abincin da zasuci ma sae ya fara gagarar su daga baya ma Sae mamarsu Huda ta koma tana zuwa ta dan taya mamarsu Barister Shehun aiki duk wata ta dan bata abunda zasuci abinci ...Da yake masu kudine ... 鈥⑩€⒙奥扳€⑩€� Wae lafiya barister two weeks baka zo office ba ..... Dariya ya sake da rafu kuka ciwo sannan yace ....Normal Shehu kawae har yanzu ban sake da lamarin munafikin mutun kamarka bane ....ya karashe maganar yana dafa kafadarshi ..... Munafukan mutane dae guda biyu ....ya bashi amsa tare da fashewa da dariya ..... Meye Ribarka ciki Shehu ka cutar da marayu wadanda kae ya dace ka taimaka masu .karamar yarinya tana rokonku amma ka kasa tausaya mata....Ya tambayeshi a sanyaye ... *_DALILIN YAYARTA_* nake komae shi yasa na tsani yarinyar don na lura duk abunda bata so to yayarta ma bata so ....saboda yarinyar yayarta take kina duk da bata fada man ba .....Barister Mahmoud ina tsananin son Saa ...amma Huda bata sona .saboda hakan Saar ma bata kaunata ...har gida naje na kaiwa saadatu kudi ta bar awarar amma taki karba tace suna da abunda zasu rufawa kansu asiri ....idan suka talauce ba ...ita da kanta zata zo ta rokeni ni kuma lokacin zanyi amfani da damata ....... Ba tare da ya bashi amsa ba ya bar office din don baya bukatar zama tare dashi ......... Gidansu Huda ya nufa cikin saa ya ganta ta fito tana cin goriba ......kwala mata kira yayi .... Daga bakin kofar gidansu ta tsaya tana watsa mashi harara tare da fadin....wallahi yaro ka mayyar garinnan ta yayeka bara ka ci goribar nan ba ..... Lumshe ido yayi ya matsa kusa da ita yana fadin ...baci zanyi ba Huda ....ki shiga kicewa Mamanki ina son magana da ita kinji ko ... Lah bata nan ....tana gidansu lauya tana aiki sae da marece zata dawo ....ta bashi amsa tana kallonshi ... five thousand ya ciro ya mika mata yana fadin ...ki kaiwa Yayarki ...kice tayi maku cefane kinji ko ... Tsaye tayi tana kallonshi kafin ta juya ta shige gida ba tare da ta karbi kudin ba ....ya dade tsaye yana tunanin ko zata sake fitowa amma sam babu dalilinta ...... Ko da ta shiga cikin gida ta iske yaya saa tana wanki ...da yake yanzu ita kewa yan gidansu barister shehu wanki suna biyansu .... Yaya Saa kawo na dauraye maki ....ta janyo bucket din da kayan wankin ke ciki ta fara daurayewadaurayewa Da sauri ta rike hannunta tana dariya ...barshi Huda karki jika jikinki .... Baran jika ba Yaya Saa ki bari na tayaki ....ke kullun mutun zaya maki abun kirki sae kice bakya so ....ta karashe maganar kamar zatayi kuka ..... Bana so ki wahala ne Huda kinji ko ....zan maki komae a rayuwarki in Allah ya yarda ba zaki wahala kamar ni ba ....karba ....ta fito da naira goma dake daure a zaninta ta mika mata .... Jiya kince kina so ki sayi dankalin gidan Lado ko ....ga kudin na samu kije ki sayo sae kici kinji ko ....karki toni kuwa saman hanya ba ruwanki da kowa ....kinji ko ... Kallonta tayi tare da kura mata ido ba tare da ta amshi kudin ba ...ita tama manta ta tayi maganar jiya ...amma yaya saa tana rike da abun bata manta ba ..... Karba kanwata ...ta katse mata tunani tare da janyo hannunta ta aza mata kudin ta turata waje tana murmushi ..... Har lokacin Motar mahmoud na kofar gidan .....ta kalleshi da idanuwanta da suka ciko da kwallah sannan ta kauda kai taci gaba da tafiyarta ..... Feedohm馃挒 鈥⑩€⒙奥� 馃挧馃挧 *_A DALILIN YAYATA馃崄馃崄_* 馃崄 *_HASKE WRITERS ASSOCIATION馃挕_* Na Feedohm馃挒 *_DEDICATED TO_* _EXCLUSIVE WRITERS..._ *_Gaisuwa mai yawa ga haske writers Allah ya kara basira da daukaka.._* 15 to 16 Saadatu bakya wankewa su hajiya kaya suna fitane sossae ....Mama ta fada lokacin da ta kai lomar tuwo a bakinta ... Da Sauri Yaya saa tace ...wallahi mama ina wankewa sossae ...cewa sukeyi basa fitane Aa cewa sukayi wae sae dae kije can ki dinga wankewa zasu fi fita acan .....amma gaskia ni bana son wannan yawon Saadatu ...ni ina fita aikatau kema ace kina wankau ...Sae dae suyi hakuri Aa mama zanje ....don Allah ki bari naje ....idan har na bar wankinnan ban san inda zaa sami kudin da zaa kai huda secondary ba ...dan Allah karki hanani ...bana so Huda ta wahala kamarni ..ina son ta samu ilmin mai yawa ...dan Allah ki bari na nemawa Huda kudin makaranta da karfina ...dan Allah mama .....hawayen dake cike da idonta suka samu damar gangarowa saman kumatunta ..... Huda ta matso kusa da ita saka hannu tana goge mata ....Dan Allah yaya saa kar kiyi kuka kinji ...ta tabe baki hawaye na sauka saman fuskarta ... Nan da nan yaya Saa ta maida hawayenta tana lallashin Huda ...Mama na zaune ta zuba masu ido ..... 鈥⑩€⒙奥扳€⑩€� Table din dake gaban Barister Mahmoud ya buga da karfi yana fadin ....Meye dalinlinka na bincikar shaguna na Idan table din ya amsa to barister mahmoud ya amsa masa .... Wallahi Mahmoud ka kuskura maganar nan ta fasu na rantse maka da girman Allah sae na watsa ka a duniya ...sai na saka ubanka da kake takama dashi ya tsaneka da ka shi zai koreka ka fitar mashi da gida ...Don wallahi bani kadae zan dauki laifinka har da kai ...sannan ka sani inda kyakykyawar hujjar da kai akayi fashin ....... Then So what idan ka fadawa duniya har dani akayi fashin ....kai duniya ta dama amma ina tabbatar maka wallahi asirinka yana gab da tonuwa.. 掳掳鈥⑩€⒙奥� Dady wani abokin aikinmu ne ke cikin matsala wallahi .. Dady ya kalleshi tare da fadin .. Subhannallah meke faruwa dashi .... Lumshe ido yayi sannan yace ...Wae wasu sukayi forcing dinshi yayi fashi a wani gida .... Ya so ne Mahmoud ....sam bai kyautawa aikinshi ba da iyayenshi ... Dady dole ba aka mashi .... Mahmoud na san idan kaine ko zaa daura maka bindiga bara kayi ba ....kabar wannan maganar ....Allah ya kyauta .. Ameen amma dady ... hannu ya daga mashi ....akul Mahmoud ....gobe ka shirya zamu je kauye akwae diyar Kawu Nalado da yace ya baka ka aura .... Aure dady ....ya fada a firgice .... Nima umarni aka bada Mahmoud Allah yasa Alkhairi ce ..... Ba tare da yace komae ba ya sadda kai ...kirjinsa ke dakan uku uku ....addua yake karantuwa har ya samu natsuwa sannan ya mike ya fice falon.... 鈥⑩€⒙奥扳€⑩€� Kamar yarda Yaya saa ta fadawa mama haka take zuwa kullun gidansu barister shehu tana wanki sannan ta dawo ta baro mama gidan .....A lokacinne Huda tayi jarabawar fita daga primary school .....bayan jarabawar ta fito ta samu Government day dake kusa dasu ..... Yaya saa tace bara tayi government ta tara kudin da zata kaita makarantar kudi ....ita da kanta ta kaita makarantar ta mata registration da kudin da take tarawa...... Ranar da ta kaita makarantar ta juya zata tafi taga discipline dinsu ya daga bulala zaya daki Huda ....tayi saurin dawowa ta rungumeta tana rokanshi kar

Table of Contents

Chapters

30 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30