Chapter 14
Chapter 14
dinta na 2.6m ...bayan ta tafine muka gane gold din jabu ne ...kuma mun rasa inda ta shiga a kasuwar...!! What ? ....Uban wa cikinku ya auna zinarin lokacin da zaku saya ? ...ya fada a firgice ... "Wallahi oga mu duka muna tsaye Bala ya auna ....Amma... "Shuttt up ...banzaye taya mace zata sayar maku da jabun zinari ku kirani kuna fada man bayan baku kamota ba ....wallahi bazanyi asara ba ...kune zaku dauketa wawaye.!!! Kashe wayar yayi yana kallon hajiya sae gumi ke keto mashi .... "Zancen banza ne shehu ...ba yarda za'ae mu dauki asara su zasu dauketa wallahi .. barsu karka kara kiransu ...!! Amma Hajiya... "Karka ce komae ...gobe zan tura Auwalu gurin ...zasu fito da su ne " Tashi yayi zai shiga daki ...tayi saurin tsaidashi tana fadin ... "Wae Shehu ya maganar yarinyar nan ta gidan Alhaji Tukur ...Kun dai daita ? Sosa kanshi yayi yana fadin .."Adama wae Hajiya" .. "Ita mana "... "Nifa dama ba aurenta zanyi ba hajiya ..kawae mum hutane ...Yarinyar duk da tana diyar mai kudi sae shegen roko ..!!..So nake Allah ya bani ta kirki sae na aura ..!..Yauwa Hajiya naga wata yarinya gidan liman ko ita za'a neman man ...tana da bala'in kamun kai ga addini ...kuma suma ba talakawa bane !! Hajiya ta saki dariya tana fadin ...Wae Maryam ...nima kaina yarinyar ta kwanya man ..akwae natsuwa gata yar mutunci..bara idan dad dinka ya dawo sae in masa magana !!!... *_MARYAM..._* Diyar liman ce wanda yace bara ya dauki Huda ba amma asali bashine ya haifeta ba agolace a gidan ....saboda Mugun Halin Matarshi ya hanashi daukar Huda !!....Hajiya zubaida itace uwar maryam ...su biyune ya'yanta ...daga Maryam sae Abdallah kaninta ....Shi liman Allah bai taba bashi haihuwa ba har yanzu ...kuma bai taba damuwa ba !!,..Kullun tana sanye cikin zunbuleliyar hijab ...a fuskarta kamar sahila amma azuciya sam babu tsoron Allah ...idan ta saka hijab a unguwarsu tana fita daga unguwar zata kira saurayinta yaxo ya dauketa ....duk wani club dake garin babu wanda Maryam bata zuwa ....yar' bariki ce ta k'in k'ari .... Feedohm💞 💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_* 🍁 *_HASKE WRITER'S ASSO💡_* ( _Home of expert & perfect writers_ ) Na Feedohm💞 *_DEDICATED TO_* _EXCLUSIVE WRITERS..._ *_41 to 42_* Duk unguwar kowa zai shedeta mutuniyar kirki ce ....mamanta kadae ta san irin rayuwar da take ...shima don tana kawo mata tsabar kudine ....ko da rana Daya liman bai taba fahimtar abunda ke faruwa ba a gidan ...!! Bayan da ubanshi ya dawo hajiya ta mashi magana aka fara nemawa Barister shehu auren Maryam ... Wata Biyar aka saka bikin ...ko da yaje gidansu Maryama bai samu matsala da Ita ba ...ta amsheshi hannu bibiyu ... Lokaci na zuwa aka daura auren ...an kashe kudi sossae ...don ko lefenta set biyar ne ..Gidansu Huda Barister Shehu ya saka a rushe suka hade da nasu ...aka dibarwa Amarya nata part din !!! ... •• •°°•• • "Huda kira man Auntynki "...ya fada tare fa sauketa daga jikinshi ... Uncle ... Hannunshi ya saka saman lebenta tare da nuna mata kofa ... Ta lumshe ido kamar yarda yayi sannan ta tafi da gudu ...Hanne na kwance tana waya tana fadin ... "Wallahi kawata na gaji da wannan shegiyar yarinya ...Ni kawae zance ya sawake man na tafi gidan iyayenshi idan ta tafi ya maidoni" tayi shiru tana saurarenta .. kafin tayi dariya tana fadin ..."Haba kawata ya za'ai yanzu na iya zama kauye ...ai sae dae gidan iyayenshi " ...don ni da kauye hai hata hai hata ....Ke nifa tunda nazo ba abunda ya shiga tsakanin mu .....abun har ya fara damuna kawata " "Aunty idan kin gama wayar Uncle na kiranki ...amma dan Allah kicewa shegiyar kawarki ina da baba ...itane shegiya bani ba ..!! ..idan kuma ke kika ce man shegiya to ...Allah ya isana !!! Bata jira amsarta ba ta kwasa da gudu .... Tarota yayi yana fadin "Bara ki bar gudu ba ko Huda ? ...baran sake goyaki ba !!... "Sorry Uncle na rantse maka da Allah na daina ..kaji ...!!!tayi rau rau da ido .. Hannunsa ta kamo ...Uncle wae idan Aunty Hanne ta tafi kauye tana da tsayayyene? ... Dariya yayi kasa kasa ..." Ban gane ba Huda !!! "Yauwa ...Ina nufin tana da wanda zai aureta ...?.. zaunar da ita yayi saman hannun kujeran .."Me ya faru Hudah ?.. "Kawae Uncle ka saketa mu zauna mu kadae ,,!! ..Kaji ? ...ta fada tare da langwabe kai .. Murmushi yayi kasa kasa ...kafin ya dago fuskarta yace .."Idan na saketa ke zaki aureni "..? "Eh mana ...ko yanzu ma ai ina aurenka Uncle ...tunda ni da aunty muke tsare maka gida ...kai kuma idan ka dawo ka dafa man abinci ko ..? Hanne ta shigo tana fadin "Wallahi munafuncin wannan Huda kullun k'ara yawa yake ...banda muguwar fata ni kike fadar a saka ?...Idan an sakeni Uwarki zaa aura?,.. Look Hanne !! ...ya daka mata tsawa ...wallahi kar na kuma jin kin zagi wannan yarinyar ..." Bata ce komae ba ta zauna tana hararan Huda .... "Ki shirya gobe ..ko kinki ko kinso ..da safe zamuje kauye a gano kawu ..!! " To dan Allah yaya ka sawo man wanan safar ta leda mai kama da takalmi ... " Cikin Mamaki yace "me zakiyi da ita ? Dan dukar da kai tayi tana fadin.."Wallahi yaya baran iya taka dattin gidan mu ba yanzu ...bana son kazanta ...!!! Dariya sossae yayi ...ba tare da yace mata komae ba yaja hannun Huda ...Kin tafiya tayi ta tsaya gurin .. Muje mana !! " Uncle ba kace zaka goyani ba ?...ta fada a hankali ... Murmushi yayi ...ai ba yanzu nace ba ko? ...ya dage gira .... Kafada ta make .."Yanzu mana " .. "To naji ...zoki hau muje ..." ..duk abunki iyakarki toilet zan direki !!! Shegiya ...hanne ta fada a hankali ... Gwalo ta mata tana hura hanci ..tare da zaro ido ... a harzuke Hanne tace .."Zanci Ubanki Hudah "... Mahmoud ya juyo tare zabga mata harara ... Feedohm💞 💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_* 🍁 *_HASKE WRITER'S ASSO💡_* ( _Home of expert & perfect writers_ ) Na Feedohm💞 *_DEDICATED TO_* _EXCLUSIVE WRITERS..._ *_Yaseen mutane ma sun maidani yarinya ...to wallahi am not a kid ..kyas nake kallonki ...wae na bata un edited copy taza duba man ..yo Fathern ki ya man typing😂😂😂😂😂_* *_43 to 44_* Karfe biyun rana suka isa kauyen ..lokacin anata haramar shiga masallaci ....Mahmoud alwala yayi ya shige masallaci ya barsu Hanne zasu shiga cikin gidan .. Hanne ta tattare Zaninta sama tana yatsina fuska ...ta shiga gidan ...da gudu kaninta ya taho yana fadin ... "Ga Hanne Ga Hanne ....." Da sauri taja baya tana fadin ..."tsaya tsaya boy ...dontu touchi mai wallahi _dont touch me_ " Sakin baki yayi yana kallonta tare da tsayawa jiki a sanye ....Hudah ta kura mata ido tana dariya kasa kasa ....Hanne na lura da Hudah ta zabga mata harara tare da jan karamin tsoki .... Inno ta fito tana washe baki tare da lale marhabun ...a dakile hanne ta amsa sannan ta isa tabarmar da inno ta shinfida ...dank'walin kanta ta cire ta shinfida saman tabarmar sannan ta zauna....ko da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30