Skip to content

Chapter 8

Chapter 8

A Dalilin Yayata Complete Hausa Novel 1,156 words 0 views Progress saved
Download Book

tsaya ko'ina ba sae kofar gidansu Barister Shehu ...Wai dadi taji ganin ba maigadi a kofar gate din.. ...ta kutsa kai ta shige cikin har tsakiyar falon ...babu kowa a cikin ...katuwar Plasma dake falonsu ita ta nufa ta fito da duwatsun dake cikin jikkarta ta makaranta ...ta dinga bugawa da karfi ...kafin me plasmar duk ta farfashe ...sannan duk wani abunda tasan na glass ne sae da ta fasa shi..harta windows din dake cikin falon sae da ta fasa...! Jin karar Glass yasa Hajiyar fitowa da sauri daga sink din wanka. ..ta daura towel ...don duk tunaninta daga waje karar ke fitowa sae da taji tabbas daga falon take fitowa Sannan ta fito daga toilet ....tana fadin .. "Waye anan ? ..."nace wane shegene ya shigo yake mana barna...? ...cak ta tsaya ganin karamar yarinya rike da duwatsu duk ta farfasha masu kayan dake falon ...!! Nice nan Hudalliya ....ta fada tare da runtumawa da gudu ta fita daga falon ...hajiya ta bita da gudu tana fadin .. Bala rike man wannan shegiyar yarinyar karka bari ta fita ...!!!...ganin babu maigadi ya saka Huda sake juyowa tare da jifar Hajiya da wani dutsin sannan ta fice da gudu ...!! Da sauri hajiyar ta dafe gefen idonta da dutsin ya sameta ..kafin zafin ya saketa Huda ta bace mata da tunani ...!! "Wace Shegiyar yarinya ce wannan ? ..take tambayar Kanta ..yar gidan wane shege ce ? ...me muka mata dan ubanta ?..."Hurul ..aa Hudiya...mts ...aa ba haka tace sunan ba" ...ta fada tare da dafe kanta tana son tuno sunan ...Da yake bata san Huda ba ...don duk da suke zuwa Huda bata taba biyo Yaya Saa ko Mama ba ... Barister Shehu ya shigo rike da friut din da Hajiyar ta aikeshi sawowa tun bayan fitar Maman Huda ....turus yayi yana kallon hajiyar da ta zabga uban tagumi zaune tsakiyar falon ... "Yan Fashine suka zo Hajiya? ...ya tambaya a rude ... "Yan fashi ko shegiyar yarinya Shehu ?...ta bashi amsa tare da mikewa tsaye..." wallahi wata shedaniyar yarinya ce ta shigo duk ta mana wannan barna ...ban san ko yar gidan uban wa cece ba ...amma tace ko Hurus ...wallahi sunan ya shige man ...amma zan saka a nemo man ita cikin unguwar nan ..." da Sauri yace ..."ko Hudallah? ... "Ba Hudallah ba Shehu ...na manta sunan ...amma wallahi duk randa na kamo ta taja wa ubanta bala'i dan baran kyaleta ba ...har da ni fa tayiwa ruwan duwatsu Shehu ji binan Yar da idona ya kumbura"..to meye hadinmu da ita ..?.. "Hajiya kinga yi man kwatancen yarda yarinyar take ...na tabbata Huda ce wallahi "... "To wacece ita Huda? ..."na fada maka ba haka sunan yake ba" ..."itama da Hu din sunanta ya fara amma nata sunan ban taba jinshi ba .".. "Huda diyar mamansu Saadatu ce wadda aka kora yau ...kuma nasan yarinyar sarai bata da mutunci ...bara yanzu zanje idan ma itace ta sake jawa uwarta bala'i ....!!! Ya fita da sauri ...ko mota bai dauka ba ya taka kasa ....baiyi Sallama ba ya fada gidan a fusace ...Mama na tsugunne ta rafka uban tagumi ...Yaya Saa tana wanke kwanukan da suka ci abincin safe dasu ... Su duka suka mike tsaye ganinshi ... ya Nuna Mama da hannu yana fadin ..."Ina shedaniyar diyarki ? .... Ran mama idan yayi dubu ya baci ta kalleshi a fusace zata yi magana yaya saa ta rigata ... "Bamu da Shedaniya a gidannan ....amma akwaita a gidanku mai dattin da kwali sabon shigan arziki ...banza maciya amana jahilai ...!!! ...ta fada tare da rushewa da kuka ... "Rufe man baki Shedaniya ...akwae shedan irinki mai bin maza ....shegiya karuwa..!!! Mama ta daukeshi da mari ..."Karya kake Shehu har yanzu ban haifi Karuwa ba Wallahi kuma baran taba haihuwarta ba " ..!! Ni kika mara ? ...ko da yake ba komae bane tunda har na kwanta da diyarki !!..zafin ba wani bane da zai dameni ....don ko kadan bai kai zafin da zakiji ba alokacin da kika fahimci diyarki karuwar Shehu ce ..!! ..don bana tunanin ban bar maku yaron da zaku raina ba na Shehu ..ko a tunaninku mutuncin da nake maku sonku nake ..? mtsee Jahilai ...to Sha'awar diyarki nake kuma fine ta kawon budurcinta har gadona ....!! ...ba wani shegen da iyasa ya tsaya maku ..matsiyatan banza!! Wani wawan mari yaya saa ta dauke shi dashi ..tare da sakin kuka ...bata sauke hannunta ba ..Mama ta dauketa da mari itama tana kallonta cike da tuhuma ....!! Sulalewa Yaya Saar tayi bisa guiwarta tana fitar da wani irin gujin kuka ....!! Dariya Barister shehu yayi tare da fita daga gidan ya barsu cirko cirko ...yaya Saa na tsugunne Mama na tsaye tana hawaye ... A zaure yazo fita sukayi karo da Huda ...wani mugun kallo ya aika mata ....itama ta sake mashi nata ...sannan tayi cikin gidan da gudu jin kukan yaya Saa .... Yaya Sa 'a ....dukanki ki ya kuma ?....ta fada tare da dukawa kusa da ita ... Mama ta saka hannu a fusace ta janye Hudar Gefe guda tare da dauke yaya Saa da mari ta janyo kwalar rigarta ta dago kanta ....! "Fada man Sa'adatu' ...fadan man gaskia abunda Lauya ya fada hakane ?..ko karya ya maki Sa'adatu?..ta fada tana kuka ... "Wallahi karya ya mata Mama!! ...Huda ta fada ba tare da tasan abunda ake magana akai ba kawae ta tsinci maganar ne... "Yi man shiru Huda dan Ubanki ...!!!..mama ta kwasa mata tsawa ....firgitar da tayi ya sakata fadawa jikin yaya Saa tare da sakin kuka ..."Fada man Saadatu "...shin na haifi karuwar Shehu kamar yarda ya fada?.. koko sharri ne .!!... Cikin Kuka Yaya Saa tace .."wallahi Mama baki Haifi karuwa ..ba laifina bane Fyad'e yayi man mama ...!! Wani uban duka ta kai mata tana kuka da karfi ....Huda ta rike mata hannu tana kuka ... "Wallahi Mama Hard'e yayi mata ".....ta leka fuskar yaya Saa tana tambayarta ...Yaya Saa Hard'e kika ce ko? ... Fizge Huda tayi daga jikinta tana dukanta ba tare da tasan inda take duka ba ...su duka ukun kuka suke kamar ransu zai fita... "Dan Allah Mama ki kyaleta na rantse maki da Allah Hard'e yayi mata ..!! .mama wallahi agabana yayi mata ...har cewa nayi karka yi mata Hard'e amma yaki saurarena !!! ...kuma wallahi Yayata bata Amai kullun!!!. ....Mamarmu dan Allah ki bar dukanta ..bana so ..!!.....ta karashe maganar tare da rike hannun mamar tana kuka... Wani Uban Mari Mamar ta bata ' ..kafin ta hankadata gefe guda ta cigaba da dukan yaya sa'a ...amma Huda dawowa tayi jikin yaya Sa'ar mama ta ci gaba da dukansu a tare ... Jikin Mama har ky'arma yake ...jin zata fadi kasa ya sakata jingina da bango tana kuka ....sannan taja jikinta ta shige daki ta barsu tsakar gida !! Feedohm💞 💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_* 🍁 *_HASKE WRITER'S ASSOCIATION💡_* Na Feedohm💞 *_DEDICATED TO_* _EXCLUSIVE WRITER'S..._ *_25 to 26_* Da marece Mahmoud yazo kofar gidansu Huda ya aje motarshi ...jingina yayi yana jiran ko Huda zata fito ...don so yake yau yayi magana da mamanta .... Cikin saa ta fito idanunta jawur tayi kuka har ta gaji ....bisa dakalin gidan ta zauna tare da

Table of Contents

Chapters

30 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30