Chapter 23
Chapter 23
hannuta guda .. tsaye tayi ba tare da ta juyo ba ...mikewa yayi shima ya rike kafadunta ya juyo da ita .... A kunnenta ya rada mata ..."Answer me please "....tsigar jikinta ta tashi tayi saurin matse jikinta gam tana kallon kafafuwanshi... "Please uncle ka sakeni ..." ...ta fada a hankali ... "Sae kin amsa man.. .this time biscuit din da kaina zan sawo maki yarda zaki ji dadin zama cikakkiyar matar Uncle dinki ..."...ya karashe maganar cikin zolaya ... Fizge hannunta tayi ta ruga da gudu tana rufe bakinta ..... Daki ta shiga tare da fadawa saman gado tana mirgina ......pillow ta janyo tare da kankamewa ...murmushi ya sake yana kallonta ...farincikin da ya gani a idon Hudah shiya tabbatar mashi da tsantsar soyayyar da take mashi ... "Ki daina Hugging pillow haka mana ' dani kika yi hugging may be da kinfi jin dadin sossae" ....ya fada cike da zolaya .... Pillown ta wurgo mashi tare da lullube fuskarta da zanin gadon tana dariya ....yafi minti 10 yana kallonta sannan ya shiga gurin hanne ya mata bankwana tare da kissing dinta a baki ...for the first time kenan a rayuwarta ....sae yanzu ta gane Hudah haskene ga dukkanin gidan... dakin Hudah ta fada tana zolayarta wae "amaryar Uncle" ...kallon mamaki Ta bita hannen da shi a tunaninta zatayi kishi sae ma taga kamar tana cikin farin ciki da abun . Mahmoud kuwa gidan liman ya wuce...da yake duk wani abun Huda sae ya gaya mashi ....magana suka je Sukayi .. liman yayi farinciki sossae da jin Mahmoud din zai auri Hudah ...ce mashi yayi duk lokacin da ya shirya yazo a saka rana .... Duk da bata da kowa ..amma duk wani abun alada sae da Mahmoud ya kawo aka saka rana wata 8 ...ba yarda Mahmoud din baiyi ba akan a barshi wata biyu ...amma liman yace " So yake yama Hudah duk wani abunda Uba kewa diyarshi ...nan da wata takwas yake tunanin kudinshi zata su fito don Haka yayi hakuri ya jira.". .... Ba yarda Uncle Mahmoud din ya iya haka aka barshi ...Hanne ya gaya mawa..Sae a gurinta ma Hudah ke ji ... ••°°•• Barister Shehu na gida aka bugo mashi waya wae shagonshi na zinarai wuta ta kama ...ba'a samu aka fitar da komae ba duk sun narke .... Sae da ya kwanta asibiti kwana 8 sannan aka sallamoshi ....Hajiya tayi ta wahala dashi don dad yanzu hankalinshi yana ga Hudah ....ko ya kirata waya bata dauka sae ta ga dama ...sannan yayi nacin yazo gidansu ta hanashi ..... Bayan an sallamo shi da gardadin a guji abunda zai bata mashi rai saboda yana da ciwon zuciya ga kuma hawan jini ...Part din hajiya ya koma ...dama safina na can tunda ya saki maryam .... Da marece ya shirya yaje gurin Hudah ...satar hanya tayi ta iskeshi gidan su lubna ... Yana zaune saman kujera duk ya rame ....ta dan kalleshi tare da kau da kai ... Yana ganinta ya mike har kyarma yake ..don kwana biyun nan da baya ganinta sae yaga ta kara wani bala'in kyau .... B'ata fuska tayi kamar zatayi kuka ....Tana gaidashi .... *FEEDOHM💞* 💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_* 🍁 *_HASKE WRITER'S ASSO💡_* ( _Home of expert & perfect writers_ ) *Na Feedohm💞* *_DEDICATED TO_* _EXCLUSIVE WRITERS.._ _Na rigaya na sadaukar da wannan book din ga exclusive da babu abunda zai hanani sadaukar maki da wannan page din Sweet Farida ... Amma duk da haka ina maki fatan alkhairi tare da addu'ar samun zuri'a ta gari ...._😘 *_70 to 71_* "Bakomae ."...ta fada tare da kawar da kai gefe guda tana matse hawaye .... "Ya zaki ce ba komae damsel ....Allah ki fada man meke faruwa ne ...indae ba so kike nima nayi kukan ba ..!!.. A hankali tace ..."ina yaron da na aiko farkon zuwanka nan gidan ya shigo da kai....? "Eh na tunashi ..wani abu ya sameshi .?... "Eh ..ya samu neotrophy ne _ita kanta bata san abunda kalmar take nufi ba ..jikin kwalin sabulu taga neotrophy din_ ...shine muke so mu fitar dashi india a masa aiki ...ga dad baya nan ...bama so mu fada mashi saboda yana da hawan jini ...to kudin ne sun tsaya cak ...ban san yarda zaayi ba!! ....ta fada tare da goge kwallah da suka zubo mata ... "Haba damsel akan kudu kike kuka ...duk da shagona ya kone bayan na gama zuba dukiyata hakan bara ya hana na samo maki kudi ba duk inda suke ....nawa ne kike bukata ? .. "ka barsa sweetheart" ...ta fada a hankali ... "No dan darajar Allah ki fada man nawa kike bukata ...." "Kudin na da yawa fa ...ka barshi kawae nagode!!! .... "Aa dan Allah wallahi ko nawa ne zan baki !!.... "ok 20m "....ta fada tare da kura mashi ido tana karantarshi ... Cikin sauri yace ..."ba matsala damsel insha Allah zan kawo maki zuwa jibi ..... "Ina zaka samesu bayan kace shagonka ya kone " .... "Takardun gidan da muke ciki yana hannuna ...zan sayar dashi ba da sanin dad ba ...na tabbata nan da one year na tara kudin sae na mayar masu da kudinsu na karbi gidan ....ba tare da kowa ya sani ba !!!! tasowa tayi tare da kissing nashi a goshi sannan ta koma suka cigaba da fira .... Bayan ya tafine ta kira dad dinshi tace tana bukatar 20M ...tana so ta sayi mota da dan karamin gida ..saboda friends dinta sun fara mata gori cikinsu itace batta da mota da gida ....suna gama wayar ya mata transfer kudin da yake akwae su ... ••°°°•• So take ta tashi tayi inserting farin pure miskin da lubna ta bata tun da aka samata rana tace duk one month da ta dinga inserting...satar kallon Uncle din tayi taga ya maida hankalinshi ga news yana kallo ....Hanne dama ba gwanar fira bace ...ya shige daki abunta.. Mikewa tayi da sauri tare da fadawa daki ta shige toilet ta dauki cotton kadan ta dangwalo .....wani uban ihu ta sake tana dire dire ... Da sauri ya shigo dakin yana kiranta ...ganin tana toilet ne ya sashi tsayawa bakin toilet din .. "Hudah .....menene ? Kokarin kunna heater take ta kasa sae uban ihu take tana tsalle ... "Na shigo Hudah? ....ya fada a hankali ...jin ihun nata yayi yawa ... bata bashi amsa ba ta cigaba da ihunta ....tura toilet din yayi ya shiga da sauri ....kwalbar miskin ya gani da cotton din da ta dangwalo ...ita kuma tana gefe sae uban ihu take ... Ko baa fada mashi ba ya san abunda takewa ihun ....duk da ta bashi tausayi amma dariya yake mata ....bai ga wanda ya sakata ba kilbibi ne irin nata ..... Cikin kuluwa da dariyar da yake mata ta juyo tana hararanshi tare da watsa mashi ruwan sanyin da ke cikin bucket .... "Ba komae kije da zafinki .....see ..naga wani abu irin wannan a gurin wata mata idan na fita zan sayo maki sae ki kara sakawa ..tunda naga kin girma da yawa ....!!! ...ya fada yana dariya ... Da sauri ta juya ta hade kanta da bango cike da kunya ...ga azabar take ji ...Allah ya isa kuwa ta jawa Lubna yafi cikin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30