Skip to content

Chapter 20

Chapter 20

A Dalilin Yayata Complete Hausa Novel 1,126 words 0 views Progress saved
Download Book

murmushi a fuskarta ...wanda ya dada fitowa da ainahin kyawunta ... " double sorry pretty".. Ya fada cikin sanyin murya ..duk da yana tunanin mistaken number tayi ba shi bane ...amma da yake ido ga mata sae yaga bara ya iya barin wannan pretty din ba ta wuceshi ... Ta bude idon da sauri tare da waro ido _wanda ta tabbata ko uncle tayi wa irinshi sae yafi minti talatin kafin yabude idonshi ya kura mata ido ..barewa wannan karen ...wanda take tunanin ko jakka aka daurawa zani sae ya bita !!!!_ Haka kuwa ya faru ..don baisan lokacin da ya rungume wayar ba ..sae alamun zanen shaddah da ta gani ... Dariya tayi mara sauti sannan ta datse kiran tare da aje wayar gefe guda ... Kasa hakura yayi ya kirata ..Tana jin alamun ana kiranta amma ta share wayar ...sae da yayi mata missed call kusa 5 bata dauka ba ... Imo din ta koma ta tura mashi text _"am sorry mistake din number nayi..a digit din karshe instead nasa 6 sae nasa 9 "_ kafin ta fira har ya fara typing ... " _Nasan prety ...amma babu ta inda Allah baya hada mutane_ !!! "Ashe kunsa Allah ? ...ta fada a fili sannan ta maida mashi da " " _Ok"..._ Kiranta yayi a video call ...har sae da ta kusa tsinkewa sannan ta dauka ba kunya ya tasa karamar yarinyar cikinshi gaba yana mata sabbatu . .... Kallonshi kawae take tana murmushi kafin tace .. "kayi hakuri na fada mata mistaken number nayi please...!! At long last ma cewa yayi ta bashi adress din garin da take da gidansu ... " ba bukata "...ta fada a hankali .."domin gaskia kai saan ubana ne kaga bara ya yiyu nayi soyayya da kai ba !!! "So baya tsufa pretty" ....ya fada cikin sauri ... . Datse wayarta tayi gaba daya sannan ta kashe ..... Dad din shehu kuwa cigaba yayi da kiranta amma yaji ta rufe ...daran ranar kasa bacci yayi ...bai taba haduwa da yarinyar da ta tafi da imanin shi ba irin yau .... tana bude wayarta kamar rige kiran dad din Shehu na shigowa ..yana katsewa na shehun na shigowa ...bata dauki ko daya ba ta shige tayo wanka ...dama tun da daddare mama ta ce da safe Mahmoud ya kawota zata tayata zama saboda Abba zaiyi tafiya .... Bayan ta shirya suka shiga mota ita da Uncle Mahmoud .. Sun dauki hanya sossae ba wanda ya tankawa wani tsakani ...sae dae lokaci lokaci suna kallon juna ...shiru ya mata yawa gani take kamar baya lafiyane ...tana so ta tambayeshi meke damunshi amma ta kasa ...da ky'ar ta bude baki tace .. "Uncle baka lafiyane ? ...tana kallonshi ... juyowa yayi a wahale yana kallonta ..wani murmushi ta sake mashi da ya sashi ta taka birki da sauri ya kauce hanya ... tsoranta da tayi yasa ta fada jikinshi tare da zagaye hannunta jikinshi ...sauke ajiyar zuciya yayi sannan ya zagaya da hannunshi bayanshi ya riko hannuwanta tare da zameta jikinshi yana kallon idonta ... Bata fuska yayi .."Kin san me kikayi kuwa? .. *Feedohm💞* 💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_* 🍁 *_HASKE WRITER'S ASSO💡_* ( _Home of expert & perfect writers_ ) *Na Feedohm💞* *_DEDICATED TO_* _EXCLUSIVE WRITERS.._ *_61 to 62_* "Uncle me nayi "...ta fada hade da fito ido waje ....yarda tayi tunani haka ta faru ..domin lumshe ido yayi na tsawon mintina ... "Da kin kashemu da kin huta",....ya fada still idonshi a rufe ... Rufe bakinta tayi tana fadin ."Uncle daga murmushi ... Harara ya sake mata ...ta kwashe da dariya ...ita kanta yarda take dariyan so yake ya zame mashi matsala ... Tada motar yayi yana fadin "please Hudallah".. ...sauran maganar ya makale a makoshi .... Dariyan ta cigaba dayi cikin salo tana kallonshi tare da fadin ..."Uncle ...!!! Tare da Jan sunan Motar ya kashe ba tare da ya kalleta ba ya fita ...napep ya tsayar ya zagayo ya bude mata kofar ... 1k ya daura mata saman cinyarta yana fadin ..."zo ki wuce Hudah mun hadu acan please " ... "Uncle .."..ta fada a shagwabe ... "Please Hudah .!!..ya hade hannayenshi guri guda yana Nuna mata napep Ba haushi ya bata ba ...sae dariyar da ta masa ta hau napep din tana waigeshi ...sae da sukayi nisa sannan ya tada motar ya tafi gidan shima Sae da ya rigasu zuwa gidansu...yana zaune falo ta shigo tana kwalawa Maman kira ... Harara ta sake mashi sannan ta zauna still tana kwalawa mamanshi kira ... mama ta fito tana fadin. ""Wannan kira haka Huda sae ko fasawa mutun kunne " "Mama na gajine mai napep din da ya kawoni zagaye yayi Dani" ..ta fada tana kallon Uncle din Wanda shima tunda ta zauna ita yake kallo .. "Yo garin ya ? ...ba tare dakuka taho dashi ba ...!! "Mama tambayarshi dae... har fa mun taho daga na mashi dariya shine ya saukeni ya tare man napep yace na taho ...!! Mikewa yayi ya shige ciki ba tare da yace komae ba ...mama kuwa dariya ta masu ..sannan Hudah ta mike suka shige ciki ... ••°°•• Kwanaki na kara ja....soyayya sossae ake tsakanin Hudah da Shehu da kuma dad dinshi ... duk sun dauki son duniya sun daura mata ...Dad address din gidansu wata kawarta ta bashi ...duk lokacin da yace zaya to sae ta shirya ta tafi .... Lokaci guda ta gama rikitasu ....Barister Shehu yace mata yana so suyi aure a wannan shekaran ... Ce mashi tayi "bara ta iya auren mai mata ba Wallahi sae dae idan zai saki matanshi sannan zata yarda ta aureshi ..!!. Kamar ta mashi asiri yace ya yarda zai saki maryam din yau ....Ita dae bata ce mashi komae ba sae murmushin da ta mashi ... Ranar da ya saki maryam din ranar yazo gidansu lubna gurinta .... Da kyar dama uncle Mahmoud ya barta ....bayan sun gama firansu ne ta rakoshi ....ko a wajen janta yake da fira sam idan yana tare da Sa'adah baya so ya rabu da ita ....murmushi kawae take mai cike da ma'anoni daban daban ....Karar motar Uncle Mahmoud taji ta juya da sauri tana kallonshi ...Ji tayi numfashinta na Neman barin jikinta ..da kyar ta tsaida natsuwarta guri guda..... Kallon kallo suke su duka ukun ....wanda barister shehu yafi maida hankalinshi ga Barister Mahmoud ...Hudah kuwa dukar da kai tayi kasa *FEEDOHM💞* 💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_* 🍁 *_HASKE WRITER'S ASSO💡_* ( _Home of expert & perfect writers_ ) *Na Feedohm*💞 *_DEDICATED TO_* _EXCLUSIVE WRITERS..._ *_63 to 64_* Ba tare da yace komae ba ya figi motar ya koma cikin gida kamar zaya tashi sama Barister shehu ya saki ajiyar zuciya yana fadin ... "Kin san wancan ne Sa'adah ? ... Girgiza mashi kai tayi tana murmushin yake .. " "kai ka sanshi ne ? ...ta tambaya tare da kura mashi ido " Yeah ...da gurin aikin mu daya ..Don shine ma babban mu ..but yanzu ya bar gurin aikin for morethan 5years ban san inda ya koma ba ...amma naga yana maki wani kallo ...ko ya kyasa ne ...? Murmushi tayi ba tare da tace komae ba ... " Kwalelenshi ...Sa'adah sae Shehu,! ...Ya fada yana murmushi ... "Jiya munyi

Table of Contents

Chapters

30 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30