Chapter 9
Chapter 9
shikuwa Sadiq yana tsaye a gefena har wannan lokacin sai dai babu wanda zai iya tantance yanayin da yake ciki. Daddy ne yayi ƙarfin halin tambayata yace "Daughter me ya faru ne kin saka mu a cikin ruɗani." Cikin nauyinsu da nakeji na labarta musu abinda zan iya tunawa, ai kuwa tamkar waɗanda ke jiran ƙiris nan suka soma fashewa da kuka hatta Daddy sai da yayi hawaye illa Sadiq da kallo ɗaya zaka mishi ka firgice da yanayinsa na tsantsar ɓacin rai da yake ciki. Nan suka fara jajanta abin kowa da abinda yake faɗi akai musamman Momi da saida Baaba ta tsawatar mata saboda ɗiban albarka da take yiwa M.J ba ƙaƙƙautawa. Tare muka wuni a asibitin har Daddy kowa da kalar kulawan da yake bani, cikin wuni ɗaya kuwa tamkar wacce ta daɗe tana jinya naji na samu ƙarfin jiki sosai, duk waɗannan abubuwa dake faruwa zuciyata a ƙage take dare ya ratsa na samu na karanta littafin da Saleem ya kawomin wanda dashi nakeson amsa musu tambayoyin da suke ta yimin akan littafin musamman Jiddah. Sai wajen ƙarfe goma na dare su Momi da Saleem suka yi mana sallama aka barni da Baaba da Jiddah domin kwana da ni, duk yadda akaso Jiddah ta je gida ta turje hakan yasa aka barta mu kwana tare. Kaɗan-kaɗan muke hira har bacci ya rinjayi Baaba ta kwanta ta barmu ni da Jiddah muna hirar, ganin baccinta yayi nisa ne yasa na fito da littafin daga ƙarƙashin filon da nake kwance na yafito Jiddah tazo gefena ta zauna muka buɗe littafin a hankali mu ka fara karantashi cikin zumuɗi. *ASALIN LABARIN WANZOWAR ALPHA*...✍🏻 _🙏🙏🙏 Nima na shaida nasan kuna haƙuri da ni sosai musamman ƴan VIP da yanzu bana iya muku update kullum. Dan Allah kuyi haƙuri abubuwa suna yimin yawa ne amma zan dinga ƙoƙari in sha Allah.🥰🥰 Kamar yadda nasan kuna yi inaso ku cigaba da sani a addu'o'inku akan abinda na sa a gaba.🙏🙏🙏 Ina son ku irin totally💃💃💃 *BY* *JASMINE*🌸🌸 *ASP ZARAH*👩✈️ *BOOK 2* *Page 6* _Mafarin Lamarin_. Asalin sunansa Al'amin, ya kasance ɗa na biyar ga Malam Mudi da matarsa Inna Habi, sauran ƴan'uwansa uku mata da namiji ɗa inda ya kasance auta, bayan haihuwar Al'amin ne Malam Mudi ya ƙaro aure inda ya auri wata bazawara da ake kira da Phalmata, tun daga lokacin kuma rainon Al'amin ya dawo hannunta. Saboda kulawar da take bashi yasa Inna Habi ta bayan ta yayeshi ta tattara kayansa ta maidawa Phalmata riƙonshi gaba ɗaya. Shekararsa takwas kacal a duniya Allah yayiwa Inna Habi rasuwa, a wannan lokacin duk sauran yayyinsa sunyi aure illa ɗan'uwansa guda da shima yake shirin yi. Tun ƙuruciya Phalmata ke koyawa Al'amin dabarun sace kuɗin mutane da zarar sunyi sake sai dai duk da haka bata gaza wajen ganin cewa ya samo ingantaccen ilimi saboda wani buri da ke ranta, baya ga haka itama tayi karatu kuma ta ɗanɗani daɗinsa. Tun girmansa sai ya kasance ya kara haɗuwa da abokai masu irin tarbiyarsa, tun daga wannan lokacin lamarin satarsu da fashi ya shahara, sai dai suna yin komai ne cikin basira basa taɓa bari su bar shaidar da za'a gane su. Bayan kammala karatunsa na Jami'a ne Allah yayiwa mahaifinsa rasuwa, a wannan lokacin ne Phalmata ta baiyana masa shirinta na zamewarsu shahararrun ƴan ta'adda da zasu addabi ƙasa da duniya baki ɗaya. Suna kashe duk wanda suka nemi dukiyarsa ya hana, sannan muddin suka kwallafa rai akan abu sai sun samu. Haɗewar sunan Phalmata da Al'amin ne ya samar da sunan ALPHA wanda mutane da dama suke tunanin sunan na mutum ɗaya ne. Shararsu ne tasa gwamnati ta shiga neman hanyar da zata kamasu gadan-gadan, sai dai sun siye baki mutane da dama daga sama wannan dalilin ne yasa duk sanda zasu tura yaransu yin fashi suke hada baki da manyan jami'ai domin a dakatar da tsaro a inda zasuje ɗin. Sun yi nesa da inda mutane suke sannan sun alkinta kansu ta yadda babu wanda zaiyi tunanin saninsu ko yasan wani abu dangane da su. A yanzu haka suna rayuwa ne a garin Enugu a cikin wani ƙauye da ake kira Keruba, wani abun mamaki shine duk da a cikin mutane suke amma hakan baisa mutane sun shaida su, dalili kuwa shine, wani madaidaicin gida kamar ko wanne gida da kuka saba ganin mutane na rayuwa a ciki, amma a ƙasan wannan gida rantsatstsiyar fada ce tamkar ta sarakai wacce aka yiwa laƙabi da _ALPHA VILLA_. Babu wanda yasan a inda ƙofar dake sada mutane da Alpha Villa take a cikin wannan ƙaramin gida, a duk lokacin da mutum zai shiga ko fita sai an shaƙa masa hodar dake saka bacci na wasu mintuna. Ta hanya ɗaya ne kacal zaku iya nasarar kama Alpha a sauƙaƙe. A kowacce ranar Lahadi yana ɓadda kama ya fito daga wannan gidan don ya zaga gari, yakan kwashe awa guda da rabi yana zagawa kafin daga baya ya koma mazauninsa. Babban lagon Alpha guɗa ɗaya ne, wato mace mai ciki. Yana matuƙar tausayin mace mai ciki ko da wucewa tayi ta gabansa sai yaji hawaye na neman fitowa daga idonsa. Saboda haka idan kunason kama Alpha dole ku nemi wata mace da ke da ciki don samun lagonsa. Mun daɗe mu na karatun wannan littafin har dare ya ratsa sannan mu ka gama, ajiyar zuciya mu ka sauke a tare ni da Jidda bayan na rufe littafin na maida shi inda yake, kallon juna mu ka yi cike da rauni kafin Jiddah ta ce "Na samo mana mafita." "Mafita? Wace iri?" na tambaya. "Mai ciki ake nema kuma gani sai ki zame min ƴar jagora." "Ke baki da hankali ne Jidda kinsan me kike faɗa kuwa." "Wallahi idan kika kuma mu sa min akan abinda na faɗa ban yafe hakkin ƙaunar da nake miki." Jiddah ta fada tana mikewa ta koma kusa da inda Baaba ke kwance itama ta kwanta, ta barni sororo ina jimami. Na jima a zaune kafin daga baya na tura littafin ƙasan filo,sannan na sulale na kwanta zuciyata cike da tunanin mafita. Washe gari tunda farar safiya Sadiq ya iso asibitin, kallo ɗaya za'a masa mutun ya gane cewa bai runtsa ba, Baaba ya fara gaidawa sannan nida Jidda muka gaishe shi ya amsa yana tambaya ta ya jiki. Zama yayi a gefena yace lafiyarki" Cikin mamaki muke kallonsa ni da Jiddah kowa da abinda yake saƙawa a ranshi. "Amma Yaya me yasa ba zaka barni anan ba." "Ina so ki yi nesa da M.J banaso ya kuma ganinki bare wani abu ya shiga tsakaninku ko da kuwa kalmace ta fatar baki." Baaba da ke zaune can gefe ne ta ce "Haka ba shine mafita ba Sadiq a barta anan ɗin kawai, ai an riga da anyi kuskure ba za'a kuma bari kalan haka ta faru ba." Ganin Baaba na son jan maganar ne yasa ya ja bakinsa ya yi shiru bai kuma magana ba. Mu na zaune a haka su Daddy suka shigo shi da Momj da Saleem, hannun Sa-Jid ɗin ɗauke da kwandon abinci, gaishe-gaishe aka yi suna ƙara tambayata ƙarfin jikin. Momi ce ke faɗamin cewa Ammi ta kira waya tana gaishe ni, sannan ta ce zasu
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24