Chapter 24
Chapter 24
an guntule sai sanda take amfani dashi. Ko da ta ganesu nan ta durƙusa tana basu hakuri sosai tana basu labarin abubuwan da suka faru da ita dan har prison sai da aka kaita sanadin wannan Alhajin daya mata ciki, gashi iyayenta ma duk basu da lafiya suna kwance ƴar uwarta ce kawai ke taimaka musu itama mijinta ya ɗauke ta sun bar ƙasar. Sun tausaya mata sosai nan M.J ya mata kyautar maƙudan kuɗaɗe bayan sun yafe mata. Shekararsu Amran ɗaya da watanni mahaifinsu ya kwanta ciwo zazzabi me zafi ya rufe shi, ba shiri ya ɗauki Zarah suka tafi asibiti aikuwa kamar yadda yayi tsammani tana da shigar ciki na wata biyu murna ce ta kamashi ita kuma Zarah ta nuna sam bataji dadi ba saboda yaranta basuyi girman da za'a yayesu duk da dai babu inda basa zuwa da ƙafarsu sannan kuma suna cin abinci sosai. Shawarwari likita ya basu na yadda zata kula dasu kafin cikin nata ya girma. Da haka suka dawo gidaa. Sanda Ammi taji labarin cikin Zarah ta kanta ta shiryo ta taho Nigeria ta ɗauki su Amran ta wuce Egypt da su dama kuma yaran sun santa gashi basa da kiwa ko kadan dan haka ne bata sha wuya da su. Tabar M.J yana cigaba da rainon cikin matarshi da a yanzu ma yake fatan ta haifo mishi ƴan biyun. *KARSHE* *ALHAMDILILLAHI NAN NA KAWO KARSHEN WANNAN LITTAFI NA ASP ZARAH, ABINDA NA FADA DAIDAI ALLAH YA BANI LADARSA INDA NA KUSKURE KUMA INA ROƘON ALLAH YA YAFEMIN.* *MASOYA INA GODIYA SOSAI DA IRIN ƘAUNARKU A GARENI, ALLAH YA SAKA DA ALKHAIRANSA YABAR ZUMUNCIN DAKE TSAKANINMU. INA GODIYA SOSAI DA HAKURIN DA KUKAYI DANI TSAWON WANNAN LOKACIN. SON SO FISSABILILLAH* *KU TSUMAYE NI A LITTAFINA NA GABA DA ZAI FARA ZUWA MUKU NAN DA WANI ƘANƘANIN LOKACI ME SUNA AL-MUSTAPHA. FREE BOOK NE NAYI SHI DOMIN KU MASOYA, YAZO DA SALO NA MUSAMMAN KADA KU BARI A LABARTA MUKU*. *TAKU HAR KULLUM* *JASMINE🌸🌸*
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24