Chapter 23
Chapter 23
da suka zo dubata, ranar da Sadiq yazo gaisheta da jiki saida yayi mamakin abinda yaga M.J na yi mata, M.J ɗan kwalisa da shan ƙamshi amma shine ya ƙasƙantar da kanshi akan mace, dan a kitchen ma ya taddashi yana soya wainar fulawa wai Zarah take son ci, tun abin na bashi mamaki har ya koma tausayin M.J din ganin gabadaya bashi da wani lokaci da zai yi abin kansa sai wanda tace dashi, hakan yasa ya musu sallama ya tafi a yanzu hankalinshi ya kwanta da auren nasu. Shikuwa M.J duk wannan abin da yake yi sam baya damunshi musamman da a yanzu ya samu sake har kwana yake yi a ɗakin Zarah kuma bata hanashi wani lokacin ma har hira suke yi sosai musamman idan suna kallon labarai aka taɓo harkar tsaro nan zasu zauna suna tattaunawa akan halin da ƙasar mu ke ciki ta fannin tsaro. Da haka zaman nasu ya fara daɗi ko bayan da ta warke, kullum tare suke bacci watarana a ɗakin M.J din ko a ɗakinta, tare suke tashi su kimtsa gidan kowacce safiya dan Zarah ta tubure batason me aiki duk da M.J yaso ya ɗauki me taimakamata dole ya hakura tunda ta nuna bataso. Tare suke fita ya sauke ta a wajen aiki kafin ya wuce nashi wajen aikin idan an tashi ma haka zai zo ya ɗauketa su wuce gida wani lokacin kuma gidan Momi suke wucewa. Da haka dai har M.J ya hillaceta haƙarsa ta cimma ruwa, aikuwa ranar ya sha kuka da nadamar abubuwan da ya aikata mata har sai da ciwon shi ya tashi, hakuri kuwa har sai da ta nuna zatayi fushi sannan ya daina bata. Zaman da ya biyu baya babu laifi zamane na aminci da kyautatawa juna duk da har a lokacin Zarah ba sonshi take yi ba kuma bata manta da Safwan cikin ranta ba dan kullum idan tayi sallah sai ta mai addu'a shi da iyayenta da sauran musulmai magabata. Babu irin gatan da M.J baya mata wani lokaci har tausayi yake bata idan taga irin kulawar da yake bata, komai nashi ita ne duk abinda ya samu ita. A cikin watannin da suka biyi baya ne watarana M.J ya tashi da wani irin zazzabi me zafin gaske, sosai hankalin Zarah ya tashi dan har sumewa yake yi da ya farfaɗo kuwa zai kuma ba shiri ta kira gida ta sanar sannan ta kira Abdallah suka ɗauke shi sai asibiti. Kwananshi biyu amma duk allurai da magungunan da ake bashi kamar ba'ayi har anfara tunanin ko ciwon bana asibiti bane. Ranar da Baaba tazo asibitin ne ta gane ainihin musabbabin ciwon, suna zaune harda su Momi da Jiddah dan lokacin dare ne anyi sallar isha'i ma, kallon Zarah tayi sannan ta kalli M.J ta tuntseri da dariya sosai har tana saukowa daga kan kujerar da take, kallonta suke yi cike da mamaki, Sadiq ne ya rike baki ya ce "Momi bari na kira likita inajin matar nan ba kalau take ba." Jin abinda ya faɗa ne yasata tsagaitawa ta kalleshi ta ce "Zan saba maka fa Habu ni kake dangantawa da taɓin hankali." "Alama kika nuna ai" ya fada yana kauda kai. Tsaki tayi sannan ta maida kallonta ga M.J dake kwance cikin ciwo tace "Wato dai kai Muhammadu da gaske kake so ka zama mijin tace koh? Ita ke da cikin amma kaine kake mata laulayin." "Laulayi kuma Baaba.?" Momi ta tambaya. "Yoo ai sai kuyi kuma sau nawa akayk muka gani Zara'u ce fa ke da ciki shi kuma yake mata laulayin cikin dama ana samun haka wasu lokutan idan mata ta samh shigar ciki ta hanyar mijinta kaɗai ake ganewa dan wasu ciwo suke kamar ba zasu rayu ba." Wani irin farin ciki ne ya sauka a zuƙatansu babu shiri Momi taja hannun Zarah suka fice kai tsaye sashin da ake bincikar masu ciki ta kaita dan ayi mata awo saboda itakam ta yarda da batun Baaba dan a zamanin baya ma kafin wani daga cikinsu ita da marigayiya yasan yana da shigar ciki Baaba ce take fara ganewa ta fada musu kuma idan anje asibiti a tabbatar. Kasancewar an sansu a asibitin ne yasa babu ɓata lokaci aka shigar da Zarah ɗakin scanning din aka kwantae da ita sannan aka jona mata na'urorin, mintun biyu tsakani kuwa sai ga hoton cikinta ya bayyanah da ɗa kwance, farin ciki ne ya rufe Momi ba shiri ta fadi acan gefe tayi sujjadar godiya ga Allah. Wani zuben zinari me matuƙar tsada dake hannunta ta cire ta baiwa matashiyar likitar tukwici. Basu dawo ɗakin ba sai da aka gama buɗewa Zarah file na masu ciki sannan ta riƙo hannunta suka dawo nan take shaida musu fa akwai cikin a jikin Zarah har na wata hudu ma, hamdala suka fara yi tare da gode ma Allah hatta M.J dake kwance sai da ya mike ya zauna sannan ya riko hannun Zarah dake gefenshi yana zuba mata godiya. A daren yace bazai kuma kwana a asibitin ba tunda angano silar ciwonshi dole haka likita ya sallameshi suka koma gida inda aka bar Baaba dan kulawa da Zarah. Sanda Rahama taji labari kuwa tayi murna sosai duk da itama a lokacin tana da ciki har ya shiga watan haihuwa. Tunda cikin Zarah ya bayyana kuma sai ciwon da M.J yake yi ya ragu nan ya cigaba da baiwa matarshi kulawa baya ko kunyar Baaba dake gidan hakan yasa ta tattara kayanta tabar gidan dan tace ba zata iya zama ayi abin kunya a gabanta ba. Sati biyu da faruwa haka Rahama ta haifi ƴarta mace. Gabadaya suka tattara suka nufi Yola da sha tara na arziki. Anyi shagalin suna sosai irin na gidan sarauta,yarinya taci sunan mahaifiyar su Mahmud Zulaihat ana kiranta da Afrah, satinsu guda suka juyo suka bar me jigo cikin kulawar dangin mijinta dan su gidan sarauta basu yarda da al'adar wankan gida ba. Watan Afrah huɗu da kwanaki Zarah ta sauka lafiya ta haihu ƴan biyunta macw da namiji kyawawa masu kama da ubansu. Farin ciki kuwa ba'a magana a gurin dangi. Nan aka fara cika gidan ƴan uwa da abokan arziki kowa na zuwa ganin ƴan biyu. Ranar suna kuwa ansha mamaki kwarai sunan da M.J ya sakawa yaran, macen Fadimatul Zarah namijin kuma Safwan inda za'a kirasu da Amrah da Amran. Mutane da dama sun jinjina wannan abu da ya yi, ita kuwa Zarah tayi farin ciki matuƙa har ta kasa ɓoye hakan. Mai Martaba da kanshi sai da yazo ya yi godiyar wannan kara, inda yawa yara kyautan manyan filaye guda biyu bayan kuma kaya da aka kawo musu. Yara sunzo da goshi dan sun samu kyaututtuka da dama na ban mamaki. Kulawa sosai suke samu daga wajan iyayensu da sauran dangi. Musamman mahaifinsu ma daya ɗaura son duniya akansu. Haihuwar Zarah ba da dadewa ba aka yi auren Sadiq wanda ya tara manyan mutane sosai sannan an kashe kuɗi sosai. A haka rayuwa ke tafiya awanni na shudewa su bada kwana daga nan satika har watanni. Watarana su Zarah sun fita shopping, a hanyar dawowarsu ne suka kusa kaɗe wata almajira, ko da suka fita suka duba ba kowa ba ce face Hajara, ƙafarta ɗaya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24