Chapter 17
Chapter 17
"Subhallahi me ya faru Muhammadu ai banji shigowarku ba ma." Abdallah ne ya riƙo shi suka ƙarasa cikin falon ya zaunar dashi acan kujerar gefe ta yadda bazai iya ganin komai a cikin laptop din ba sai bayanta da yake gani kawai, hannu yasa ya dafe saitin zuciyarsa da yake ji tana barazanar fitowa, sosai ya yi mamakin irin canjawar da Zarah tayi ta zama kamar wata balarabiya musamman yanzu da ta yaga tana sanye da arabian gown sannan ta rolling kanta da veil din rigar, fatarta sai sheƙi take yi kamar a taɓa jini ya fito, ganinta ya faranta mishi da farko sai dai batun da tayi wa Safwan ya matuƙar ɗaga mishi hankali musamman da yaga irin kallon da suke wa juna hankalinshi yayi masifar tashi kar dai ace su Daddy aurar mishi da Mata suka yi, abinda yayu sanadin tarin nashi kenan. "Sannu ɗan nan bari na kawo maka ruwa." cewar Baaba tana nufar hanyar kitchen, dawowa kuma tayi da hanzari ta isa gaban laptop din tace "Zara'u ku kashe na'urar nan zanyi wani abu yanzu Muhammadu ne ba lafiya." Baki Zarah ta taɓe dan ita har ga Allah ta manta da M.J kwata kwata a rayuwarta sai yanzu da Baaba tayi maganarsa, ko meke damunsa oho "Toh" ta amsawa Baaba, da sauri Safwan ya ce "Subhanallahi waye haka Baaba.?" Shi kam Sadiq tunda Baaba ta ambaci sunan M.J ya mike ya bar Falon ya shige ciki. "Ai ɗan uwar matarka ne shine ma mij.." bata ƙarasa ba saboda tarin daya kuma sarƙafe M.J wannan karon har yana faɗowa daga kan kujerar da yake, da hanzari ta nufi kitchen ta ɗauko ruwa daidai lokacin kuma Momi ta fito, dama suna zaune ne da Baaba su hira da su Zarah kiranta da akayi a waya ne ya sata miƙewa ta shige ciki. Da sauri ta ƙarasa inda Abdallah ke riƙe dashi tana tambayar meya faru, bai kula da yanayin ciwo da yake ciki ba da kuma suya da ƙirjinsa ke masa tamkar a tsaga a saka mishi ƙanƙara, saukowa yayi ya riƙe ƙafar Momi lokaci guda kuma ya fashe da kuka mai taɓa zuciyar duk wani me sauraronshi, sosai yake kukan yana faɗin ta yafe mishi. Tsakanin uwa da ɗa aka ce sai Allah, tuni tausayin ɗan nata ya kamata taji kamar hawaye zasu zubo mata amma ta kauda kai sannan ta kwace ƙafarta tayi tsaki ta ce "Sakeni dan Allah, sai yanzu kasan da cewa kamin kuskure har kake nema na yafe ma ka toh bazan yaf..." Salatin da Baaba tayi ne yasa ta kasa ƙarasa wa sakamakon M.J da ta gani kwance a ƙasa riris ba alamun motsi a tattare da shi, salati ta doka sannan ta tsugunna tana jijjigashi cikin tashin hankali. Baaba ce ta kalli Abdallah da tsantsar tausayin abokin nashi ya sashi zubda hawaye ta ce "Audullahi ɗauke shi mu tafi asibiti." "Babu inda za'a kai shi yana nan a gida." Daddy da tun ɗazu yake tsaye a ƙofar shigowa yana kallonsu ne yayi wannan maganar. Ƙarasowa yayi cikin ya isa har gaban Baaba ya ce "Ke mahaifiyace a gareni ban taba neman alfarma a gareki kin hana ba dan Allah karki dakatar dani daga abinda nayi niyya." Faɗan da yafi ƙarfin ka aka ce maida shi wasa, don haka Baaba bata kuma tankawa ba ta nufi hanyar ɗakinta duk da tana tausayin M.J amma can ƙasar zuciyarta tana murnar sakayyar da ya fara gani, shima Daddy hanyar ɗakinsa yana faɗin "Ban yarda ki zauna a inda Jawwad yake ba." daga haka ya shige, itama Momi miƙewa tayi tabi bayanshi fuskarta na zubar da hawaye. Matuƙar tausayin M.J ne ya cika zuciyar Abdallah, jiki ba kwari ya miƙe ya ɗauki ruwan da Baaba ta ajiye a center table ya watsa mai a fuska, cikin sa'a ya ja wata doguwar ajiyar zuciya irin na wanda ya farfado daga suma. Miƙewa yayi zaune yana ƙara fashewa da wani sabon kukan duk da rarrashin da Abdallah ke mai amma bai dakata ba, dan haka ya barshi ya cigaba da kukan har yayi mai isarsa, a lokaci anfara kiraye kirayen sallar magriba dan haka suka mike don zuwa masallaci. Sai da suka yi sallar isha'i sannan suka kuma nufowa gidan. Sai da aka kai ruwa rana kafin Daddy ya sauraresu, nan Abdallah ke basu labarin abinda Hajara ta aikata, Momi kam taso a kama Hajara a kulle amma Daddy ya ce yanzu abu ya wuce ba za'a tada shi ba. Daƙyar da siɗin goshi suka yafewa M.J laifukan da ya musu sannan Daddy ya jadda mishi cewa lallai ya samu Zarah ya nemi gafararta idan ba haka ba kowa rayuwarshi tana cikin haɗari. Abu da mai neman kuka jin Daddy ya ambaci sunan wacce yake muradin gani yasa yayi ta taɓa Abdallah kan ya tambayi Daddy inda Zarah take, gyaran murya Abdallah yayi sannan yace "Emm Daddy ko za'a gaya mana inda ita Zarah take sai muje har can mu bata haƙuri. Bayan haka kuma muna so a sasanta inda rabo ta koma gidanshi." "A sasanci me Abdallah?" Momi ta faɗa a firgice harda dafa ƙirji kamar wacce taga mugun abu. Kai M.J ya sunkuyar shi kuma Abdallah ya fara sosar kai. Murmushi Daddy yayi sannan ya ce "Ai Zarah ba bare bace duk inda take ma ai zata dawo gida idan tazo sai ya nemi afuwarta, sannan maganar sasantawa banaso na ƙaraji dan babu aurenshi akan Zarah maganar da akeyi yanzu ma ƙarshen satin nan za'a kawo sadakinta daga masarautar Yola dan ɗan sarki ke nemanta na daɗe da bashi umarnin hira saboda sun kawo kuɗin nagani inaso. A taƙaice dai a janye wannan maganar banson kuma jinta kunsan babu kyau neman aure akan aure". Daga haka Daddy ya sallamesu, M.J ji yayi gabaɗaya duniyar ta mishi zafi, Allah ba azzalumin bawanshi bane, a yanzu yana ji a ranshi lallai idan ya rasa Zarah ba zai iya cigaba da rayuwa ba. A haka ya tattaro kayansa gabaɗaya ya dawo gidansu ya tare a tsohon sashinsa. Yawan rashin lafiya da yake fama da ita musamman ciwon ƙirji da matsanancin ciwon kai ne yasa ya yanke shawarar zuwa asibiti don duba lafiyarshi. Gwajin farko likita ya tabbatar mai ya kamu da ciwon zuciya kuma ya kai matakin ƙarshe komai na iya faruwa da shi idan har bai kula ba, a haka likitan yayi mai gwaje-gwaje sannan ya bashi magunguna tare da shawarwari akan matakin da zai ɗauka na rashin sanya damuwa a rai. Da haka ya dawo gida. Tsawon lokaci yana fama da jinya babu wanda ya sani sai Abdallah shima kuma ya hana ya faɗama kowa, haka yake fama da matsanancin ciwo, baya yin sati ɗaya cikakke batare da ciwon ya tashi ba saboda damuwa da ya sakama kanshi akan Zarah musamman yanzu da ya tabbatar tana gab da kubce masa. Yana galabaita sosai idan ciwon nashi ya motsa don aman jini yake yi sosai amma duk da haka bai sanar da kowa ba. Watarana irin haka da ciwon nashi ya tashi lokacin yana gida a sashinsa, nan yayi ta aman jini har ya suma, a haka Abdallah yazo gidan ya same shi aikuwa bai ɓata lokaci ba ya sanarwa su Daddy nan aka ɗaukeshi zuwa asibiti
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24