Skip to content

Chapter 12

Chapter 12

Asp Zarah Book Two Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
Download Book

kuwa garin Abuja ta karɓi baƙuncin mutane da dama, sai da aka cika kotun nan maƙil babu masaka tsinke domin wasu a waje ma suka tsaya don babu gurin zama kowa nason ganin mutum ɗaya jal! da ya daɗe yana gallazawa mutane, bayan alkali ya zo ne aka gabatar da tuhumar da ake musu inda lauyan Gwamnati ya gabatar da kansa, babu batun lauyan da ke kare waɗanda ake tuhuma domin ba su da shi, cikin sauƙi ba ta re da wahalar da shari'a ba aka zartar musu da hukunci, Al'amin da Phalmata hukuncin kisa ta hanyar rataya inda sauran kuma hukuncinsu zaman gidan kaso na har abada. Daga haka Alƙali ya sallami kowa sannan aka bada umarnin wucewa da masu laifi gidan yari, kotu fa ta hargitse kowa da abinda ke fadi inda mutane da dama su ka so ɗaukar doka a hannunsu sai dai babu hali. Sosai na so ganawa da Alpha amma Sadiq ya hana ni gudun kada wani abun ya faru, haka ina ji ina ganin muka bar garin Abuja zuciyata sam babu daɗi saboda yadda na so mu yi sallamar ƙarshe da Alpha, sam a wannan lokacin sai nake jin tausayinshi na kamani matuƙa ta yadda mace ɗaya ta lalata mishi rayuwarsa ta duniya, ko da yake shima yana da laifin biyewa son zuciya don bai tsaya a inda Allah ya ajiye shi, yana da kyau na ɗaukar hankali wanda iya shi kadai zai iya zama jarinsa don ga dukkan alamu mutum ne mai farin jini, dole daga baya na cire tunaninshi a raina. Rayuwa kenan ban taɓa kawowa cewa al'amurana zasu warware cikin sauƙi haka ba. Tsarki ya tabbata ga Allah ubangijin talikai wanda baya zalunci sannan baya barin masu aikata zalunci. Kwananmu biyu da dawowa Gwamnati ta shirya mana ƙayataccen Dinner wanda ya haɗa da ƙarin girma, gabadaya jami'aina an musu ƙarin girma inda ni kuma Gwamnati ta tura ni ƙasar Malasia domin yin course na musamman a harkar tsaro, na so naki karban wannan tayin amma Daddy ya tursasa dole banj da wani zabi daya wuce hakan. Haka dai aka kammala taron Dinner ɗin zuciyoyin mutane cike da murna. Washe gari gaba ɗaya muna zaune a dinning mu na breakfast, M.J ne kawai bayanan a wannan zaman, cikin nutsuwa kowa ke cin abincin da Momi da kanta ta sarrafa shi, wayar Ammi da ke falo ce ke ta ƙara don haka ta kalleni ta ce "Little miƙo min wayar nan kinji, na ga wanda ke kirana haka da safe ko karyawa ba za'a barni nayi ba." Dariya muka yi duka kana na miƙe domin zuwa ɗauko mata wayar. Da sauri na taho na bata wayar sakamakon wani kiran da ya shigo, mijinta da ga ƙasar Egypt Dr. Adam ke wannan kira, cike da mamakin kiransa a wannan lokacin ta ɗaga, bai jira ta yi magana ba ya riga ta, ai kuwa sai gani muka yi ta mike tana faɗin "Alhamdulillahi Allah mun gode maka Ya Allah kai kadai ke yi a duk sanda ka so ya Allah muna ƙara gode maka da ni'imomin ka gare mu." ba su dade ba ta sauke wayar a kunnenta fuskar ta kaɗai ta isa fallasa farin cikin da ta ke ciki, zuba mata na mujiya mu ka yi cikin son ƙarin bayani, ai kowa fahimtar hakan da ta yi ne ya sa ta ce "Wani abin farin cikin ya kuma samun mu, wallahi ashe labari mai dadi ne Dr. Ke san gayamin tun dazu shi ke kiran wayar." cike da zumuɗi na ce "Ammi meya faru ne" Cikin fara'a ta ce "Rahama ce ta warke daga Trauma ɗin da ke damunta, yanzu haka ta dawo hayyacinta harta labarta ma Dr. Abinda ya faru waccan ranar shine ta ke daɗa tambayar duk ina muke." Wani wawan tsalle na daka na rungume Ammi da ke tsaye cikin murna, hamdala duk mutanen da ke wajen suka fara, an ɗau lokaci ana maida magana kafin Daddy ya ce "Ai kamata yayi a kira Rahama ɗin ta video mu ganta ta ganmu ko hankalinta ya kwanta." "Wallahi abinda na ce ma Dr. Kenan amma wai an yi mata allurar bacci saboda kukan da ta ke yi." "Toh masha Allah sai kuma ayi shirin tafiya koh" cewar Baaba. Dariya muka yi ganin yanayin yadda ta yi maganar. Daddy ya kuma ce wa "Insha Allahu kuwa sai tafiya a yau ɗin nan zuwa dare sai mu wuce. Tunda akwai private jet ɗin kamfani na sai mu wuce gabaɗaya kawai." "Haka za'ayi kawai Daddy amma dare kamar yayi nisa fa." Jiddah ta faɗa a shagwaɓe. "A'a Mamana(sunan da Momi ke kiran Jiddah da shi kenan kasancewar sunan Mahaifiyarta ne) babu kyau gaggawa aikin shaiɗan ne a bari zuwa daren mu shirya a nutse, zan kira Hajiyarku (Mahaifiyar Jiddah) na shaida mata nasan itama za ta so ayi tafiyar nan da ita." "Hakane ya kamata a shaida musu kam." Bayan mun kammala breakfast ɗin ne duk muka miƙe don fara shirye-shiryen tafiya, inda Saleem ya ɗauki Jiddah suka wuce gida don yin nasu shirin. Bayan na dawo daga rakiyar su Jiddah ne na tarar Sadiq na ƙoƙarin fitowa daga falon don zuwa sashensa, wani tight and friendly hug ya bani, dama nasan ɗazu kunyar su Daddy ya sa bai wani nuna ɗokin shi ba, cike da farin ciki ya ce "Little ina taya mu murna ragowar farin cikinmu ta dawo hayyacinta, bansan wani irin murna zanyi ba wallahi." sassauta riƙon da yayi min yayi sannan ya riƙe hannuwana biyu ya ce "Ku kaɗai ne farin cikina yanzu a wannan rayuwar, tabbas a yau na ƙara jaddadawa kaina alƙawarin amanarku da Abbanmu ya bani, zan ɗau alƙawari har a gaban ubangijina bazan taɓa bari ku ji kewa ko maraici ba, zan kasance Uwa, Uba sannan Yaya a gare ku ke da Rahama bazan bari ko ku ƙara yin kukan baƙin ciki ba matuƙar ina numfashi a duniya." hawaye ne ya silalo a kan fuskarsa, hannu na saka na share mai sannan na ce cikin zolaya "Ka tafi ka shirya ka ji young Abbah." Doka ya kaimin cikin sauri na sunkuya na wuce ciki da gudu, kai tsaye ɗaki na nufa don haɗa kayana. Wayata na ɗauka na kira Jummai sannan na gayamata ta baiwa Raliya 1million sannan ta sallameta idan da hali ma ta kaita har gaban danginta. Ƙarfe bakwai na dare muka private jet ɗin Daddy ya ɗaga damu zuwa ƙasar Egypt and here we're tare da Trauma Patient Rahama. Dukan wasa Rahama ta kaiwa Zarah lokacin da ta kawo ƙarshen labarin. Kana daga baya ta rungumeta tsam a jikinta tare da fashewa da kukan tausayin ƴar uwarta ta, sun jima a haka har sai da Sadiq ya yi magana kafin suka tsagaita yin kukan. Satinsu Daddy ɗaya a Egypt suka koma Nigeria inda aka bar Sadiq da Zarah saboda daga nan zasu wuce Malasia. Su ma kwanaki goma kacal suka ƙara jirginsu ya ɗaga zuwa ƙasar Malasia. _Bari mu leƙa amarya da ango._..✍🏻 *BY* *JASMINE*🌸🌸 *ASP ZARAH*👩‍✈️ *BOOK 2* *Page 9* Sai dai kafin ta kai ga miƙewa Sadiq ya ruƙo hannunta ya zaunar da ita ba ta re da ya ce komai ba abincinsa kawai ya cigaba da ci, tuni ta gane abinda

Table of Contents

Chapters

24 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24