Skip to content

Chapter 19

Chapter 19

Asp Zarah Book Two Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
Download Book

gefe guda Safwan na taya ta, tun Sadiq na tsokanarsu yana faɗin na marmari har abin ya wuce ƙarfin tunaninshi dan Safwan ko ƴar sa ce iya siyayyar da zaiyi mata kenan. Ana saura kwana biyu suna suka iso Nigeria,a Gombe jirginsu ya sauka har Safwan dan yace sai angama shagalin suna zai wuce Yola(Kome ya haɗashi da shagalin suna oho). Tarba ta musamman Momi ta musu da ƙayatattun abinci, sosai taji daɗi ganin yadda ƴarta tayi kyau sosai alamun kwanciyar hankali ya bayyana a jikinta, gefe guda kuma ga irin soyayyar da Safwan ke nuna mata dan har a gaban su Momi ba ya kunya musamman da suke mutane ne masu barkwanci. Sai da suka huta sannan aka haɗu a dinning dan cin abinci. Duk wannan wainar da ake toyawa M.J baisani ba saboda ba shi da labarin Zarah zata dawo don ba'a gaya mishi ba, yaushe ma ya zauna har da za'a faɗa mishi. Kullum da safe idan ya shigo ya gaishesu Office yake wucewa bayan ya ɗan tsakuri abinci kaɗan wani lokacinma baya iya ci, da Yamma ma idan ya dawo zai shigo yakan jima wani lokacin dan watarana harda shi ake yi dinner. Kasancewar su Zarah tafiyar safe suka yi yasa baisan da isowarsu ba. Sosai Baaba ke tsokanar Safwan tana mishi hira lokaci guda. Suka saba tamkar dama sun shekara a tare kodayake haɗuwar fuska ce kawai ba su yi ba. Bayan Sallar la'asar ne suka shirya zuwa gidan Jiddah harda Sadiq wanda sai da ya gama ƙorafi kafin Momi ta lallaɓashi su tafi tare. Shiga me kyau suka yi dukkansu, daga nesa idan mutum yaga yadda Zarah da Safwan suka jero ko maƙiyine sai ya yaba da yadda suka dace da juna. A daidai wannan lokacin kuma M.J na zaune a office yana aikin tunanin daya saba yi na Zarah, lokaci guda yaji ƙirjinsa ya buga da ƙarfi har sai sa ya durƙusa ya dafe gurin, jin kamar ciwonshi zai tashi ne yasa ya mike ya lalubi key ya fita dan zuwa gida saboda magungunan shi duk a gida ya ajiye. A hankali yake tuƙi har ya iso gaban wawakeken gate din gidan nasu, me gadi ya buɗe masa ya kunno kan motar cikin gidan. Ai kuwa idanunshi suka yi mugun gani. Zarah ce tsaye sanye da doguwar riga ba atamfa me kyau, kanta na yane da wani gyale me duwatsu a jiki, gefenta kuwa Safwan ne cikin wank tsadadden yadi kalar fari da hula ɓaka a kansa. Sun yi kyau sosai Sadiq na tsaye a gabansu yana ɗaukarsu hoto duk suna dariya. Duk da sun ganshi amma sai suka yi biris suka gama abinda suke yi Sadiq ya jasu suka fice daga gidan, jiki ba laka haka ya shige sashin sa a lokacin har jiri ya fara ɗebarsa aikuwa yana shiga ya zube akan doguwar kujera lokaci guda kuma tari me karfi ya turneƙeshi sai kuwa aman jini ya biyo baya. Ya daɗe cikin wannan yanayin kafin ya samu lafawar ciwon ya mike dakyar ya watsa ruwa sannan ya fito ya sha magani ya fara gyaran gurin da ya ɓaci bayan ya gama ne ya jona ruwan zafi a ƙaramin kofi ya haɗa tea me kauri yasha. Sannan ya kwanta da niyyar hutawa sai dai abu ya gagara domin daya runtse ido hoton Zarah da Safwan ne ke mishi yawo a kwakwalwa. Ajiyar zuciya me karfi ya sauke dan ya tabbar indai Safwan shine mijin da Zarah zata aura tayi sa'a don hatta shi da yake kyakkyawa babu abinda zai nunawa Safwan din indai wajen kyau ne ko kuma cikar sura, gashi kuma an faɗa mai ɗan gidan Sarauta ne dan haka dole ya koyi yadda zai rarrashi zuciyarsa akan Zarah dan tun farko shi ya jama kanshi. A haka har wani wahalallen bacci ya ɗaukeshi. Ɓangaren su Zarah kuwa sosai Jiddah tayi farin cikin ganinsu musamman aminiyarta, sai koɗa yadda Zarah ta koma take yi har tana faɗin itama za'a haɗa da ita a musu gyaran amarcin, sun yi godiya sosai da irin kayan da suka narka musu. Nan su Sadiq suka bar Zarah ta ƙarasa yininta sai dare suka dawo suka ɗauke ta nan suka dawo gida. Sai dare kafin Daddy ya samu ganawa da ƴaƴan shi da kuma sirikinshi, yayi murna sosai da zuwansu musamman da ya fahimci hankalinsu kwance ya ke babu alamar damuwa a tattare da su. Sun jima suna hira kafin kowa ya nufi makwancinsa. Kwanciyarta kenan a kan gado taji ana kwankwasa ƙofar ɗakinta, a tunaninta Momi ko Baaba ne amma tana buɗewa taga M.J tsaye cikin farar jallabiya, ƙofar tayi nufin rufewa amma yasa hannu ya dafe sannan ya tura da ƙarfi ya shiga ɗakin ya maida ƙofar ya rufe, kallon tuhuma take binshi da shi bai ko kula da yanayinta ba ya durƙusa a gabanta ya haɗe hannayenshi guri guda ya fara magana "Bansan dame zan fara ba, nasan nayi miki kuskuren da ban cacanci ki yafemin, amma gani a gabanki na cire duk wani girman kai ina roƙonki dan Allah ki yafemin abubuwan da na aikata a gareki bansan da wasu irin kalmomi zanyi amfani da su wajen baki haƙuri ba. Ki taimaka ki yafemin ko zanga haske a rayuwata. Dan Allah wallahi nayi nadamar komai dana aikata miki." Tsaki tayi a fili sannan ta ce. "Malam tashi ka ficemin a ɗakina dan Allah ba zan yafe ba ɗin." Ƙafar ta ya riƙo hawaye na bin fuskarsa ya ce "Nasan laifukana a gareki masu girmane ki taimaka badan halina ba ki yafemin." "Wai meye haka sakar min ƙafa karka jamin abin kunya ko ka manta mijin da nake shirin aura na cikin gidan nan ne " Me neman kuka an jefe shi da kashi awaki, nan take yaji zuciyarsa ta masa nauyi saboda ambatar Safwan da tayi aikuwa kamar yadda ya saba idan ranshi ya ɓaci, tari ya fara a hankali har yayi yawa jini ya fara biyowa bayan, hankalin Zarah ne ya tashi ganin yadda yake ta aman kuma najini gashi dare yayi tasan motsi kaɗan za'a iya jinsu. Tsugunawa tayi a gabanshi ta tallabo fuskarsa da hannayenta cikin murya irin na masu raɗa ta fara magana hankali tashe. "Dan Allah kayi haƙuri ka tafi a ɗakinnan wallahi na yafe maka duniya da lahira duk laifukan da kayimin da wanda nasani da wanda bansani ba wallahi duk na yafe, kaji dan Allah bari na taimaka maka ka tashi." Idanunshi a lumshe yaji wata irin nutsuwa ta sauka mishi lokaci guda, abu biyu ne sila na farko yafiyar da yaji ta ambata a gare shi abu na biyu kuwa a karo na farko ta taɓa shi da lallausan hannayenta kuma cikin kulawa take maganar. Wani yanayi ya tsinci kanshi a ciki lokacin da ta dafa kafaɗarshi tanason mikar dashi tsaye, ganin ta kasa ne ya sashi mikewa ya kalleta cikin ido ya buɗe baki da niyyar magana tayi saurin saka hannu ta rufe mishi baki dan a tunaninta zai iya yin wani aman dan haka tace "Ba sai ka godemin ba ka tafi kawai" Jiki ba kwari ya fice a ɗakin ya barta tsaye cikin tunanin iri iri, sosai taji tausayinshi ya kamata kasancewarta mace me rauni sosai, wannan wata irin lalura ce

Table of Contents

Chapters

24 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24