Skip to content

Chapter 7

Chapter 7

Asp Zarah Book Two Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
Download Book

tayi ta kalli agogo 2:05am kallonta ta maida kan Saleem dake sharar baccinsa hankali kwance, a hankali ta fara bubbuga bayansa har ya farka ya buɗe idanunsa ganinta a zaune ne yasa shima ya zauna yana miƙa ya kalleta yace "Lafiya kuwa me ya same ki.?" "Sa-Jid nayi mafarki Zarah na ta kirana tana faɗin na taimaka mata, zuciyata da jikina sun amsa bana jin daɗi sam ina da tabbacin cewa akwai abinda ke faruwa da ita." "Me zai faru da ita da wannan daren haba dan Allah mafarki fa ba gaskiya bane." "Na sani amma dai wannan yayi kama da gaskiya, miƙomin wayar can na kirata." Hannu yasa ya ɗauko wayar dake kan bedside drawer ya bata, cikin hanzari ta fara danna lambar Zarah tana kira amma kusan kira 30 babu amsa. Zuwa lokacin ta gama ruɗewa, kuka ta sakawa Saleem akan lallai sai ya kaita gidan Zarah a daren duk yadda yaso ta haƙura amma taƙi, sanin da yayi cewa idan damuwa zata iya jawowa ƙaramin cikin dake jikinta matsala ne yasa dole ya miƙe ya zura jallabiya ya ɗauki key ɗin motar suka fice a gidan, har zuwa lokacin kuma bata daina kuka da sambatu ba...✍🏻 *BY* *JASMINE*🌸🌸 *ASP ZARAH* *BOOK 2* *Page 5* ... Su uku ne zaune a cikin wani ƙayataccen falo da yaji kayan alatu tamkar na shugaban ƙasa Sadiq, Rahma da kuma Zarah, kallo ɗaya zaka musu ka gane suna cikin tsantsar farin ciki da suka daɗe basu samu ba duba da yanayin yadda fuskokinsu suka kasa ɓoye farin cikin da suke ciki. Rahma ce ta ajiye cup ɗin dake hannunta a center table ɗin dake gabanta sannan ta juyo ta dubi Sadiq dake nunawa Zarah abu a waya suna ƙyalƙyala dariya ta ce "Bazan iya tuna ranar ƙarshe da naga dariyarku haka ba musamman Zarah." "Ba mu da wata sauran damuwa ne shiyasa ki ka ganmu haka, ke ba abin farin ciki bane a gareki ace yau wanda yayi sanadin da iyayenmu suka bar duniya shima ya mutu ta dalilinmu, baya ga haka ƴar'uwar mu wacce muke tunanin ta zauce yau ta samu lafiya ingantacciya, kinga kuwa dole mu yi farin ciki." Sadiq ne yayi wannan sharhin bayan ya maida hankalinsa kanta. Gyaɗa kai tayi ciki da gamsuwa tace "Haka ne amma naku ne kawai ke fitowa fili, nawa na barshi a zuci." Zarah waccw tun da aka fara maganar bata tanka ba ta ɗago tace "Meye zai hana ki fito dashi fili mu haɗu mu yi murnar tare." Cike da zolaya Rahma tace "Yau kam naci girma na bar muku." Ɗaya daga cikin ƙananun pillows ɗin dake kan kujerar Sadiq ya ɗauka ya jefeta da shi cikin harara yace "Ke banson raini fa" Itama cikin zolaya tace "Kwanaki ƙalilan a ne tsakaninmu fa." "Duk da haka dai ya riga ki shaƙar iskar duniya." Cewar Zarah. "Haka ne toh na baka girman ka, yanzu daga nan ina zaku wuce." Shiru sukayi na wani lokaci kafin Sadiq yace "Daga nan Malasia zamu wuce, Little zata fara karatun masters ɗinta acan, ni kuma na cigaba da aikina." Fuska ta sauya kamar zatayi hawaye tace "Za mu ƙara yin nisa da juna.?" "Ki shirya mu tafi tare." fadin Zarah. Hararar wasa ta mata sannan ta kuma cewa "Na gaji da kawaici fa, tun ɗazu inaso ku ɗauko min hirar abubuwan da suka faru amma kun share." Dariya suka yi duka sannan Sadiq yace "Tun ɗazu na lura dake kawai na yi miki shiru ki furta da bakinki." "Na tambaya yanzu a gayamin meya faru." "Labari ne mai tsawo fa ki nemo biro da takarda" Inji Zarah. "A'a bani wannan baiwar sai dai na kira Sis Jasmine ta mana aikin rubutun." "Tom shikenan haka za'ayi." "Ke nake sauraro." 🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸 Ina cikin tsananin azaba a wannan rana da yaran Alpha suka shigo har gida sukamin rauni amma Yaya Jawwad yaƙi ko kula da lamarina bare yayi tunanin kaini asibiti duk da a lokacin babu dangantakar aure a tsakaninmu amma nayi tunanin zai taimakeni a matsayi na na ƴar'uwarsa sai dai hakan bai kai ga ci ba. Ganin sun bare yashe a falo cikin jini ne yasa nayi ƙoƙarin nafara jan jiki domin zuwa na saka Baba Mai gadi ya kiramin Daddy ko Sa-Jid saboda a halin da nake ciki a wannan lokacin nasan komai zai iya faruwa dani sakamakon jinin da ke zuba daga jikina, da jan jiki na fita har farfajiyar gidanmu zuwa ɗakin Mai gadi sai dai nayi rashin sa'a domin shima sun yi mishi duka bai san inda kansa yake ba. A lokacin nafara ficewa daga hayyacina saboda tsananin azaba da zafin raunukan dake jikina, ina cikin wannan halin ne naji ana horn a ƙofar get ta waje amma bani da kuzarin da zan iya xuwa na buɗe, an daɗe anayin horn ɗin daga baya kuma akazo jikin ƙofar ana bugawa, ganin gate ɗin a buɗe ne yasa su shigowa ba kowa bane illa Sa-Jid. Ko da suka shigo da ni suka fara yin arba a kwance cikin jini ai kuwa hankalinsu ya tashi sosai domin saida Jiddah ta suma dakyar ya samu ta nutsu kaɗan sannan ta taimaka mai suka shigar da ni cikin motar ba su ko kula da mai gadi ba bare su ɗauke shi mu tafi asibitin a tare saboda tsananin firgici da suke ciki. A guje Saleem ya ja motar muka bar cikin anguwar muka nufi hanyar asibiti, gudu yake yi tamkar zai tashi sama saboda azalzala da Jiddah ke yi masa, ni dai a lokacin sama-sama nake iya jiyo maganganunsu saboda zafin raunukan dake jikina da kuma jinin da har a lokacin bai daina zuba ba. Cak! Motar ta tsaya taƙi yin gaba ko baya duk yadda Saleem yayi ƙoƙarin ta motsa amma taƙi hakan ne yasa ya fito daga cikin motar cikin tsananin mamaki domin yasan motarsa lafiya lau take sannan akwai mai sosai a ciki, buɗe-buɗe ya fara yi yana dubawa ko zai ga ta inda matsalar take amma bai fahimci komai ba, ganin haka yasa itama Jiddah ta fito a motar tana taya shi dubawa ko zasu gano matsalar motar. Kamar wanda aka umarta haka ya sunkuya ƙasa tare da leƙa ƙasan motar, abinda ya gani a gurin ne ya matuƙar bashi mamaki, bakomai ne ya hana motar tafiya ba illa wani littafi ƙaramin dake ƙasan tayar gaba na hagu, cikin al'ajabi ya sa hannu ya zaro littafin da ƙarfi, cikin zarewar idanu ya nunawa Jiddah littafin wanda a bango cikakken sunana ne a rubuce cikin rubutu mai matuƙar kyau. A wannan lokacin bana tsayawa wasu maganganu bane saboda halin da nake ciki hakan yasa Saleem ya ajiye littafin a gaban motarsa zuwa lokacin da zan samu kaina. Bansan abinda ya faru ba domin a lokacin juriyata ta ƙare tuni na sume, a haka muka isa asibitin cikin gaggawa, ba mu sha wahalar samun likita ba domin a wannan asibitin Jiddah ke aiki sannan ita ke dubani lokuta da dama idan kalar hakan ta faru, a wasu lokutan ma bama zuwa asibiti idan zamana a asibiti na da hatsari. Emergency room aka shigar dani, nan da nan Jiddah da wasu likitoci biyu tare da nurses suka duƙufa domin ceto rayuwata, sai bayan da aka idar

Table of Contents

Chapters

24 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24