Skip to content

Chapter 3

Chapter 3

Asp Zarah Book Two Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
Download Book

zuwa tare da gaishesu, amsawa sukayi cike da fara'a kafin Zarah tace "Babu wata matsala ko Jummai.?" "Babu ranki ya daɗe, sai dai jiya tayi ƙoƙarin guduwa bayan na kwance ta zatayi amfani da toilet, amma ta rasa hanya ina kitchen naji ta shine nazo na ɗaure ta." "A tunaninta zata iya guduwa daga nan.?" -Jiddah "Haka take gani." wacce aka kira da Jummai ta bada amsa. Gabanta Zarah ta isa ta ɗago fuskarta da ta nuna alamun galabaita tace. "Kinga wannan Raliya acid ne a yau idan baki mana bayanin inda Alpha yake ba zamu kona fuskarki ta yadda ko kin kuɓuta babu yadda za'ayi ya aure ki kamar yadda kike da buri." A razane Raliya ta ɗago ta kalli Zarah tana mamakin yanda akayi tasan wannan zancen domin bayan ƙawayenta dake gidan da Alpha yake ajiyesu babu wanda yasan wannan zance, yanzu ta sadaƙar cewa ko bata gaya musu ba zasuyi amfani da asiri su karanci abinda ke ranta. Hawaye ne ya wanke mata fuska cike da takaicin yau zata faɗi wani sirri na masoyinta tace. "Zan faɗa miki." "Muna jinki." Saleem ya faɗa. 🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂 Malam Surajo Mai Idon Naira shine sunan da mutane kw kiranshi saboda tsantsar son kuɗi da yake da shi daga shi har Matar sa mai suna Lauratu. Malam Surajo da Lauratu ma'auratane da aka sansu da masifar son kuɗi da roƙo tare da bibiyar masu kuɗi suna musu fadanci, ƴaƴansu biyu kacal a duniya. Hajara itace ta farko wacce a yanzu take da shekaru 22 sai ƙanwarta Na'ima dake shekaru na 17. Duk wani buri sun ɗaurashi akan ƴaƴansu domin suna mishi kallon kadara wacce zasu dinga zamun kuɗi dasu. Saidai a cikinsu Hajara ce kaɗai tayi gadon iyayen nata domin tana da buri sosai, a cewarta ma bazata yi aure ba idan ba mai hannu da shuni ta samu ba, saidai a ɓangaren Na'ima abin ba domin yarinya ce mai nutsuwa da sanin ya kamata sam bata yi halin iyayen nata ba shiyasa basa shiri sam dasu. A daren ranar lahadi ne wanj abin farin ciki ya samesu a cewarsu, domin wani baƙo ne ya zo musu da wata kwangila mai tsoka. So yake su yi sanadin da ƴarsu Hajara zata auri ɗan shahararren mai kuɗin nan wato Eng. Muhammad Jawwad Sulaiman, batare da tunanin komai ba suka amince saboda zunzurutun kuɗin da za'a basu bayan haka kuma zasu samu kuɗi sosai idan ƴarsu tayi nasarar auren shi. Ya tsara musu komai da yadda Hajara zata haɗu da M.J tare da kalan aikin da yake so tayi mishi idan taje gidanshi, a haka suka rabu bayan ya ajiye musu makuɗan kuɗi domin yin hidima tare da faɗa musu cewa ta kasance cikin shiri domin a kowani lokaci zai iya kiranta domin su haɗu da M.J ɗin. Wannan abu ya matuƙar faranta musu rai, domin a ganinsu fa kakarsu ta yanke saƙa. Washegari kuwa kamar yadda yace, ya kirasu tare da yin magana da Hajara bayan ya gama gaya mata abinda zatayi idan ta fita. A ɓangaren M.J kuwa bayan ya sha magani ya ɗan samu sauƙin abinda ke damunshi, shiryawa yayi ya fita zuwa gurin aiki domin bazai iya zama a gidan ba. Yana tafe zuciyarsa cike da tunani kala-kala, bai ankara ba hannu motar ta kwace mishi cikin rashin sa'a kuwa ya bige budurwar dake ƙoƙarin tsalleke titin tana sanye ta dogon hijabi har ƙasa milk colour, da hanzari ya taka birki ya kashe motar cikin tashi hankali ya fito ya sameta a zaune tana ƙoƙarin miƙewa alamun motar bata taɓata sosai ba. "Sannu kinji baiwar Allah, kiyi haƙuri, daure ki mike na kaiki asibiti a duba ki." Cikin sanyin murya tace "A'a banji ciwo ba ka barshi kawai." tana mikewa da kyar tamkar saniyar dake naƙuda. "Kar muyi haka dake dan Allah muje na kaiki ko da Pharmacy ne a duba ki." Babu musu ta bishi tana takawa dakyar har ta ƙarasa inda yake tsaye ya buɗe mata ƙofar motar yana jera mata sannu babu adadi. Bayan shigarta ne shima ya shiga motar ya tada ta suka bar gurin zuwa asibiti.....✍️ _Kai na na mini ciwo_.🥺 *BY* *JASMINE*🌸🌸 *ASP ZARAH*👩‍✈️ *BOOK 2* *Page 3* Da kwatance take nuna masa hanya ya Isa har ƙofar gidansu bayan ya kaita Pharmacy an duba lafiyarta duk da ba wani rauni sosai ta ji ba, ita ta fara shiga cikin gidan jim kaɗan kuma Na'ima ta fito ta gaidashi tare da faɗin ance ya shiga daga ciki, babu musu kuwa ya bita har cikin gidan inda aka shimfiɗa masa tabarma a tsakar gurin Inda su Malam ke zaune tare tare da Hajara. Bayan gaishe gaishe ne M.J ya kuma basu hakuri akan abinda ya faru, nan suka nuna babu wata matsala, miƙewa sukayi duka inda aka barshi da Hajara bayan ta kawo mishi sihirtaccen zoɓon da Ummansu ta haɗa mishi, duk da yake mutum ne mai ƙyanƙyami amma haka bai hanashi shan zoɓon ba ganin kamar yanayin mutanen baiyi kama da ƙazamai ba. Sun daɗe suna hira kamar da ma can sun saba duk da shi ba mutum bane mai yawan magana amma ya sake sosai yana hira da ita, ya jima kafin ya musu sallama ya tafi bayan yayi musu ɓarin naira tare da alƙawarin zai dawo ya duba jikin Hajara, haka sukayi sallama zuciyar wannan ahali cike taf da farin cikin samun wannan arziki da sukayi. Yana tafe amma zuciyarshi fal tunanin mutanen da yau ne ya fara haɗuwa dasu musamma ƴar su da ta riƙe mishi zuciya lokaci ɗaya yaji kamar sonta na barazanar kamashi, lokaci guda kuma zuciyarshi ta aminta cewa ya samu kalar matar da yake nema a fannin tarbiyya duk da yanason mace wacce tayi karatun boko, fata yake a cikin ranshi Allah yasa babu wanda ya riga shi domin kam bazai yarda yayi rashin wannan kamilar mace ba. Da wannan tunanin ya isa office amma ya kasa taɓuka komai tunanin yadda zai ɓullowa su Daddy da zancen ƙara aure ne ya dameshi musamman da bayaso auran ya wuce nan da wata ɗaya ko biyu. ⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡ Cike da ƙosawa Jiddah ta kalli Raliya dake faman zubda hawaye tace "Kina daɗa ɓata mana lokaci fa idan ba zakiyi magana bane ki faɗa tun wuri mu samawa kanmu masalaha." "Bansan ta yaya bane zaku isa ga inda Alpha yake domin nima bansan hanyar inda yake ba bare nayi muku jagora." ta faɗa gami da sunkuyar da kanta ƙasa. Cikin ɓacin rai Jummai ta kawo mata duka saidai bata kai ga isarta ba Zarah ta tare ta tana faɗin. "Sassauta Jummai abinda ta faɗa gaskiya ne amma tsaya muji ƙarashan zancen" komawa baya Jummai tayi tana huci kamar wani firgitaccen zaki. "Ke muke saurare Raliya bamu da lokacin da zamu cigaba da zama anan." Shiru tayi na wani lokaci kafin tace "An haifeni ne a garin Jos, ni kaɗai ce ƴar da iyayena suka haifa kuma mahaifina hamshakin mai kuɗi ne na ban mamaki yana da dukiyar da shi kanshi bai san adadinta ba, watarana sai harƙalla ta haɗasu da Alpha batare da yasan ko shi waye ba. A zahiri Alpha dukiyar mahaifina kaɗai yaso karɓa amma ganin mahaifin nawa yasan wasu daga cikin sirrikanshi yasa watarana da daddare yazo har

Table of Contents

Chapters

24 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24