Skip to content

Chapter 14

Chapter 14

Asp Zarah Book Two Complete Hausa Novel 1,207 words 0 views Progress saved
Download Book

gauraye falo ta re da suwar happy birthday to you, ido ta waro tana kallon mutanen falon cikin mamaki harda maƙotansu da matayensu, tuni ta ƙara rudewa ganin Jiddah da Saleem a gefe ɗaya, hawayen da ake kira na farin ciki ne ya sauko a fuskarta. Da sauri Rahama ta zo ta ja ta zuwa gaban tebur din da aka aje ƙaton cake kalar pink da fari, hannun ta kai da nufin yankawa Rahama ta yi saurin riƙe hannun, kallonta ta yi da alamun tambaya bata amsa mata ba sai ma zura hannayenta da tayi ta rufe mata idanu, kusan sakan goma sannan ta buɗe mata, sai da ta razana saboda abinda ta ga ni ta kuma ji, Safwan ne a durƙushe gabanta riƙe da ɗan ƙaramin akwati na zobe yana faɗin "Will you marry me (Shin zaki iya aurena)" Sam ta rasa a wata duniyar ta ke ciki, tana fata idan mafarkine ta yi gaggawar farkawa, kallon gefe da Jiddah ke tsaye ta yi, gira ta ɗaga mata tare da kashe ido ɗaya sannan ta rungumo Saleem a jikinta. Abin yaso baiwa Zarah dariya matuƙa yadda Jiddan ke yi kamar za'a kwace Saleem din. Bata san ya akayi ta gyaɗa kai ba sai ji tayi kawai an zura mata zobe a hannu. Tafi suka yi gabaɗaya sannan ne ta yanka cake ɗin. Ƙaramin shagali suka yi sannan kowa ya watse sai su Jiddah da zasu wuce Dubai da daddare ita da Saleem zasu je siyayyar haihuwa. Cikin ƙanƙani lokaci soyayya mai ƙarfi ta ƙullu tsakanin Safwan da Zarah, har wani lokacin suna mamakin junansu ta yadda basa iya ɗaukan awanni ba ta re da sun ji muryar juna ba, idan suka zauna hira kuwa da ƙyar Sadiq ke lallaɓa Safwan ya tafi gida ya kwanta idan dare ya yi, da ya shiga gida kuma zai kirata su ɗaura daga inda suka tsaya. Harta su Daddy sai da suka san da batun soyayyar nan domin Safwan dai ya yi wa Abbansa maganar Zarah inda shi kuma ya aika Waziri da wasu wakilansa har garin Gombe su ka tambayowa Safwan auren Zarah tare da bada kuɗin nagani inaso da goron tambaya kamar yadda ya ke a al'ada ya tanadar. Yau ma kamar kowani lokaci a ƙarshen mako sukan wuni tare ne harta ayyukan gidan tare suke yi, su na yi wani lokacin Sadiq na tsokanar Safwan mijin Hajiya, don shi Sadiq ba shi da wani girman kai irin na Yayu akan ƙannansu musamman idan su na soyayya da abokansu, ya na zama su yi hira sosai wani lokacin idan su ka yi faɗan masoya ma shi ya ke sasanta tsakaninsu idan bayanan kuma sai a kira Rahama ta video ta shirya tsakaninsu. Yana zaune saman durowar kitchen ita kuma tana gaban fanfo tana wanke-wanke, hirarsu su ke yi cikin nishaɗi kamar waɗanda suka ɗauki tsawon shekaru su na soyayya. Tufa ɗin da ke hannunshi ya gutsira sannan ya ce "Mrs. Safwan kinsan me ya sa ban takura anyi auren nan da wuri ba.?" Ba ta re da ta juyo ba ta ce "Sai ka fada" "Saboda inaso ki gama ƙarasa wannan karatun don idan na aure ki nasan ba zaki nutsu ki yi karatun nan ba saboda yadda zan ruɗa ki da salon soyayyata sai kin daina fahimatar kowani zance idan ba nawa bane." Dariya ta yi sannan ta juyo ta naɗe hannayenta a ƙirji tana kallon shi ta ce "Saboda ina da ƙaramar kwakwalwa koh.?" "A'a saboda soyayyar da zan nuna miki ta musamman ce kina buƙatar cikakkiyar nutsuwa don fahimtarta." "Toh Allah ya kaimu lokacin yasa kada ka canza abinda ka fada." "Bazan canja ba saboda ina miki ƙaunar da bana yiwa kowa irinta a duniyar nan." "Uhmm" ta ce cikin murmushi sannan ta juya ta cigaba da wanke-wanke suna hira har ta gama ta gyara gurin. Sai a lokacin ya sauko daga inda ya ke zaune ganin ta fara hada-hadar ɗaura abincin rana, kamar ko da yaushe idan yana nan yakan taya ta da ƙananun aiyuka kamar su yanka albasa, fera dankali, bare maggi da sauransu a haka har su gama girkin. A haka Sadiq ya zo ya tarar da su a kitchen ɗin ya kalli Safwan ya ce "Mijin Hajiya zo ka min wani aiki a falo." "Haba babban Yaya baka ga ina taya ta aiki bane." cewar Safwan. "Little ba shi umarni kinji abu zai min mai mahimmanci." Dariya Zarah ta yi ta ce "Ba ni na riƙe shi ba fa, jeka ta ya shi aikin mana" Hannunshi Sadiq ɗin ya kama su ka fice ta re suna dariya. Haka kullum suke kasancewa cikin farin ciki yayinda soyayyarsu ke da ɗa ƙaruwa. Kwanci tashi asarar mai rai a haka kwanaki ke shuɗewa har suka zama watanni. NIGERIA A watannin da suka biyo baya duk wanda ya kalli M.J zai gane hankalinshi ba'a kwance ya ke ba gabaɗaya ya rame ya yi baƙi, abubuwan da Hajara ta ke masa ya ƙaro musamman yanzu da take ɗauke da juna biyu babu kalar fitsarar da bata yi mishi idan ya nemi ya tanka sai ta yi iƙirarin zata zubda ciki, gashi Allah ya ɗora mishi son cikin sosai musamman da su Daddy su ka sassauta mishi tunda suka ji labarin Hajaran na ɗauke da juna biyu, a gefe guda kuma tunanin Zarah da ke addabar zuciyarsa duk yadda ya so dainawa amma ya kasa nan ya fahimci cewa sonta ne ya mishi mugun kamu sai dai yana ƙoƙarin ɓoye hakan don har a wannan lokacin bai daina zargin cewa tana bin maza ba musamman idan yayi la'akari da yadda ya ganta a hotel ta re da wanda ba muharraminta ba. Yana zaune a office ɗinshi cikin tunanin da ya saba ya ji ana kwankwasa kofar shigowa, umarni ya bada aka shigo sakatariyarsa ce riƙe da takarda a hannunta ta ce "Yallaɓai wannan saƙo ne aka kawo ance a baka." "Daga wanene saƙon?" "Bai fada ba yallaɓai ya ce dai a baka ne yana sauri zaku yi waya." Kan tebur ɗin ya nuna mata ta ajiye daga haka ta fice, hannun ya zura ya janyo takardar ya buɗe, wata irin zabura ya yi tare da miƙewa tsaye daga zaunen da ya ke. Zufa ce ta karyo masa lokaci guda wasu hawaye masu ɗumi suka sauko daga idonshi, sambatu ya fara yana kiran sunan Hajara. A haka Abdallah ya turo ƙofar ofishin ya shigo ya same shi cikin wannan yanayi, a kiɗime ya ke tambayarsa abinda ya faru. Bai iya magana ba illa takardar da ya miƙa mishi cikin zubda hawaye. "Innalillahi wa inna ilahi raji'un." shi ne abinda Abdallah ke maimaitawa bayan ya karanta abinda ke cikin takardar...✍🏻 *BY* *JASMINE🌸🌸* *ASP ZARAH*👩‍✈️ *BOOK 2* *Page 10* Fuska ba walwala ya ɗaga ido yana kallon M.J dake dube-dube a kan tebur ya ce "Me kake nema ne haka.?" "Abdallah gidan zanje naji ba'asi wallahi yau kome za'ayi sai na ci mutuncin Hajara a garin nan." Duk da suna cikin wani hali amma hakan bai hana Abdallah dariya ba ganin yadda gabaɗaya M.J ya birkice yana neman key ɗin mota bayan ga key din nan a gefen tebur amma tashin hankali bai barshi ya gani ba, kai ya kaɗa sannan ya ce

Table of Contents

Chapters

24 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24