Chapter 4
Chapter 4
gida ya same mu ni da iyaye ya basu zaɓin ko ya barsu a raye ya kasheni ko kuma ya barni a raye ya kashe su. Haka ina ji ina gani ya bani bindiga na kashe iyaye na da kaina, daga nan ban kuma sanin inda kaina yake ba sai lokacin da na farfaɗo na tsinci kaina a Alpha Villa." wani gauron numfashi taja mai bayyana abinda take faɗa yana mata zafi a rai kafin ta cigaba da cewa "Bahagowar Rayuwa muke yi acikin wannan gida ni da wasu daga cikin matan da yanayin rayuwa yakai su wannan wajen, na daɗe kafin nasan wasu daga cikin abubuwan dangane da Alpha a lokacin ne nagane cewa ba shi ne yaje ya samu mahaifina ba wani yaronsa ne domin a yadda ake bani labari babu wanda ya taɓa ganin wani ɓangare na jikinsa wanda za'a iya shaida shi dashi, tun daga lokacin na ɗau alwashin sanin wani abu dangane dashi. A haka na cigaba da neman kusanci da shi har zuwa lokacin da nayi nasarar ganin faratanshi waɗanda zan iya ganewa a ko'ina idan naga mai kalansu ko shi ɗin, bayan ya gano ni ne kuma ya saka aka shigar dani ɗakin duhu inda anan yake horar da yaran dake mishi akai. Ta haka ne nasan Alpha sosai har na kamu da sonshi matuƙa duk da har yanzu bai taɓa bayyana kanshi gareni. Na rantse da sarkin dake busamin numfashi wannan ne iya abinda nasani game da shi ko da kuwa zaku bani qur'ani na dafa iyaka gaskiya ta kenan." daga haka ta cigaba da rera kuka a hankali ta barsu kowanne da abinda yake saƙawa a ranshi. Zarah ce ta fara katse shirun ta hanyar tambayarta tace "A wani mataki kika tsaya da karatu kafin afkuwar wannan lamarin." "Ina shekarar farko a jami'ar Jos na fara karantar Mass com." Shiru suka kuma yi duka na wani lokaci babu mai tankawa kafin Jiddah tace "Akwai wani ɓoyayyen al'amari da kika sani dangane da rayuwarsa ko wani nasa?" Kusan mintuna uku kafin ta ɗago tace "Ehh na taɓa karanta wani kundin sirri a ɗakinsa, akwai wata da naga hotonta da sunanta Phalmata." A tare suka kusan haɗa baki wajen faɗin "Phalmata.??" fuskar Zarah da Jiddah cike da mamaki. "Meye alaqarsu da ita." "A yadda na karanta na fahimci cewa ita kishiyar mahaifiyarsa ce kuma tare suka fara duk wannan harkallar, a yadda na gani ma ita kaɗaice yanzu a duniya tasan sirrikanshi na da dana yanzu. Inajin idan kuka nemeta zata iya sanar daku komai akansa musamman a yanzu da suke halin gaba zaku fi samun ingantattun bayanai." "Kinsan wani abu dangane da inda zamu sameta ne." "Eh toh ita ɗin fasihiyar na'ura ce bayan haka kuma tana ƴan tsibbace tsibbace, ina ganin ta hanyar tsibbu ne kaɗai zaku iya isa gareta." "A ina take.?" Saleem ya tambaya cike da ƙosawa domin shi burinshi kawai yaji inda zasu samu wannan matar "Tana garin Dutse a Jigawa." "Zaki iya tuna adireshinta da kika gani a kundin." "Eh zan tuna harda fuskarta ma domin yanzu ba ita kaɗai take aiki ba kamar dai Alpha, idan ba sanin wani abu nata akayi ba zata iya haɗa mutum da wata daga cikin masu yi mata aiki a matsayin itace." Miƙewa Zarah tayi tana gyara tattarewar da kayanta yayi saboda tsugunno da tayi, kana ta kalli abokan tafiyar tata tace "Muje koh? Jummai ke kuma zuwa gobe ki wuce da ita gidanki ta cigaba da zama acan amma ki tabbatar da tsaro." "Toh ranki ya daɗe Allah ya tsare." Da haka suka fice zuwa inda motarsu take, kai tsaye office ɗin Zarah suka wuce domin tattaunawa. "Zamu ɗaukarwa Raliya malamin dazai dinga koya mata zane-zane domin lallai da taimakonta ne zamu samu zanen hoton Phalmata da yatsun Alpha." cewar Zarah bayan sun zauna zaman tattaunawa akan matsalar. "Nima nayi tunanin haka, amma bakya ganin koyamata zai ja lokaci? Ina ganin a neme mai zanen kawai ta dinga fasalta mishi ya zana koh." "A'a Saleem yarinyar tana da kwakwalwa sosai zata koya cikin ƙanƙanin lokaci musamman idan muka mata barazana, da kanta zata fi iya zana komai da ta sani ba kamar idan faɗa take yi ba." "Wannan haka yake, amma tsawon wani lokaci kenan.?" "Sa-Jid yau muna ɗaya ga wata, a cikin sati ɗaya Raliya zat gama koyan zane tare da yi mana zanen da muke buƙata, a sati biyun da zasu biyu baya na binciko inda Phalmata take ne, a satin ƙarshe na wannan watan kuma zanje Abuja na neme takardar shaidar kama Alpha kunga kenan a wata ɗaya zamu gama wannan task ɗin muje na gaba wato binciko inda Alpha yake tare da kamashi." Tafi suka mata cikin jinjina da barkwanci, Saleem ne yace "Wani lissafin ƴan sanda ne kaɗai zasu iya shi." Murmushi kawai tayi sannan tace "Zanyi magana da Daddy idan yaso shi sai yayiwa M.J maganar tafiyarmu Zamfara" "Shikenan wato har yanzu kunƙi sasanta kanku" cewar. Saleem Bata ce komai ba ta fara haɗa abubuwanta domin tafiya gida, tare suka fito ta shige motarta bayan sunyi sallama sannan suma suka tada motarsu suka wuce. A kwanakin da suka biyo baya sam Zarah bata zauna a gida ba saboda ta tsaya kai da fata wajen ganin Raliya ta koyi abinda suke buƙata, a ɗaya ɓangaren kuma suna shirye-shiryen tafiya Zamfara ita da ɗan'uwanta Sadiq da kuma Jiddah da Saleem domin tafiyar da zasuyi ba ƙarama bace saboda adireshin da Raliya ta basu yana da nisa da garin dutse sosai dan haka suna buƙatar su shirya sosai. Wannan dalilin ne yasa kwata-kwata basu haɗu da M.J ba. 💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕 A ɓangaren M.J da Hajara kuwa soyayya da shaƙuwa mai ƙarfi ne ya shiga tsakaninsu, basa iya ɗaukar dogon lokaci batare da sunji muryoyin juna ba. Da fari Hajara tanason auran M.J ne saboda kuɗinshi saidai daga baya ta gane shine irin mijin da take so kuma gashi ta samu dan haka ne ma tayi alwashin cewa idan akayi aurensu ta gama aikin da zata yiwa Alpha zata cigaba da zama da mijinta domin ta samu kalarta. Shima a nashi ɓangaren yana mamakin yadda cikin ƙanƙanin lokaci ya kamu da matsananciyar soyayyarta. Takurawar da Malam Surajo ke mishi akan idan yanason ƴarsa ya turo magabata ne yasa yau yasha alwashin bayan ya tashi a aiki zai biya ta gidan ya sanar musu komai zai faru ya faru. Ƙarfe shida ya tashi a office kai tsaye kuma gidansu ya nufa, saida ya tsaya yayi sallar magriba a masallacin dake unguwar kafin ya ƙarasa zuwa cikin gidan nasu. A harabar gidan ya ga motar Zarah hakan ya tabbatar masa cewa tana cikin gidan, ba ƙaramin daɗi yaji ba kuwa domin yana son duk abun da za'ayi ayi a gabanta. A babban falo ya tarar da su duka suna ƙoƙarin yin dinner Daddy, Momi, Sadiq da kuma Zarah, dan haka shima kai tsaye teburin ya nufa da suci abincin tare. Gaishe da iyayensa yayi kana ya baiwa Sadiq hannu suka gaisa fuska babu yabo ba fallasa ko da Zarah ta gaidashi sharewa yayi batare da ya amsa ba wanda duk su Daddy sun lura da hakan amma babu wanda ya tanka haka suka fara cin abincin cikin nutsuwa kowa da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24