Skip to content

Chapter 10

Chapter 10

Asp Zarah Book Two Complete Hausa Novel 1,209 words 0 views Progress saved
Download Book

taho a satinnan, cikin jindaɗi na amsa ina ƙara jaddada ƙaunata a zuƙatan waɗannan mutanen. Jidda ce ta zuba mana abincin, dafa dukan cous-cous da farfesun kayan ciki, sosai naji daɗi abincin kuma na ci sosai irin wanda na jima ban ci ba saboda a lokuta da dama ba na samun damar yin girki saboda aiki, dama kuma M.J ba abincina ya ke ci ba bare nayi tunanin dafa mishi. Ƙamshin turarensa ne ya fara sanar da ni zuwansa, mu na zaune su ka turo ƙofar ɗakin shi da Hajara cikin kyakkyawar shiga irin na masu morar amarci, da alama hankalinsu kwance yake kamar tsumma a randa. Da sallama a bakin Hajara, Baaba ce kaɗai ta iya amsa sallamar hatta Daddy kai ya kauda gefe. Ganin haka ne yasa suka gaida Baaba kaɗai sannan suka nemi guri su ka zauna. Jim ɗakin ya yi babu wanda ya tanka, Daddy ne ya ciro wata farar takarda daga aljihunsa sannan ya baiwa Sadiq ya miƙawa M.J da kansa ke a sunkuye, cikin son ƙarin bayani ya kalli Daddy sai dai ya kauda kansa gefe, hakan yasa shi buɗe takardar don ganin abinda ta ƙunsa. Cikin razana ya ɗago ya ce "Kotu! Daddy me na yi?" "An haɗa baki da kai wajen cutar min da ƴata." Da matuƙar mamaki mu ka ɗago a tare muna kallon Daddy, Baaba ce tayi ƙarfin halin cewa "Sulaimanu wanj zance nake ji haka, wa za'a kai kotu." "Ba wani abin tashin hankali bane fa Baaba, komai zai zo da sauƙi." Daddy ya faɗa. "A wani garin marasa hankalin aka taɓa aikata haka Sulaimanu? Kana nufin kenan Muhammadun ya fi ƙarfin ka eyeee. Kai ba za ka iya masa hukunci ba kenan har sai ka dangana da wasu a waje, kai ne uban ko shine? Ban yarda ba, ban amince ba, matuƙar na isa da kai toh ban yarje maka ka kai ƙarar Muhammadu kotu ba." Baaba ce ta yi wannan zance. "Baaba laifin da Jawwad yayi mai girma ne, ko da Gwamnati ne ta ji labarin abinda ya aikata ba zata barsa ba, ki bari kawai a hukunta shi." Cewar Momi "A'a ban yarda ba a nemi wata hanyar hukunta shi amma ba ta hanyar kotu ba." "Ko da yaushe wannan tsohuwar sai kin kaucar da mutane akan hanya." Sadiq ya faɗa. "Ka kiyayeni fa Habu, ba na wasa da kai." "Shikenan Baaba za'ayi yadda kike so, amma wannan karon Jawwad ya ɓata mana rai matuƙa dan haka zan yanke masa hukunci mai tsauri." Inji Daddy. "Yauwa ɗan albarka ai idan rai ya ɓaci hankalj baya gushewa." Daddy ne ya maida kallonsa inda M.J da Hajara ya ce "Ka tashi ka tafi banaso na ƙara ganin fuskarka." "Dad-dy!" M.J ya faɗa cike da rauni. "Ehh ka tafi Jawwad ba ma so ƙara ganin fuskarka a cikin mu." Momi ta faɗa cikin hawaye. Gwiwarsa ya zube a ƙasa da nufin ba ta haƙuri sai dai ta riga shi da faɗin "Ka bani kunya Jawwad, wallahi da nasan akwai ranar da zata zo da zaka yi sanadin shigata baƙin ciki kamar yadda nake ji a yanzu, da tun kafin Allah ya bani cikin ka zan roƙe shi ya hanani cikin ka, Allah ya jiƙan Rahama ko da ɗaure fuska nayi cikin wasa sai hankalinta ya tashi, kai da nake tunanin zaka maye min gurbinta sai gashi kaine mai son kashe ni da baƙin cikin ka, Allah ya w...." "Kul! Kada ki yarda ki ƙarasa, kin san munin da tsananin da fushin iyaye ke jawo wa ƴaƴan su kuwa? Banason ƙara jin kunyi mugun furuci akan yaron nan." Baaba ta katse Momi da ke magana cikin tsananin fusata. Gabaɗaya ya firgice da kalaman iyayensa, ya san fushin su akan sa babban musiba ne a gareshi, hawaye ne suka fara sintiri a kuncinsa. "Matuƙar na buɗe ido na same ka a ɗakin nan ban...✍🏻✍🏻 *BY* *JASMINE*🌸🌸 *ASP ZARAH*👩‍✈️ *BOOK 2* *Page 7* ..."Matuƙar na buɗe ido na same ka a ɗakin nan ban yafe maka ba." Momi ta yi wannan furucin cikin zafin rai. Da hanzari ya miƙe ya fice Hajara ma ta miƙe ta bi bayan shi ba ta re da ta ce komai ba. Nan Baaba ta rufe Momi da Daddy da faɗa, ta inda ta shiga ba ta nan take fita ba, su dai sai haƙuri kawai suke bata, daƙyar suka samu ta daina faɗan. A wannan ranar ma tare muka wuni da su cikin kulawa, wajen ƙarfe tara na dare ne muna zaune sai sallamar Ammi muka ji, cikin mamaki nake kallonta Momi kuwa sai dariya ta ke min tana faɗin dama taki sanar da ni ne saboda zumuɗi irin nawa. Cikin murna muka gaisa tana tambayata yanayin jikina, ko da lokacin tafiya yayi sai Ammi ta ce nan zata kwana, daƙyar aka samu Jiddah ta bi Saleem suka tafi gida. Tare muka kwana da Ammi tana bani kulawa kamar zata maida ni ciki. Kwana na goma a asibiti kuma naji sauƙi sosai sakamakon kulawar da likitoci suke bani a gefe guda kuma ga kulawar da su Momi ke ba ni. Tun waccan ranar kuwa ban ƙara saka M.J a idanuna ba, saboda su Momi sun ɗau zafi sosai, Ammi ce ma wani lokacin nake jin su suna magana a waya wanda yawanci roƙonta ya ke akan ta baiwa su Daddy hakuri akan fushin da suke yi dashi. A yadda na fahimta, ko kaɗan abinda ya same ni bai damu M.J ba fushin da iyayensa ke yi da shi ne kaɗai abinda yake damunsa. Kayana da ke gidansa kuwa tun waahegarin da Ammi ta zo suka je da Jiddah aka kwashemin aka maida min gidan Daddy, part guda aka waremin tamkar wata matar gida. Gabaɗaya mun gama shirin tafiya Enugu sallamar likita kawai muke jira, dama na riga da na jima da karɓar takardar shaidar kama Alpha dan damƙa shi a hannun hukuma a ko wani hali, dan haka abinda kaɗai nake jira shine na ƙarasa warwarewa don mu tafi Keruba. Tafiyar ta mutane bakwai ce Ni, Sa-Jid, Yaya Sadiq, sai wasu jami'aina na sirri guda uku da zamu yi tafiyar tare. A daren da na cika sati biyu ne a asibiti likita ya sallameni inda a washegarin ranar kuma zamu wuce Enugu, tafiyar da bamu da tabbacin ko zamu yi nasara, haka dai muke ta shiri zuciyoyi sam babu dadi. Kasancewar tafiyar mota zamu yi yasa washegari da asuba bayan munyi sallar asuba muka yi sallama da su Daddy muka ɗauki hanyar tafiya cikin motoci biyu. Sallah kawai ke tsayar damu a hanya amma duk da haka ba mu isa cikin garin Enugu ba sai wajen sha biyu na dare, hotel ɗin da muka kama ta internet muka nufa kai tsaye ba mu sha wahalar ganewa ba saboda munyi amfani da google map, cikin lokaci ƙanƙani muka isa wajen. Bayan karɓi makullan ɗakin ne muka wuce don kowa ya huce gajiyar da ke tattare da shi. Kwananmu biyu muna huce gajiyar hanya kafin ranar asabar da yammaci muka shirya tafiya garin Keruba kamar yadda aka kwatanta mana zuciyoyin mu cike da zullumi duk kuwa da kasancewar a daren wannan ranar kwana muka yi sallah muna neman zaɓin Allah a cikin lamarin. Sai Yamma lis kafin muka

Table of Contents

Chapters

24 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24