Skip to content

Chapter 8

Chapter 8

Asp Zarah Book Two Complete Hausa Novel 1,205 words 0 views Progress saved
Download Book

da sallar asuba'i kafin numfashina ya daidaita bayan sun gyaramin raunukan dake jikina sannan nasha ɗinkuna a waɗanda ke buƙatar ɗinki. Daga haka aka yimin alurar bacci sannan Jiddah da kanta ta turani ɗakin hutu. Sai a lokacin ta samu sukunin kiran Daddy ta shaida mishi abinda ke faruwa, ba'ayi mintuna ashirin ba kuwa sai gasu a cikin asibitin gabaɗayan su harda Baaba, ganin yanayina kuwa ta matuƙar ta da musu da hankali nan suka tambayi abinda ya faru, Saleem ne kaɗai ya iya buɗe baki ya musu bayani tun daga kan farkawar Jiddah daga bacci har zuwa lokacin da nake kwance bansan me ke gudana ba. Sun shiga damuwa sosai musamman Baaba da a lokacin take tunanin na mutu ne ake ɓoyewa, shi kuwa sarkin zuciya Sadiq ya kasa furta ko kalma ɗaya amma kallo zaka yi masa ka gane yana cikin tsananin damuwa da ɓacin rai duba da yadda idanunsa suka sauya kala zuwa jajaye sannan kyakkyawar farar fuskarsa ta rine tana nuna alamun ɓacin rai. Haka suka zauna shiru har ƙarfe goma na safiya amma ban farka ba wannan dalilin ne yasa Momi da Daddy suka nemj komawa gida domin taho da abinda ba'a rasa ba na buƙatar majinyaci domin ita kam Jiddah ta ce babu inda zata motsa sai taga farkawa ta, tana gefen Baaba a zaune acan wata kwanar ɗakin suna sharar kwalla lokaci lokaci. Duk cikinsu babu wanda yayi tuna M.J bare ayi tunanin abinda ya hanasa zuwa a matsayinshi na mijinta, Sadiq ne kawai ya farga ga haka tun lokacin da yazo baiga M.J a wajen ba yasan akwai wata manaƙisar a ƙasa saidai ya share saboda jiran farfaɗowata amma cikin ranshi ya ɗau alwashin cin zarafin M.J matuƙar ya bincika ya samo da sa hannunshi a cikin abinda ya faru dani. Wani abu da nafara manta wanzowarsa a cikin shafin rayuwata shi ya sameni a lokacin da nake tsaka da baccin dole da likitoci suka sani yi sakamakon allurar baccin da akamin, duk da daɗewar shekaru amma ko a ina naga wannan fuskar zan ganeta, kinsan wacece?" Rahama dake sharar kwallar tausayin ƴar'uwar tata ce ta girgiza kai alamun a'a domin ba zata iya bude baki tayi magana ba, tabbas ta daɗe bataji ko a labari ba wacce ke da irin ƙaddarar Zarah, domin da ta fita daga wannan take kuma shiga wata batare da ta warke ƙuncin da ke ranta ba. Numfasawa Zarah tayi sannan ta cigaba da cewa. Ba kowa bace face Almajirata wacce na daɗe da fara manta abinda ya gudana a tsakaninmu, ina tsaka da wannan baccin nayi mafarkinta ta zo min tana hawaye tace "Kamar yadda na ɗaukar miki alƙawarin cewa zan barki a baya amma zan kuma dawowa domin taimakonki, Batula ban taɓa nesa daga inda kike ba saidai kawai ina ɓoye kaina ne saboda alƙawarin da na miki na rashin bayyana a gareki. Sai dai a yau na bayyana gareki ne domin taimaka miki akan abinda kw jefa rayuwarki cikin ƙunci. Ki riƙe wanna littafin duk wasu bayanai da zaki buƙata na Alpha yana ciki baki da buƙatar zuwa wani waje domin samo su." Ta ƙarashe maganar tana mikomin wanj ƙaramin littafi dake hannunta, cike da rauni na miƙa hannu na karɓa ina kallon jikin littafin, ɗagowa nayi da nufin tambayarta saidai kuma banganta ba. A daidai nan na farka daga baccin a firgice ina faɗin "Kin bani littafin.?" a gaggauce Jiddah ta matso kusa da ni ta riƙeni tana ƙoƙarin maida ni na kwanta. Bansan abubuwan da nake furtawa ba a lokacin sai dai naji Jiddah na faɗin "Littafin yana cikin motar Saleem bari na kira shi ya shigo miki dashi." daga haka na maida kaina ina sauke numfashi a hankali. Shuɗewar mintuna goma ne ya dawo dani hayyacina, a lokacin ne kuma na fara jin raɗaɗin raunukan dake jikina, haka nayi ta daurewa har zuwa lokacin da wata Nurse ta shigo, ganin idona biyu ne yasa ta kuma suka dawo da likita ya ƙara duddubani tare da tambayata inda kemin ciwo, nan na faɗa mishi ina jin zafin raunukan jikina cikin sanyayyar muryata ta marasa lafiya, take ya haɗa allurai yayi min sannan suka fice a ɗakin suna mai ƙara yimin addu'ar samun sauƙi. Fitarsu ke da wuya Baaba da Jiddah suka ƙaraso kusa da gadon nawa suna jeramin sannu kamar zasu aro baki, da taimakon Jiddah na samo na miƙe zaune bayan ta saka filo a bayana na jingina da gadon, zafin da nakeji ya ragu sosai sakamakon allurar rage zugi da akamin, wannan ne ya bani damar yi musu ƴan tambayoyi game da mutanen da nake da tabbacin zasu zo dubani, nan Jiddah ke gayamin Daddy da Momi suna hanya sunje gida su dawo ne, Saleem kuma ya fita samo musu wani abu su ci kafin Momi ta kawo abinci sai Sadiq da ta nunamin wanda kw zaune a can gefe. Sai a lokacin na juya a hankali na kalli inda take nunamin ai kuwa na ganshj zaune yana aikomin da murmushin da iyakarsa fuska nima na maida masa martani, a hankali ya miƙe ya tako zuwa inda nake ya dafa kafaɗa ta cike da kulawa yake tambayata ya jiki na amsa mishi. Shiru ya biyo baya kafin ya nisa yace "Little meya faru ne? ina mijinki yaje ne da bai samu damar kawo ki asibiti ba sai su Jiddah ne suka kawo ki? Meyasa tun zuwanmu ba muga yazo domin duba lafiyarki ba ko baya ƙasar ne?" "Habu ka kiyayeni fa, yarinyar na gadon jinya zaka tasa ta a gaba kana yi mata irin waɗan nan tambayoyin da basu shafi lafiyarta ba." Baaba ta faɗa cikin hargowa. Murmushi nayi mai ciwo sannan na kalleta nace "Baaba ina jin ƙarfi sosai a jikina yanzu,karki ga laifinshi dan yamin waɗannan tambayoyin. Yaya kasan meye a tambayarka akwai gyara, a yanzu zaifi dacewa ka dinga danganta Yaya Jawwad a matsayin Yayana ba miji ba, domin a yanzu yadda nake nan babu igiyar aurensa a kaina." Na faɗa ina zamewa da nufin na koma na kwanta. "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un, Allah yasa kunnuwana ba daidai suka jimin ba." Abinda Momi ta faɗa kenan wacce suka shigo a tare da Daddy suka tarar ina wannan zancen, gabaɗaya muka juya gareta muna kallonta har ta ƙaraso inda nake ta zauna tana fuskantata tace "Zarah dan Allah me naji kina faɗa yanzu? Kice min ba abinda naji kika faɗa ba dan Allah.?" ta ƙarashe maganar tana riƙo hannuna ɗaya da babu ciwo, tausayinta naji ya kamani zuciyata tayi nauyi, tabbas nasan banason auren nan nayi biyayya amma mutuwar aure sam babu daɗi musamman ga mace mai irin aikina lokaci guda mutane zasu juya maganar zuwa wata daban, ciwon ƴa mace na ƴa mace ne, nasan tabbas Momi tana jin wani irin yanayi a cikin ranta kwatankwacin yadda nakeji, ban taɓa son M.J ba har gobe amma ban taɓa fatan ace aurenmu dashi ya rabu ba. Cikin murya mai rauni na ce "Ehh Momi hakane aurenmu da Yaya Jawwad ya rabu a daren jiya." wasu hawaye masu ɗumi naji suna zubomin saboda hoton abinda ya faru a wannan daren daya bayyana cikin kwakwalwata. Salati suka saka gabaɗaya illa Jiddah gwanar kuka da tuni ta fara zubda hawaye,

Table of Contents

Chapters

24 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24