Skip to content

Chapter 6

Chapter 6

Asp Zarah Book Two Complete Hausa Novel 1,207 words 0 views Progress saved
Download Book

yi bacci ba a wannan lokacin harda Zarah dake zaune gaban na'urarta tana gabatar da wani aiki gefenta kuwa wani ƙaramin kofi ne da shayi a ciki sai tururi yake yi, tana sanye da riga da wando na bacci mai santsi kalar sararin samaniya ta ɗaura wata hula mai gashi a kanta, gabaɗaya hankalinta ta maida akan aikin da take gabatarwa. A hankali ta miƙe ta nufi window ɗin ɗakin saboda jin alamun kamar hayaniya na tasowa daga farfajiyar gidan, labulen ta ja kaɗan tare da leƙa tsakar gidan ga mamakinta sai taga kamar gilmawar mutum, ganin dare ne yasa bata wanj damu ba ta koma inda take zaune da ta cigaba da aikinta. Zamanta ke da wuya ta ji an hayaniya da kururuwar Hajara a babban falon tare da sallallami da M.J ke yi, take ta gane cewa wasu sun shigo cikin gidan, da sauri ta miƙe ta ɗauki jacket ɗinta ta saka sannan ta zari ƙaramar bindigarta ta nufi falon. Ai kuwa kamar yadda ta zata mutane ne a falon su tara kowanne da shiga mai kyau fuska a rufe, uku daga cikinsu ne kawai maza amma duk sauran mata ne, ganin fitowarta ne yasa wasu mata su huɗu suka nufeta da nufin rikota, wani wawan naushi ta kaiwa waɗanda ke da nufin riƙe mata hannu da duka hannuwanta biyu sannan ta sunkuya ta kaiwa wacce take gabanta naushi a ciki take ta durƙushe saboda zafin da taji. Sai dai kafin ta kuma wani yunƙuri wasu suka tura ta ta faɗi ta gaba kafin ta ɗago suka yi nasarar ɗaure mata hannaye. Ɗaya daga cikinsu ne yayi maganar su ƙyale Zarah haka sannan ya juya ya kalli M.J ya ce "Ran matan ka ko kuma dukiya.?" Cikin kauda kai M.J dake riƙe a hannun ƙarti biyu da mace ɗaya yace "Malam ni matata ɗaya ce kuma gata nan" ya nuna Hajara sannan ya cigaba da cewa" Ku kama wacce ta muku laifi ku rabu da mu." Dariya yayi sannan yace "Ya za'ayi mu yarda da hakan bayan a mun shaida ɗaurin auren ku." Shiru yayi na wasu mintuna sannan yace "Idan kuna so ma zaku iya shaida warwarewarsa." Cike da dariya mugunta ya kuma cewa "Mai zai hana kuwa." Cike da takaici Zarah tace "Yaya Jawwad kada kayi abinda zaka zo kana da na sani, ina da rauni sosai sannan ni marainiyace. Kada ka lalatamin rayuwa ta hanyar maida ni ƙaramar bazawara." Bai kula da maganganunta ba ya ce "Na sake ki saki ɗaya Zarah." Tabbas mutuwar aure babu daɗi ko da babu soyayya wannan dalilin ne yasa Zarah taji zuciyarta tayi mata zafi sosai lokacin da ɗan'uwanta ya furta kalmar saki a gareta. "Kinsan abinda ya kawo mu dan haka ki bamu salin alin saboda yau zamu yi ta mukare tsakanin mu da ke." Mutumin ya kuma faɗa batare da ya kula da halin da take ciki ba, kauda kai tayi gefe tana addu'ar Allah ya bata nasarar kunce kanta duk da suna da yawa tasan zata iya musu mugun lahani ba tare da makami ba ma. Saura ƙiris ta fasa ƙara saboda wani gigitaccen zafi daya ziyarce ta a gefen cinyarta, kallonta ta maida gurin taga ashe ɗaya daga cikin matan nan ne ta yi mata muguwar yanka a cinyarta take kuwa jini ya ce dama hanya nake nema nan ya fara zuba tamkar kwararo shi ake yi, raɗaɗi take ji sosai amma hakan bai sa ta amsa tambayar da ya kuma mata ba, ya ce "Ba zakiyi magana ba ke wace iriyar yarinyace mai taurin kai ne, mtsssw ku shiga ku bincika min ko ina a cikin gidan nan." Dukkansu suka nufi hanyar da suka ga Zarah ta fito mutum uku kaɗai suka bari biyu na tsare da M.J da Hajara sun saka musu bindiga akai sai babban dake gefen inda Zarah ke ɗaure yana wasa da wuƙar hannunshi yayinda ɗaya hannu ke rike da bindiga. Kusan mintuna arba'in suna dube-dube a cikin gidan amma basu ko ga wata alamar da zata nuna musu cewa Diamonds ɗin suna cikin gidan ba, cike da rashin kwarin gwiwa suka dawo suka sanar da shi, bai ce komai ba ya zaro waya ya daddanna sannan ya kara a kunnenshi jim kaɗan ya fara magana yace "Yallaɓai jiya i yau fa, taurin kan yarinyar yayi yawa ta tushe kowace hanya bata bamu damar sanin komai ba." Huci ya furzar mai zafi kana yace "Wannan karon inaso ku taɓa Zarah, ina so taji a lafiyarta cewa ba'a gardama dani, ina so taji lallai cewa bazata iya cigaba da ajiyar Diamonds ɗin nan ba, lallai ku yi mata mummunan lahani kamar yadda zuwa yanzu na tabbatar idan Raliya tana raye to tana cikin mawuyacin hali." "Angama ranka ya daɗe." daga haka ya katse wayar ya kalli matan dake tsaye ya ce "Ku cika aiki" tamkar suna jira haka suka ruftu su biyar akan Zarah kowa da irin dukan da yake kai mata amma duk da haka ko tari bata yi ba bare ayi tunanin zatayi kuka. Karo na farko Hajara taji mugun tausayi da dana sani sun baibayeta, ciwon ƴa mace na ƴa mace ne, sosai taji da na sanin haɗa kai da ita da akayi tun farko har zuwa yau da suka shigo cikin gidan nasu. Shikuwa M.J ba yadda za'ayi ka gane yanayin da yake ciki domin fuskarsa tana nan yadda take. Cikin mintuna ƙalilan farin tiles ɗin dake falon ya fara rinewa yana yin ja saboda jinin dake gangarowa daka jikin Zarah sakamakon bugu da yanka da suke jikinta, ganin kamar ta daina numfashi ne yasa ya dakatar da su sannan suka fice a gidan. Da hanzari Hajara ta rarrafa ta isa kanta hawaye na biyowa a idanunta ta juya ta kalli M.J ta ce "Hubby ɗauki key da sauri mu kaita asibiti." "Ni? Asibiti? Babu inda zan fita da daren nan, ita ta jawo wa kanta." "Ka dubi halin da take ciki mana dan Allah ka taimaka." "Yaya Jawwad dan Allah ka kiramin Daddy ko da bazaka kai ni asibitin ba." Zarah ta faɗa a galabaice, numfashinta na fita ɗaiɗai. Bai kula ta ba ya zo yaja hannun Hajara suka nufi ƙofar part ɗin shi, tsayawa yayi cak! Sannan ya dawo ya tsugunna a gabanta yana ƙare mata kallo shi kansa yasan tana buƙatar taimako na gaggawa amma yana jin zafinta sosai a ƙasan zuciyarsa, gyaran murya yayi sannan yace "Kinsan yanzu babu igiyar aure tsakanina dake, dan haka zan taimaka miki ne kaɗai a matsayin karuwar da nakeso ta tuba ga Allah kafin ta mutu, wannan ne kaɗai gatan da zan miki, kin amince na taimaka miki.?" "Zan fi ƙaunar na mutu a haka matukar da wannan ƙudurin zaka taimake ni, na tsane ka, baka da tausayi ko kaɗan, kai mara imani ne." Kafaɗa ya kaɗa ya mike sannan yace "Duk yadda kika gani sai ki kira wanda kike jin shi zai iya taimakonki ko a cikin abokan watsewarki ne." daga haka yaja matarsa suka shige suka barta a nan kwance. Cikin dakiya da juriya ta miƙe zaune tana jan jiki harta isa ƙofar da zata sada ta da farfajiyar gidan cikin tsananin azaba da ciwo. A firgice ta miƙe daga baccin da take yi, juyawa

Table of Contents

Chapters

24 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24