Skip to content

Chapter 16

Chapter 16

Asp Zarah Book Two Complete Hausa Novel 1,208 words 0 views Progress saved
Download Book

ya waiwayo ba. Cikin mamaki M.J ya kalleshi ya ce "Amma shine baka taɓa fadamin ba Abdallah." "Eh saboda naga kai ba mutum bane me yarda da mutane." Nan Abdallah ya labarta mishi abinda ya faru a waccan ranar lokacin daya tambayi wannan saurayin. Abin mamaki sai ga M.J yana zubar da hawaye yana faɗin "Meyasa baka gayamin ba, kabarni ina cutar baiwar Allah meyasa Abdallah." Sauka akan hanya Abdallah yayi sannan yayi parking ya kashe motar ya juyo ya kalli M.J yace "Na ɗauka idan anyi muku aure zaka nutsu sai naga ba haka bane, ba wannan ba ma saurari wannan kaji." ya ƙarashe faɗa yana danna wayarshi, sai kuwa ga muryar Baaba rangaɗau na fitowa a wayar da alama recording akayi bata sani ba. "Audullahi ina sane da duk abubuwan dake faruwa a gidan Muhammadu, kasan Zara'u bata da wata abokiyar shawara da ta wuce ni, na dade da sanin cewa yana zarginta da aikata zina idan ta fita aiki. Wallahi duk da batare muke fita ba ko Qur'ani aka bani zan dafa nayi rantsuwar cewa Zara'u bata taba ko da tunanin aikata wani abu da bai dace da wani ba, nasan cewa tana yin basaja don kama masu laifi idan sun kasance masu neman mata. Sau da dama tana zuwa nan ta sameni akan ajiye aikinta saboda zargin da yake mata ni nake hanata, ba gori zanyi ba amma Zara'u ta bada rai da lafiyarta don kare dukiyar mahaifinsa. A sanadin wannan dukiyar ne akayi asaran rayuka takwas. Ita fa iyayenta biyu ta rasa, kasan zafin da mutum yake ji idan ya rasa iyayensa kuwa kuma a lokaci guda sannan ƴar uwarta da zata lallasheta ta rasa hankalinta, amma duk da haka bata karaya ba ta cigaba da tsaron wannan kadara. Da ace zan shaida maka irin halin da ta shiga a waccan lokacin sai ka zubda kwalla amma duk da haka bata birge Muhammadu ba shi burinsa a kullum yaga ya ƙuntatawa rayuwarta duk da kasancewarta marainiya, ina sane da abinda ke faruwa da ita haka ma iyayensa duk sun san irin ƙuntatawar da ɗansu ke mata saboda na shaida musu duk da Zara'u ta gargaɗeni akan hakan, a ranar da mahaifiyarshi taji wannan batun da ba dan ni ba sai tsinuwarta ta tabbata akanshi, ni na hana hakan. Na so ace kafin rabuwarsu mu'amala ta aure ta shiga tsakaninsu don ya tabbatar da zargin da yake mata ba gaskiya bane amma hakan bai tabbata ba sai gashi daga ƙarshe ma ya mata saki irin na wulaƙanci. Ko ba yanzu ba Audullahi ko da ƙasa ce ta rufe mana idanu na tabbata sai Muhammadu yayi nadamar abinda ya aikata don laifine me girma ƙuntatawa maraya." Ƙitt! Abdallah ya kashe wayar batare da ya kula da yanayin da M.J ke ciki ba ya ɗora da cewa "Tun ranar da muka fara ganin Zarah a Abuja naji ta burgeni matuƙa musamman yanayin shigarta, idan baka manta ba bayan na ajiye ka a gida a waccan ranar na fita naje adireshin da muka ji Zarah na fada a waya, ba wani abu ya kaita ba wata abokiyar aikinta ce ta ɗauka suka wuce gurin wani taron ƙarawa juna sani da ake gudanarwa ba kamar yadda kayi zargi ba, ina wajen har sanda aka karramata na musamman a matsayin wacce ke baiwa ƙasa babbar gudumawa akan tsaro, na so kwarai na karɓi lambarta sai kuma kiranka ya shigo wayata na tafi da niyyar zuwa na dawo kuma muka tafi wani gurin, a ranar da muka ganta a hotel a bauchi kuwa ban bar wajen ba sai da na tabbatar ba abin banza ya kaita ba. Na barka ne kayi aiki da hankali da kanka sai gashi ka kasa. Dawowata ƙasar nan da banga Zarah a gidanka ba shine naje har wajen Baaba muka yi wannan hirar batare da na bari tasan ina ɗaukar muryarta ba." Kuka wiwiii! M.J yake yi tamkar ransa zai fita har numfashinsa na ɗaukewa yana dawowa, rarrashinsa Abdallah ya fara yi yana gayamasa kalamai masu tausa zuciya ya ce "Ba kuka ya dace kayi ba M.J tsawo lokacin nan kana ɗauke da zunubai manya akanka kamata yayi ka godewa Allah da ya ganar dakai tun waɗanda kayiwa laifin suna numfashi ta yadda zaka iya neman yafiyarsu. Zargi zunubi ne ko da ya kasance gaskiya, kaga a sanadinshi kayi manyan laifuka da har Allah ma yana fushi da kai, kayi zargi sannan ka ƙuntatawa marainiya ta hanyar hakan zunubi ne babba domin Allah yana fushi da duk wanda zai cuci maraya komin ƙanƙantar cutar, sanadin zargi ka saka iyayenka suna fushi da kai musamman mahaifiyarka da har tayi iƙirarin tsine maka wallahi kana cikin uƙuba da fushin Allah bazai taba dubanka da rahama ba harsai ta daina wannan fushin da take yi da kai. Tun farko sai da na gaya maka ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba amma baka ji ba yanzu wa gari ya waya kaine. Don haka tun wuri kaje ka nemi yafiyarsu." "Wallahi Abdallah nayi dana sanin ƙin bin shawarwarin da kake bani tun farko gashi na saka kaina a halaka, gaskiya tsohuwar nan ta faɗa da tace sai nayi nadama kuma sai naga sakayyar abinda nayi, wallahi tun ranar dana furta kalmar saki ga Zarah Allah ya ɗaura min ƙaunarta tun ina ƙoƙarin kauda hakan a zuciyata har na fahimci cewa na kamo da sonta sosai. Bansan ya zanyi ba Abdallah ka kaini gurin iyayena na nemi gafarar su." ya ƙarashe maganar yana rushewa da kuka. Sosai tausayinshi ya kama Abdallah don ya hango alamun nadama sosai a tattare da shi don haka ya kunna motar suka cigaba da tafiya, mintuna kaɗan suka iso gidan mai gadi ya buɗe musu gate suka kunna kai. Batare da ɓata lokaci ba suka fito don nufar babban falon gidan, tun kafin su ƙarasa suke jiyo muryar Baaba da alamu tana cikin nishaɗi don har dariya take ƙyakyatawa. Da sallama suka shiga turus M.J ya ja ya tsaya saboda abinda yaji kuma ya gani...✍🏻 Uhmm lallai tsugunne bata ƙare ba Muhammad Jawwad angon Hajara.😅😅😅 *BY* *JASMINE*🌸🌸 *ASP ZARAH*👩‍✈️ *BOOK 2* *Page 11* ... Baaba ya gani kwance akan doguwar kujera sai Laptop kunne akan center table, cikin laptop din kuwa hoton mutane biyu ne wanda ya tabbatar musu video call take yi da wasu, sai dai abinda ya sanya M.J shiga ruɗu shine batun da yaji Baaba tayi na cewa "Idan kaga ba zaka iya hakura da rashin ganinta ba ka biyo ta kawai kuzo tare idan kun gama hoton sai ku koma, ita ma nasan saboda kai ne take faɗin ba zata zo ba." "Toh Baaba ai yanzu tare zamu taho." Safwan kenan dake zaune a kujera kusa da Sadiq suna video call da Baaba. Zarah ce ta ɓullo riƙe da kofi a hannunta wanda ke cike da fresh milk ta zo saitin computer din tana miƙawa Safwan tana faɗin "Sweetheart ga shi kasha ka rabu da tsohuwar nan ba zata barka ka huta ba idan ta fara surutu." ta ƙarasa tana fuskantar Laptop din har da muguɗawa Baaba baki. Tari mai ƙarfi ne ya sarƙafe M.J dake tsaye ƙiƙam kamar an dasa sa, sai a lokacin Baaba dake kishingiɗe ta miƙe tana faɗin

Table of Contents

Chapters

24 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24