Chapter 15
Chapter 15
"Muje na sauke ka a yadda kake din nan bai kamata kayi tuƙi ba." "Muje muje Abdallah." Fita suka yi M.J a gaba tamkar zai tashi sama, a haka suka shiga motar Abdallah ya tada suka ɗauki hanyar zuwa gidan M.J din, Abdallah ne ya kalleshi ya ce "M.J ya akayi haka ta faru har yake ƙoƙarin maka ka a kotu.?" "Bansani ba Abdallah, innalillahi wa inna ilaihi raji'un, a gidana ace har matata na ɗauke da cikin wani amma bansani ba. Wallahi sai yanzu na tuna sam bai kamata ace cikina bane don yanzu ne cikin ya shiga wata uku kuma rabona da ita na jima sai lokacin da aka ce tana da cikin nan sam zumuɗi bai barni nayi lissafi ba." M.J ya fada idonshi na zubar da kwalla. "Ishara ce Allah ya nuna maka Jawwad shiyasa ake so mutum ya dinga kyautata zato akan ɗan uwansa." "Me kake nufi ne.?" "Abubuwan da kake zargin Zarah da su ne Allah ya tabbatar maka akan matarka." "Ba zarginta nake ba tabbatarwa nayi." Murmushi Abdallah ya yi wanda iyakarsa baki sannan ya ce "Rana na tafe, sai dai kamar yadda nayi alƙawari duk randa ka gane gaskiya kada ka neme ni don taimaka maka. Yanzu ya za'ayi da batun Hajara.?" "Abdallah zanje na tuhumeta sai ta faɗa gaskiya matuƙar da aurena ta ke bin wasu mazan wallahi sai na rabu da ita bayan na wulaƙanta ta, har ni za'a turowa takardar sammaci zuwa kotu akan bana kula da cikin da wani ƙato yayi har ana ikirarin idan wani abu ya same shi sai anyi shari'a da ni." "Uhmm" kawai Abdallah ya ce daidai lokacin da yayi horn a gaban gidan M.J mai gadi ya buɗe masa ya shiga da motar, ko parking bai gama tsaidawa ba M.J ya fita a sukwane yana faɗin "Jirani ina zuwa." Rai ɓace ya shiga falon ganin bata nan ne yasa ya nufi hanyar ɗakinta, a fusace ya banka ƙofar ɗakin. "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" ya shiga maimaitawa, tashin hankali da ba'a saka masa rana, Hajara ce da wata babbar mata a kwance kan gado haihuwar uwarsu suna aikata masha'a. Sulalewa yayi a ƙasa ya rasa ma abinda zaiyi, sai lokacin suka farga dashi da hanzari suka miƙe matar ta rarumi kayanta zata gudu aikowa ya miƙe ya rufe ƙofar ɗakin sannan ya koma ya zauna, sun ɗau mintuna a haka lokacin duk sun maida suturunsu miƙewa yayi ya kwance belt ɗin da ke jikinshi ya shiga dukansu ba ji ba gani tun suna ihu da neman taimako har muryarsu ta daina fita, sai da ya tabbatar sun galabaita sannan ya tsagaita cikin fushi ya ce ''Kinci amanata Hajara wallahi yau bazan barki ba sai kin gayamin abinda na miki har kika nemi ƙuntata min haka, dama badan Allah kika aureni ba. Bayan zina har ƴan uwanki mata kike bi, ke kuma ki tashi ki ficemin daga gida tun kafin na halaka ki." Da mugun sauri ta miƙe ta bude ƙofar ta fita, karo suka yi da Abdallah wanda tun sanda suka fara ihu ya jiyo su shine ya shigo dan ganin abinda ke faruwa, sai yanzu da M.J ya yi magana ya fahimci dalilin dukan na su. Kaɗa kai ya yi cike da takaici ya shiga ɗakin don fito da M.J kar ya yiwa Hajara wani illah. Da ke Hajara matsoraciya ce gashi kuma ta ji jiki a hannun M.J tuni ta fara sakin zancen da batasan tana furtawa ba, tiryan-tiryan ta labarta mishi dalilin da ya sa ta aureshi har zuwa ranar da aka zo har gida aka duki Zarah, ashe da ita aka haɗa baki ta buɗe musu ƙofar falon dan ta kasance automatic ne ba da key ake buɗewa ba. Cikin kuka ta cigaba da cewa "Ni bansan me ta yi musu ba, kawai sun same mu ne suka faɗa mana cewa ta yaudari wani da ke musu aiki har tayi sanadin da aka kamashi a garin bauchi shiyasa suke son ɗaukar fansa. Sai daga baya na fahimce cewa Diamond suke son karɓa a wajenta shiyaaa aka haɗa baki da ni don idan ta bayar nima a bani wani kaso a ciki." Rigiji gabji! A yau Jawwad ji yayi ya fi buƙatar mutuwarsa saboda yadda yake jin zuciyarsa na suya tana barazanar fitowa a ƙirjinsa, tabbas bai cacanci yayi farin ciki ba a rayuwarsa a yadda ya ɗau tsawon lokaci yana ƙuntatawa marainiya. Sai yanzu abubuwa suka fara dawo mishi dalla-dalla, a lokacin daya dawo daga ƙasar waje gabaɗaya sanda zai fara aiki a _M.J JEWELS_. ya tambayi Daddy diamond ɗin da ya siya a hannun turawa sai dai bai bashi cikakkiyar amsa ba sai cewa da yayi "Son waɗannan Diamonds ɗin suna hannun wacce duk rintsi duk wuya nasan bazata taɓa bari su salwanta ba saboda tsananin ƙaunata da take yi da kuma riƙon amana da gaskiya da ta ginu akai." A lokacin da Daddy ya faɗa mai haka yayi tunanin Momi aka baiwa ajiya ashe Zarah ce, sam a lokacin bai kawo ta cikin tunaninsa ba sai yanzu da Hajara ke mai bayanin nan. Wani abu da ya kuma zuwa tunaninsa shine batun Hajara da ta ce Zarah ta yaudari wani an kamashi a hotel a jihar Bauchi, kardai abinda ya fara tunani ya zama gaskiya. Cikin zare ido ya kalle Hajara dake ɗar-ɗar ya ce "Kince ta kama wani a Bauchi wane ne wannan." "Bansan shi ba nidai kawai sunce min wai ta yaudareshi akan zata bishi hotel su kwana tare ashe shi baisan cewa ƴar sanda bace bayan sunje ne ta ga hodar iblis dama suna zarginshi shine ta kira jami'an da suke tare aka tafi dashi." "Ya Hayyu Ya Qayyum" abinda M.J ya shiga maimaitawa kenan don ya riga da ya tabbatar da abinda yake tunani, sun jima cikin wannan yanayi Abdallah na daga tsaye a ƙofar ɗakin yana Hamdalar yadda zargin Zarah dake zuciyar M.J ya fara wankuwa a hankali. "Ki tafi na sake ki saki uku Hajara, dama cikin jikinki ba nawa bane dan haka ki tattara ki ficemin daga gida, kuma ina tabbatar miki iyayen wanda kika cuta zasu tsayawa ƴarsu har sai an hukuntaki akan abinda kika aikata." Kuka ta fashe dashi, zata fara roƙonshi ya dakatar da ita ta hanyar faɗin "Kada ki kuskura don wallahi idan kika ƙara koda minti biyar ne a cikin gidan nan sai dai a fice da gawarki." Ba shiri ta miƙe mayafi kawai ta iya ɗauka ta fice daga gidan. Hannun M.J Abdallah ya kamo suka dawo falo inda ya bashi ruwa mai sanyi yasha sannan ya fara maimaita mishi kalmar innalillahi wa innailaihi raji'un. Kusan mintuna talatin sannan ya miƙe yace Abdallah ya kaisu gidan Daddy, kallo ɗaya zaka mishi ka tabbatar yana cikin matsananciyar damuwa saboda yadda jijiyoyin kansa suka tasa fuskarsa tayi jajir ga idanunshi har sun kumbura. Babu musu Abdallah ya mike suka fita yaja mota suka bar gidan, dake tsakaninsu akwai ƴar tazara yasa tun suna tafiya shiru har M.J ya nisa ya ce "Abdallah kaji ashe ganin da muka yiwa yarinyar nan a hotel aiki ne ya kaita kamar yadda ka daɗe kana faɗa." "Na daɗe da sanin haka ai." Abdallah ya fada kanshi akan hanya batare da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24