Chapter 18
Chapter 18
hankali a tashe. Sosai Daddy ya ma Abdallah faɗa jin abinda likita ya faɗamai na cewa ya daɗe da cutar a jiki kuma suna zuwa karɓar magani. Ko da ya nemi jin ba'asin ciwon daga gurin Abdallah kai tsaye ya shaida mishi cewa akan Zarah ne, duk da likita yace a nemowa M.J abinda yake so amma sam Daddy yace baisan wannan zance ba indai akan Zarah yake wannan ciwon sai dai ya ce Allah ya jiƙansa da Rahama dan kuwa ba samunta zai yi. Nan likita ya bada shawarar sai anfita dashi ƙasar waje anyi mai aiki don kuwa a yanzu zuciyarsa na gab da bugawa, abu na kuɗi nan Daddy ya fara shirye-shiryen fitar da M.J zuwa ƙasar India don ayi masa aikin zuciya. Hankalin Momi da Baaba ya tashi sosai jin abinda ya samu Jawwad din nan Daddy yayi ta tausarsu daƙyar ya samu suka ɗan kwantar da hankali. ***************************** Duk yadda Zarah taso dawowa Nigeria hutu abun ya faskara saboda jarrabawar ƙarshe da zatayi don haka dole ta zauna ta fuskanci karatunta dan fitowa da sakamako mai kyau, watanni uku kaɗai suka rage mata ta gama wannan course ɗin mai mahimmanci dan haka tana buƙatar ta ƙara ƙaimi. A gefe guda kuma soyayyarsu da Safwan na ƙara ƙarfi sosai ta yadda har mutane na mamakin irin son da suke yiwa juna dan basa iya ɓoyewa ko a gaban wa suke. Maganar aurensu tayi nisa dan har ankai sadaki kamar yadda Daddy ya faɗa sannan a tsaida ranar aurensu watanni huɗu masu zuwa, kenan wata ɗaya bayan Zarah ta kammala karatun da take yi a yanzu. Ammi kuwa tunda aka saka ranar auren ta ɗauko mai gyara guda tun daga Maidugurin Nigeria ta kaita har ƙasar Malasia don gyara mata ɗiyar ta ta. Ai kuwa kwalliya ta biya kuɗin sabulu dan a cikin satin kafin Ammi ta wuce Egypt ita kanta ta yaba da irin canji da ta fara gani tattare da Zarah don haka gargaɗi matar akan kada ta bari Zarah da Safwan su dinga yawan haɗuwa gudun aikin shaiɗan. Da haka ta musu sallama ta wuce Egypt. Gyara sosai Matar mai suna Hajiya Jamila keyiwa Zarah lokaci ƙanƙani ta koma tamkar wata baturiya ko balarabiya saboda tsananin kyau da sheƙi da take fitarwa. Duk wani shiri na fitar da M.J ƙasar waje an gama shi, inda abokinshi na kwarai Abdallah yace dashi za'ayi tafiyar dan ya dinga kula da shi. Sati na zagayowa suka ɗaga zuwa ƙasar India, sai dai kafin tafiyarsu Daddy ya kira Sadiq ya shaida mishi halin da ake ciki, sosai Sadiq ya tausaya mishi sannan yayi mai fatan samun sauƙi sai dai bai faɗawa Zarah ba, ko meye dalili oho. Dake sun riga sun gama komai ta internet yasa har airport motar asibitin ta zo ta ɗaukesu, babu ɓata lokaci kuma aka fara baiwa M.J kulawar likitoci, irin asibitocin nan ne da ba'a buƙatar masu jinya dan haka su Daddy na gama duk cukucukun asibitin suka nemi masauki dan hutawa. Kullum sai dai su shirya su je da safe su dubashi su dawo sannan da yamma su ƙara komawa. Satinsu ɗaya a ƙasar jikin M.J ya fara samowa dan har yana iya bude idon sannan yana motsi da jikinsa ba kamar a Nigeria ba da tunda ya suma bai ƙara motsawa ba saboda rashin isassun kayan aiki a ƙasarmu. Kwanansu goma aka yiwa M.J tiyatar kuma cikin sa'a akayi lafiya ba tare da ansamu wata matsala ba sai dai fatan a kiyaye gaba. Sai da ya kwana tara cur! Kafin aka basu damar sake ganinsa kuma Alhamdu Lillahi yaji sauƙi sosai sai dai rama da ya yi. A ranar har video call sukayi da su Momi wanda tunda suka bar ƙasar kullum sai sun kira fiye da goma, har Ammi ma takan kira wajen sau biyar a kowacce rana don jin yanayin jikin Jawwad ɗin. Wata ɗaya Daddy yayi a India ya tattaro ya dawo gida ya bar Abdallah don kulawa da M.J saboda shirye-shiryen bikin Zarah da za'ayi nan da watanni biyu da satikai ( Su Daddy manya kana namiji mai ya haɗaka da wani shirye-shiryen aure, kodayake ƴar so za'a aurar). Kafin tahowarshi sai da ya zaunar da Jawwad ya mishi faɗa sosai tare da nasihohi sannan yace ya cigaba da neman zaɓin alkhairi a gurin Allah ya rabu da batun Zarah tunda dai ita Allah ya ƙaddara ba zasu sake zama da juna ba. Kuma da alama nasihohi da tunatarwan da Daddy ya mishi sun shige shi don yanzu baya yawan tunani da sanya damuwa a rai sai dai sonta na nan danƙare a cikin zuciyarsa babu alamun zai ragu ko ya sassauta mishi. Da haka suka yi sallama ya taho gida. Sati uku tsakani aka sallami M.J nan suka tattaro suka dawo Nigeria da tsauraran ƙa'idoji da likitoci suka gindayawa M.J. Alhamdulillahi jikinshi yayi sauƙi sosai a fili amma cikin ransa kam baiji sauƙi ba, wani lokacin yakan kulle kansa a ɗaki yayi ta kuka da nadamar abubuwan daya aikata ma Zarah gashi yanzu Allah ya bi mata haƙƙinta cikin lumana sai dai bai bari an fahimci halin da yake ciki ba duk da haka sai da Momi ta fahimta kuma ta tausayawa ɗan nata sosai, shiyasa duk abinda mutum zaiyi kada yasa son zuciya a ciki domin shaiɗan zai iya kaishi ya baro shi. *******Duk da a gajiye take sosai amma hakan baisa can ƙasan ranta takejin daɗi sosai ba, saboda a yau ne ta kammala jarrabawarta na course din da aka turota yi dan haka ne take jinta tamkar ta sauke wani icce mai nauyi akanta. A matuƙar gajiye ta isa gidan nasu, falon shiru kamar ba kowa a gidan sai dai ta jiyo motsi a kitchen wanda ke tabbatar mata Mama Jamila ce dake sunan da take kiranta dashi kenan. Jakar hannunta ta wurga kan kujera sannan ta zauna ta tsiyayi ruwan da ta gani a center table ta kafa kai tana sha, ƙarar da wayarta keyi ne yasa ta ajiye kofin ta ɗaga kiran cikin mamakin wanda ke kiran. A zabure ta mike jin abinda aka faɗa cikin wayar....✍🏻 *BY* *JASMINE🌸🌸* *ASP ZARAH* *BOOK 2* _About to end_🥰 Wani irin tsalle ta daka tare da ihu sannan ta tsagaita ta ce "Wayyo Allah na zama uwa Sa-Jid me muka samu ne." Daga ɗaya ɓangaren Saleem yayi dariya kana ya ce "An samu baby girl" "Masha Allah, a gaida Baby da mamanta. Allah ya raya mana ita bisa tafarkin addini. Zan taho zuwa jibi insha Allah." "Ahh har kin gama jarabawar ne." "Wallahi na gama ɗazu, idan ta tashi kace zan kirata." "Tom sai anjima." Wani daɗi take ji a ranta tana yiwa Allah godiya daya sauki Jiddah lafiya, inda tayi farinciki ma ta gama jarabawarta dan haka tafiya Nigeria bazai mata wuya ba. Lambar Sadiq ta kira ta shaida mishi aikuwa shima yayi murna sosai dan cewa yayi kafin ya dawo gida zaije ya fara nema musu visa zuwa gida. Sanda Safwan yaji labarin tafiyarta kuma cewa yayi sam baisan zancen ba dole shima ya bisu su koma tare. Kwanaki biyu a tsakani suna ta shirye-shirye zuwa Nigeria, duk abinda Zarah ta fita ta gani indai na yara ne sai ta siyawa Baby
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24