Chapter 21
Chapter 21
shirune yasa Jiddah ta kira likita yana zuwa kuwa ya mata allurar bacci nan bacci ya ɗauke ta sannan ya cigaba da dubata. Sai da Zarah ta yi wata guda a asibiti kafin ta fara dawowa daidai tare da sakawa ranta cewa lallai Safwan ya tafi ya barta saidai ya barta da rauni a zuciyarta da bazata taɓa warkewa ba, ta kuma shiru shiru sam bata son hayaniya kullum cikin jan carbi da karatun alqur'ani take yi, a haka likita ya bata sallama bayan nasihohi da aka mata. A ranar da Safwan ya rasu harda M.J da Abdallah suka shirya zuwa jana'izarsa. Kuma a gabansa aka ɗaura aurensa da Zarah, a ranar ji ya yi tamkar mafarkan da ya saba yi ne yake yi, babu kalar addu'ar alkhairi da bai yima mai martaba ba godiya kuwa har saida ya dakatar da shi, kwana yayi yana sallar godiya ga Allah da kyautar da yayi masa a lokacin da ya cire tsammanin samu. A haka suka gama kwanaki uku suka baro Yola zuciyar M.J cike da farin ciki sai dai a ɓangare guda yana taraddin yadda zai fuskanci Zarah ko da wani idon zata kalleshi idan taji labarin ya zama mijinta a karo na biyu. Kullum sai yaje asibitin dan dubata sai dai yafi zuwa lokacin da yasan tana bacci, tana bashi tausayi sosai saidai a ɓangare guda yana kishi idan ya tuna saboda wani take yin wannan jinyar. Kwanaki biyu da sallamo Zarah Mai martaba da tawagarsa suka zo, da kanshi ya nemi ganawar sirri da Zarah, shima dai nasihar ya mata sosai kafin daga baya ya shaida mata batun aurenta da Jawwad, aikuwa nan hankalinta ya ƙara tashi ta fashe da kuka, roƙonta mai martaba ya shiga yi dakyar ya samu ta sassauta bayan ya shaida mata yau yake so dukkansu a wuce dasu ɗakin mazajensu dan dama Rahama tare da masu ɗaukarta suka zo. Nisawa yayi ganin yadda take risgar kuka yace "Fadimatu bawai shawararki nake nema ba ina baki umarni ne a matsayina na uba gareki indai kin bani wannan matsayin. Kiyi hakuri da yadda ƙaddara tazo miki mun sani duka cewa kina halin da yakamata a tausaya miki amma hakan da aka miki shine gata kuma zai rage miki raɗaɗin abinda kike ji. Ki sani cewa a yanzu Safwan babu wani abu da yake bukata a gurinki face addu'a sannan bazai taɓa yin farin ciki ba matuƙar kika bijirewa iyayenki saboda kawai son da kike mishi sannan bazai ji dadi ba idan aka tada ki ranar alkiyama a matsayin wacce bata bin umarnin iyayenta, a yanzu akwai auren wani a kanki tunanin Safwan da irin soyayyar da kukayi ba shine mafita a gareki ba domin dai hausawa sunje matar mutum kabarinsa, dama can aurenku da Safwan babu shi cikin lauhul mahfuz, ta iya yiwuwa akwai tanadin da Allah ya muku a lahira shiyasa bai saka kun zama ma'aurata a duniya ba. Shi kanshi Safwan ba zaiji dadin kwanciyarsa a cikin kabarinsa ba matuƙar kin take dokar Allah saboda kawai son da kike mishi. Matukar kin bani wannan matsayi na mahaifi dan Allah Zarah ki amince da wannan auren sannan ki rikeshi hannu bibbiyu dan samun rabauta duniya da lahira, shin zaki iya yimin wannan alfarmar." Cikin sheshsheƙar kuka ta gyada kai sannan tace "Na aminci Baba zanyi amfani da duk abubuwan da ka fadamin sannan zanyi ƙoƙari na cigaba da ɗaukan hakan a matsayin ƙaddarata." Kalamai masu taushi ya cigaba da gayamata har saida yaga hankalinta ya kwanta sannan ya kira sauran mutanen gidan yayi musu maganganu masu ratsa jiki musamman M.J dan kusan gabaɗaya fadan akanshi ne, da haka ya baiwa sauran iyayensu damar magana shikam Daddy ya kasa furta komai dan gani yake kamar a yanzu bashi da wata kima a idon Zarah dan kila zatayi tunanin saboda yana son ɗanshi ne kawai ya saka aka ɗaura auren. Duk shiru sukayi kafin Momi ta bude baki ta ce ''Muhammad Jawwad a matsayina na mahaifiyarka matuƙar ka ƙuntatawa Zarah a gidan aurenka ban yafe maka ba duniya da lahira ko bayan bana raye." daga haka ta mike ta fice a falon. Kai kawai mai martaba ya kada sannan yasa aka kira mishi matan da suka zo tare ya shaida musu su shirya Zarah su fara kaita ɗakinta kafin su zo su wuce da Rahama zuwa Yola. Haka kuwa akayi da taimakon Ammi da Jiddah suka shiryata fes ta fito amarya sai dai kallo daya zaka wa fuskarta ta baka tausayi saboda yadda ta kumbura lokaci guda tayi jazir saboda kukan da take yi. Sam Baaba da Momi sunki yarda suyi Sallamar ƙarshe da Zarah shikuwa Sadiq hannunta kawai ya riko ya kaita har ciki sabuwar motar da Daddy ya siya musu ta fitar biki ita da Rahama ya zaunar da ita a ciki sannan ya rike hannunta gam yace "Ki sani a kowani lokaci zan kasance tare da ke sannan bazan taba bari a cuceki ba a wannan karon matukar akayi yunkurin hakan sai inda karfina ya kare akanki, banaso ki saka damuwa a ranki ki cire komai ki saka a ranki cewa ibadah zakije yi sannan ibada dole sai da sadaukarwa. Zan kasance a tare da ke a kowani lokaci." Hannu ya saka ya share mata hawayen fuskarta sannan ya sake hannunta ya rufe motar ya ja hannun Rahama dake fama risgar kuka suka shige cikin gidan. Basu jima sosai a gidan Zarah ba suka yi niyyar komawa saboda tafiyar dake gabansu, hakuri sosai Ammi ta kara bata kafin su bar gidan, itama dai Jiddah bata zauna ba duk da taso hakan amma Ammi ta hana. Haka suka tafi suka barta ita ɗaya tana aikin kuka. Rahama ma haka aka tafi da ita cikin kuka da kewar rabuwa da gida musamman Ammi dan daƙyar aka rabasu saboda shaƙuwar dake tsakaninsu. A haka aka wuce da ita zuwa airport jirginsu ya daga zuwa garin Yola. Sai fatan zaman lafiya mai ɗorewa. *************************** Zaman dai na Zarah da Jawwad ba'a magana dan kuwa zamane na doya da manja sai dai yana iya bakin ƙoƙarinshi dan kyautata mata dan da gaske yake son gyara laifukanshi na baya. Kullum safiya shi ke gyara ko'ina na cikin gidan daga falo har sauran ɗakuna hatta ɗakin da Zarah take kwana shike tsabtacewa duk safiya idan yazo zai gayamata zai gyara ɗaki sai ta fita zuwa falo ta bashi guri idan ya gama ta kuma, bata kuma fitowa sai idan ya gama breakfast yazo ya gayamata ta fita duk da bawani abincin take ci ba kawai tsakura kawai ta tashi, idan ta gama kuma yazo ya tattare kayan da taci abincin ya wanke kafin ya shirya ya tafi office dan ma dai shine shugaba shiyasa bashi da wata matsala a fannin ƙorafin latti, da rana ma haka duk abinda yake yi zai bari ya siya abinci a resturant ya kai mata. A haka rayuwar tasu take kasancewa sai dai babu wata alaqa tsakaninsu dan kafin Zarah ta mishi magana ma yana jimawa sosai sai dai idan abu ya kasance mai mahimmanci ne. A haka aka shirya taron ƙarawa Zarah matsayi a wajen aikinta inda aka bata muƙamin mataimakiyar Commissioner na ƴan sanda a jahar Gombe gabaɗaya, gagarumin taro aka shirya Daddy da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24