Skip to content

Chapter 20

Chapter 20

Asp Zarah Book Two Complete Hausa Novel 1,206 words 0 views Progress saved
Download Book

ta samu M.J haka gaskiya yana cikin wani hali da ya kamata a tausaya mishi. Har cikin zuciyarta ita kam ta yafe mishi dama can bata rikeshi da komai ba. A wannan dare kusan kwana tayi idonta biyu da tunanin M.J a ranta. Washegari kuwa da manyan baƙi suka tashi don Ammi ce da Rahama suka diro ƙasar tun safiya, murna kuwa a gurin Zarah kamar ta shiɗe. A ranar haka suka wuni cikin walwala da yamma kuma suka wuce gidan Jiddah dan acan zasu kwana saboda aikace-aikacen suna da za'ayi washegari. Mutanen sunyi mamakin karar da Jiddah tawa Zarah kodayake ba mamaki idan aka duba irin shaƙuwar dake tsakaninsu. Yarinya dai taci suna Fatimah Zarah za'a dinga kiranta da Amrish. Suna ya ƙayatar sosai uwa da ƴa sun samu kyaututtuka na ban mamaki, a haka aka watse taron kowa ya tafi da souvenirs da aka yi. Saleem bai yarda a tafi da Jidda wankan gida ba dan haka ne aka nemi wata daga cikin danginsu ta zauna da ita. Kwanaki biyu tsakani Safwan ya shirya tafiya Yola sai dai zai jira Yayanshi da yazo Gombe aiki ya gama su tafi tare. Tun ranar da yazo basu haɗu da Safwan ba sai ranar tafiyarsu gida ya taho gidansu Zarah dan gaisawa da surukan ƙaninshi. Rabon kwaɗo ko a ruwa zafi yake baya wucewa, Tunda yayi arba da Rahama zuciyarshi a karo na farko ta gamsu da ita yaji yana sha'awar ƙulla taraiya ta har abada da ita. Bai bayyana hakan ba sai a hanyarsu yake shaidawa Safwan aikuwa yayi murna sosai inda yace zai sanar da mai martaba a haɗa aurensu tare. Sanda iyayensu suka ji wannan batu sunyi murna matuka musamman da kullum burinsu bai wuce suka Mahmud yayi auren ba, babu wani jan lokaci dan sun yanke shawarar a haɗa auren biyu indai ya tabbata, ko da Mai martaba ya kira Daddy ya tambayeshi ko anyiwa Rahama mijin cewa yayi a'a amma zai tambayeta ko akwai wanda take so, Alhamdulillah bai sha wuya da Rahama ba ta gayamai babu wanda ta tsayar dan haka ya kira Mai martaba ya shaida masa. Kwanaki uku tsakani aka hado lefe da sadakin Rahama aka kawo inda aka tsaida biki rana ɗaya da nasu Zarah wata ɗaya da sati biyu masu zuwa. Murna kuwa ba'a magana, nan Ammj ta ƙara zagewa ta fara gyara ƴaƴan nata na musamman. Shidai M.J ya daina jinya a fili sai a zuciya, yana matuƙar galabaita sosai dan ya rame yayi haske kamar wanda ke gargarar mutuwa. ********************************* Kwanci tashi asarar mai rai, yau gashi har an shiga satin da za'a fara shagalin bikinsu Zarah, duk wasu shirye-shirye da suka kamata anyi. Kuɗi kuwa tamkar ba nemansu ake yi da zafi ba yadda ake fiddasu kamar ba'asu. Daga masarautar su Safwan kaɗai miliyon goma aka turo na gyaran amare banda manyan akwatuna da aka ciko da kayan fitar biki masu tsadar gaske. Ɓangaren su Daddy ma shirye-shirye ake yi sosai dan Daddy kwarai yake son nuna su Zarah na da gata duk da ubansu baya raye, shikanshi sai da ya musu akwati bibbiyu ya shake da kaya na fitar biki bayan kayan ɗaki da suka shirya da Momi da Ammi suka je har Italy dan siyowa, hatta cokali abin banza a ƙasar waje aka siyo musu komai nasu daga can ne. Baaba kuwa tayi faɗan harta gaji amma sunƙi dainawa. Babban Yaya kuma wani danƙareren Boutique ya gina musu wanda aka cikashi da kayan siyarwa na manyan mutane da ko a ƙasar waje sai haka, inda aka shirya taron buɗeshi ranar da za'ayi bridal shower ɗin amaren, bayan haka sai da ya saka musu makudan kudi a cikin account dinsu. Tun ranar Monday aka fara gudanar da shagulgula inda akayi Welcoming dinner ranar monday a farfajiyar gidan Daddy an kashe kuɗi sosai amare kuwa sun sha kyau tamkar a sace su a gudu, washegari ranar talata kuma akayi Fulani day mai ban sha'awa dan harta mutanen Yola sai da suka zo a jirgi bayan angama ya kwashe su ya kuma, Ranar laraba kuma akayi shagalin buɗe Boutique ɗinsu Mai suna *RAHAZAR BOUTIQUE* wanda ya samo asali daga farkon sunan kowaccensu. Washegari Alhamis ne za'a gabatar da Reception kuma a ranar Safwan da abokansu zasu taho Gombe dama shi Mahmud tun ranar Monday yake nan saboda wani taro da suka gabatar shiyasa bayan an kammala yayi zamansa kawai tare da wasu daga cikin abokanansu. Fitowar Zarah daga wanka kenan saboda bata tashi da wuri ba dan gajiya dama kuma tana fashin Sallah, turo ƙofar akayi a hankali kanta ta maida kan me shigowar Sadiq ne da Daddy suka shigo kallo ɗaya zaka musu ka gane tsantsar damuwa a tattare da su. Hijab ta ɗauka ta zura sannan ta gaida Daddy bai amsa mata ba illa zaunar da ita da yayi a gefen gado ya fara magana kamar....✍🏻 *BY* *JASMINE🌸🌸* *ASP ZARAH* *BOOK 2* Nasiha sosai Daddy ya fara mata me ratsa jiki, ƙirjinta ne ya fara dukan uku saboda yadda taji yana ambatar karɓar ƙaddara, ko wacce ƙaddarar ce ta kuma samun rayuwarta, tunaninta ya katse sanda taji Daddy na faɗin "Zarah haƙuri da juriyar da na sanki dashi a wannan karon ma shi nakeso kiyi sannan ki rungumi ƙaddarar da Allah ya ɗora miki da hannu biyu. Kiyi haƙuri Zarah yau da asuba Allah yayiwa Safwan mijin da zaki aura rasuwa sakamakon ciwon ciki da ya kulleshi a jiya da dare." Tamkar saukar aradu haka taji maganar Daddy a kunnuwanta bata kyma gaskatawa ba sai da taji ɗan uwanta na maimaita batun Daddy ɗin. Bata kuma sanin inda kanta yake ba sai buɗe ido tayi ta ganta kwance a gadon asibiti da ƙarin ruwa a hannunta, a hankali ta fara juya idanunta tana ƙarema inda take kallo da mutanen dake wajen, mutum uku ta gane a cikinsu Baaba, Jiddah sai Rahama da suka yi wujiga-wujiga alamun tashin hankali ya bayyana a garesu, ƙoƙarin mikewa ta farayi da sauri duk suka ƙaraso inda take suna mata sannu bata kula ba ta fara magana tana cewa "Dan Allah kuce mafarki nayi na zahiri bane dam Allah kada kucemin Safwan ya rasu bazan iya rayuwa batare dashi ba, wayyo Allah shin wani zunubi na aikata a rayuwata da nake ganin irin waɗannan kaddarori." Kuka mi cin rai ta fashe da shi me cin rai. Gabaɗaya tausayinta ne ya kamasu su kansu rasuwar Safwan ta jijjigasu matuƙa bare ita kuma da kowa ya zauna da su a ɗan ƙanƙalin lokacin nan zai fahimci irin ƙaunar da suke wa juna. Kwananta biyar kenan a kwance batasan wanda yake kanta ba tun ranar da aka faɗa mata batun rasuwar Safwan ɗin. Bayan su Daddy sun kawota asibiti ne suka bi jirgi zuwa garin Yola dan jana'izarsa, kwanansu biyu suka dawo kuma kafin su dawo sai da aka ɗaura auren Rahama da Mahmud sannan Zarah da Jawwad dan Mai martaba ya ce baza'a ɗaga auren ba sannan shi da kanshi ya baiwa Daddy shawarar a ɗaura aurenta da Jawwad ɗin sannan yace shi da kanshi zai zo ya taushi Zarah idan anyi sadakar bakwai sai dai an dakatar da shagulgulan da aka shirya. Kuka takeyi sosai harda shiɗewa suna bata baki ganin taƙi yin

Table of Contents

Chapters

24 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24