Chapter 2
Chapter 2
ta fice daga gidan ta wuce office ɗin. Tun daga harabar gurin take ganin kamar tasan wasu daga cikin jami'an dake shawagi a farfajiyar wajen bata kula ba ganin tayi latti ya sa kai tsaye ta nufi office ɗin commissioner kai tsaye ko kula da sunan dake manne a jikin ƙofar batayi ba ta kutsa kai ciki bakinta ɗauke da siririyar sallama. Tashin hankali _ba'a saka masa rana_, zuciyarta ce ta cunkushe _damuwa tayi adabo a fuskarta_. Jikin tsantsar baƙin ciki ta riƙe handle ɗin ta nufi ficewa a office ɗin......✍️ *BY* *JASMINE*🌸🌸 _Fans Mi😜😜😜 Meerah, Zee Bassa, Nab baby, Hussy, Mrs. Mukhtar, Miss Japanese and others da kuka hana kanku bacci jiya toh gashi nan kusha karatu😅😅 A daina hana kai bacci hilis dan nima bana hana kaina 🤦♀️._ _Su Ummu Huzaifah a sakar mini mara nayi fitsari, kada masoyiyata ta fara nata itama JJLuV😘😘_ Luv y'all. *ASP ZARAH*👩✈️ *BOOK 2* *Page 2* ...Dariya yayi mai cike da ma'anoni kafin yace. "Barka da zuwa Zarah, ya zaki koma tun baki yimin maraba da samun sauyin gurin aiki ba?." A hankali ta juyo ta kalleshi cikin tsana tace. "Abinda ya kawoni kenan na taya wanda aka naɗa murna saidai wanda na tarar bai cancanci hakan ba, hmm so kake na tayaka murna kabar garin Bauchi a matsayin commissioner ka dawo Gombe a matsayi iri ɗaya? Wani cigaba kenan?. Zuwa na ya ƙaramin aiki domin kuwa ganinka da nayi anan ya tabbatarmin da cewa akwai hannunka a kisan tsohon commissioner saboda kanaso ka dawo inda nake aiki. Allah ya baka sa'a." "Dakata ai baki karɓi saƙon naki ba." ya faɗa yana miƙewa a kan kujerar ganin tana ƙoƙarin barin offishin, tsayawa tayi harya iso inda take tsaye ya miƙa mata farar takarda yace. "Wannan takarda ce ta dakatar dake daga aiki har na tsawon lokacin da za'a gama ƙaddamar da bincike akanki, an kamaki da laifi biyu, na farko ana zargin sa hannunki a ɓatan ƴar aikin dake muku aiki a gida wacce ta ɓata watanni biyu da suka wuce an rasata, na biyu kuma akan mutuwar ɗan jaridar da kukayi ganawar sirri dashi a ranar litinin wanda shima a daren aka kashe shi." Tsaye tayi tana kallonshi har ya gama magana kafin ta sa hannu ta karɓi takardar tace "Kamar yadda muka saba a kowani lokaci mai girma commissioner.." tana gama faɗin haka ta saka hannu ta yaga takardar ta kuma cewa. "Ya fuskanceni, gaba da gaba mu gwabza dashi. Kai harka manta da sharaɗina, ba kallon shugaba nake maka ba kallon abokin gaba nake maka dan haka baka da hurumin da zaka dakatar da Zarah a aiki ko da na second ɗaya ne. Idan ya cika jarumi ya fuskanceni, na barka lafiya." daga haka ta fice a office ɗin ta barshi a tsaye sororo kamar wawan da yaga mace na wanka. Bata ko tsaya amsa gaisuwar da ake mata ba lokacin data isa gurin aikinsu, kai tsaye office ɗinta ta wuce saboda sarawa da kanta yake yi yana mata masifar ciwo, kanta ta kifa a teburin ta fashe da kukan da batasan dalilin yin shi ba. Tsagaitawa tayi da kukan batare da ta share hawayen dake zubo mata ba jin alamun za'a shigo office ɗinta batare da an nemi izini ba, tasan ɗaya daga cikin mutum biyu ne ke shigowa ko su duka biyun wato Saleem ko Jidda. Hannunsu sarƙe dana juna suka shigo bakinsu ɗauke da sallama, cike da mamaki suke kallon fuskarta da ta jiƙe da hawaye, tuni hankalin Jidda ya tashi ta nufeta gadan gadan tana tambayarta abinda ke damunta. "Babu komai fa Habibaty, kawai kaina ke min ciwo." Murmushin daya tsaya iya baki Jiddan tayi kafin da zauna shima Saleem ya zauna akan kujerun dake fuskantarta, shiru Jidda tayi ta ƙura mata ido tanason gano abinda ke damunta kafin tace. "Kinje Office ɗin commissioner da nufin taya shi murna sai akayi rashin sa'a kika tarar da Muttaka wato tsohon commissioner na jihar Bauchi a matsayin Commissioner a garin Gombe, hakan ne ya haddasa miki damuwa kike tunanin taya zaki shawo kan matsalolin dake damunki. Shin zance na haka yake ko akwai gyara.?" Bata koyi mamakin jin batun Jiddah ba saboda sabo da tayi da hakan, shikuwa Saleem ganin Zarah ta gyaɗa kai alamun hakane yasa shi mamakin a ina Jiddah ta samu wannan labarin suna tare amma shi bai sani ba. "Jeki ɗauraye fuskarki kizo muyi magana." Ta kuma faɗa. Wannan karon Zarah abin na Jiddah ya bata dariya domin dai ta fahimci Jiddah ta gane fitsari ya cika mata mara ne shiyasa tace taje ta ɗauraye fuska gudun kada Saleem ya fahimci zance. Babu musu ta miƙe ta shige banɗakin dake manne a office ɗin. Saleem kuwa maida kallonshi yayi ga Jiddah cikin zaƙuwa yace. "Sa-Jid a ina kika samu labarin abinda ya faru bayan muna tare banga wani ya kiraki ya faɗa miki ba." Shiru tayi na wani lokaci kafin tace "Nima bansan ya akeyi nake gane abinda ke ran Zarah ba, wani lokacin sai naji kamar anayi min raɗa a kunne na tuhumeta kuma na bata shawara. Abinda yake ƙara ɗauremin kai kuma shine idan mukayi amfani da shawarar sai muga ribar abin. Nima na rasa gane me hakan ke nufi." Jinjina kai Saleem yayi cike da gamsuwa, yana ƙara tabbatar da cewa ƙaunar dake tsakanin Jiddah da Zarah daga Allah ne, babu yadda za'ayi ɗayansu ta ɓoye damuwarta batare da ƴar uwar ta fahimci haka ba. A wannan yanayin Zarah ta fito ta samesu, zama tayi suka cigaba da tattauna abinda da ya shafi binciken da Saleem yake gabatarwa akan mutuwar ɗan Jaridar. "Ni fa inaga lokaci yayi daya kamata mu tunkari inda azzalumin nan yake tunda yaranshi biyu na hannu, mu tursasa sai sun faɗa mana inda yake." Inji Saleem "A'a dear lokaci baiyi ba amma saura ƙiris domin muna gab da sanin inda yake." Cewar Jiddah. "Hakane Barrister akwai sauran lokaci, baya ga haka har yanzu Raliya taƙi mana bayani akan komai daya shafe shi duk kuwa da irin azabar da ake gana mata."- Zarah "Shikenan amma ya kamata muje ki ƙara yiwa mutumin nan barazana domin shima bashi da alamar yin bayani." "Inada niyyar hakan dama tunda kunzo sai muje gaba ɗaya daganan na sake yiwa Raliya tambayoyi". "Ok muje ɗin" Daga haka suka miƙe tare da barin offishin. Babu wani da zaiyi tunanin mutane na rayuwa a inda su Zarah suka je, domin wani tsohon kwango ne da ya ji jiki ginin gaba ɗaya ya fara rugujewa. A haka suka shiga tare da kutsa kai a wani babban ɗaki, Saleem ne ya isa daidai inda wasu shukoki suke ya kauda ƙasar dake gurin gefe sai ga wani murfi kamar na rijiya ya bayyana a gurin. Key Zarah ta miƙo mishi ya saka ya buɗe babban kwaɗon dake wajen tare ɗage murfin sai ga matattakala ta bayyana. Juyowa yayi ya kallesu yace "Muje ko." Kamar ko yaushe sune ke fara shiga sai ya biyo bayansu, yauma hakan ce ta faru saida suka shige kafin shima ya bisu bayan ya dudduba baiga kowa ba. Tana ɗaure a jikin kujera sai wata mata dake gefe a zaune tana daddana waya, ganin shigowarsu Zarah ne yasata miƙewa tana musu barka da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24