Chapter 22
Chapter 22
kanshi ya kira M.J ya shaida mishi bai ko yi musu ba ya amince inda shima yasha alwashin zuwa batare da yayi tunanin komai a ranshi ba. Taron ya ƙayatar sosai inda Zarah ta samu manyan kyaututtuka hatta su Daddy sai da suka samu kyautar karramawa a matsayinsu na iyayenta. A haka aka watse taron aka watse. Sosai hankalinsu Momi ya kwanta ganin babu wata alamun damuwa a tattare da Zarah ga kuma yadda M.J yake bin umarninta kamar dai itace mijin. Sai dai shi kallo ɗaya zaka masa ka gane cewa hankalinshi ba'a kwance yake ba amma tunda ba furtawa yayi ba babu wanda yasan abinda ke damunsa. Zamansu dai bai canza zani ba dan jiya iya saboda M.J ya maida kanshi tamkar bawa ya cire duk wanj girman kai yana baiwa Zarah kulawa, a yanzu da ta fara fita aiki kullum yana idar da sallar asubahi yake fara aiyukan gidan sannan ya hada musu breakfast. Idan ta gama karyawa kuwa shi da kansa yake ɗaukar mata jaka ya kaita mata mota sannan ya bude mata idan ta shiga ya rufe ya mata addu'ar dawowa lafiya kafin nan ya kuma ciki ya shirya ya tafi nashi aikin. A haka rayuwar tasu take kasancewa har zuwa tsawon wani lokaci sai dai an samu sassauci dan yanzu Zarah tana gaidashi wani lokacin kuma da kanta take dafa musu abinci musamman idan ta fahimci baya jin dadi dan a zaman su sau biyi ciwonshi yana tashi kuma yana wahala sosai. Yau ta kasance weekend babu aiki dan haka ne tunda tayi sallar asuba ta kuma ta kwanta saboda tana bukatar hutu dan a satin tayi aiki sosai ta gaji. Baccinta take yi hankali a kwance a haka M.J y shigo dan gyara mata dakin ganin tana bacci ne yasa ya tsaya yana ƙare mata kallo tare da jinjinar girman soyayyar da yake mata, ya dade a tsaye kafin ya fita ya ja mata ƙofar a hankali ya koma kitchen da hada musu abinda zasu karya dashi. A firgice ta mike zaune jikinta na rawa lokaci guda ta haɗa gumi har tana diga sosai hankalinta ya tashi akan mafarkin da tayi...✍🏻 *BY* *JASMINE*🌸🌸 *ASP ZARAH* *BOOK 2* Take abinda ta gani cikin mafarkin ya fara dawo mata filla-filla sosai hankalinta ya tashi. Zaune take a cikin wani haɗaɗɗen garden tana zaune tana hutawa iskar gurin na kaɗa ta, a hankali ta fara hango wani haske na nufo inda take har ya iske ta, ware ido tayi sosai ganin iyayenta cikin kyakkyawar shiga sai sheƙi suke yi. Da sauri ta mike da nufi isa inda suke sai kuma ta tsaya ganin Mami ta ɗago mata hannun alamun ta dakata batason ta iso inda suke sannan tace "Fadimah ashe irin abinda kike aikatawa a gidan mijinki kenan saboda kinga kasa ta rufe mana ido, kenan duk tarbiyar da na baki akan yarda da ƙaddara baki ɗauka ba ko so kike Allah ya azabtar damu saboda kinki bin umarninshi, kinsan a rana sau nawa mala'iku ke tsine miki kuwa akan halin ko'in kula da kikewa mijinki. Ki gaggauta gyarawa dan sauke fushin Allah akanki, nima da kika ganni cikin jindaɗi ba komai bane sila face biyayyar da nayiwa nawa mijin shin bakyaso ki shiga jindadi ki kasance tare da mu a ƙoramar alfarma. Mahaifinki yana fushi dake sosai bayaso ma ya miki magana sai ranar da kika gyara halayenki. Na tafi kiyiwa mijinki biyayya Fadimah kiyiwa mijinki biyayya kiyiwa mijinki biyayya." A nan zancenta ya ƙare saboda hannunta da Abba yaja suka bar wajen, zama tayi a ƙasa tana kuka sosai har na tsawon lokaci kafin taji an dafa ta ɗagowar da zatayi tayi arba da Nusaiba itama cikin shigar alfarma, kafin ta iya furta komai Nusaiban ta ce "Yaya Zarah kowa yana fushi dake harsu Kaka dake sonki duk sunyi fushi saboda abinda kike aikawata, Kaka ta ce bataso taga kullum mala'iku suna tsine miki dan haka ne ma tace babu ruwanta dake, har su Adeel duk sun daina sonki, nima kawai nazo ne na gayamiki idan baki gyara halayyarki ba bazan kuma zuwa inda kike ba." Kafin ta ankare ta neme ta ta rasa dan haka ne ta miƙe ta fara tafiya dan barin wajen, tana cikin tafiyane ta hango wani a zaune kan wata kujera ta alfarma sai sheƙi take yi, tsayawa tayi daga nesa tana ƙare mai kallo, juyuwar da zaiyi taga ashe Safwan dinta ne da mugun gudu ta nufi inda dan isa gare shi, Dakata! Shine abinda ya faɗa da ƙarfi sannan ya cigaba da cewa "Baki kasance cikin masu yarda da ƙaddarar da Allah ya jarabesu da shi ba dan haka karki zo inda nake." bat ta nemi shi ta rasa, kuka riris take yi tana kiran sunayen su amma babu wanda yazo. Wasu hawaye masu zafi ne suka sauko daga idanunta, duk da ance mafarki ba gaskiya bane itakam wannan gaskiya ta ɗauke shi dan a fahimtarta iyayenta dake kwance cikin kabari basa jindadin abinda take aikatawa. Amma ya zatayi takasa cire Safwan din a ranta, bawai bata yafewa M.J abinda ya aikata mata bane amma tana jin ciwo ace ta rayu da shi a maimakon Safwan din da take buri. Sai dai wannan mafarkin lokaci guda ya sauya tunaninta ta saka a ranta cewa zata yi ƙoƙarin ganin ta sauke haƙƙin aurenshi da Allah ya ɗaura mata. Istigfari ta fara tana neman yafiyar Allah dan tasan ba ƙaramin zunubi ta kwasa ba a zamanta da M.J din, shi Allah babu ruwansa da tanaso ko bataso haƙƙin da ya rataya a wuyanta kawai zata sauke idan kuma takasa zunubi ne a kanta, tabbas tasan hukuncin macen da bata yiwa mijinta biyayyah ba a gurin Allah kaɗai hatta mala'iku da sauran halittu kullum cikin tsine mata suke yi. Kuka ta ƙara fashewa da shi har da sheshsheƙa zuciyarta na mata zafi sosai, M.J dake tsaye gaban Dinning yana jera abinci ya jiyo sautinta ai da gudu ya nufo ɗakin. Tana nan a zaune tana kuka, da hanzari ya nufi inda take yana tambayarta meya faru sai dai bata bashi amsa ba. Zama ya yi yana rarrashinta tare da bata haƙuri dan a zatonshi shine ya mata laifin. Sun dade a haka kafin ta sassauta kukan tana sauke ajiyar zuciya, toilet ya shiga ya hada mata ruwan dumi sannan yace taje tayi wanka, mikewar da zatayi jiri ya ɗebeta luuu! Ta kuma zata fadi ya tare ta. A hankali ya ɗauke ta ya shigar da ita bayin, da kanshi ya mata wankan ganin lokaci guda zazzaɓi me zafi ya rufeta sai rawar ɗari take yi. Riga kawai ya zura mata bayan ya fito da ita sannan yaje ya hado mata tea me kauri ya haɗo da Paracetamol, dakyar tasha Tea din kaɗan ya bata maganin sannan ta kuma ta kwanta. Ganin har rana jikin nata yaki sauki ne yasa ya kira Abdallah ya mata allura sannan ya ɗaura mata drip, falo suka koma suna tattauna matsalar M.J din Abdallah na ƙara bashi shawarwari akan wannan ce kaɗai damar da zaiyi amfani da ita wajen sasanta tsakaninsu da Zarah, sun dade kafin ya maj sallama ya tafi. A takaice dai sai da Zarah tayi sati tana jinya har su Momi sai
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24