Chapter 11
Chapter 11
isa cikin garin wanda yake da kyawun tsari, duk da mun baro arewacin Najeriya a bushe amma wannan yankin ko ina da damshi alamun dai basa dadewa ba ta re da ruwan sama ba. Wani ƙaramin masauki muka kama don mu kwana a ciki kafin washegari mu ƙaddamar da abinda ya kawo mu. Wannan dare kwana nayi a gaban maliccina ina kai mai kukana ya taimaki ne akan abinda na sa gaba. Wallahi ban taɓa sanin cewa addu'a na da wannan ƙarfin ba sai a washegarin wannan dare, ban taba tunanin abubuwa zasu zo mana da sauƙi ba sai a lokacin na tabbatar cewa babu kamar hawayen wanda aka zalunta a wajen Allah. Washe gari kamar yadda aka faɗa mana cewa Alpha na fita zagayawa a gari cikin ɓadda kama haka muma muka shirya ɓadda kama tamkar wani shirin film. Duk da cewa cikin Jiddah bai wani girma ba amma a haka muka yi amfani da ita. Kasancewarsa mutum mai kaifin basira yasa ba mu yi tunanin yin ƙaryar yin dressing da bandage ba gudun karya gane ƙarya muke yi. Dole ta sa aka yi wa Jiddah rauni a jikinta, duk yadda ta so daurewa sai da ta kasa na gane cewa tana matuƙar jin zafi a jikinta. Kayan masu aikin Momi da muka karɓo muka saka sannan wata daga cikin jami'an nan ta shafa mana wani abu a fuska da jiki wanda idan ba mutum ya sammu sosai ba bazai gane mu ba. Tunda wuri muka yi wa hanyar da Alpha zai bi tsinkaye, cikin tsananin shiri da taka tsantsan. A tsakiyar hanya muka zauna Jidda ta kishingiɗa ta yi matashi da cinyata, kasancewar a yanki kudu kowa harkar gabanshi yake yi ya sa babu wanda ya kula da lamarin mu kowa ya zo wuce wa yake yi batare da ya tambayi dalilin da yasa muke zaune a gurin cikin wani yanayin da babu kyan gani ba. Mu na zaune a wajen har kusan mintuna talatin ni da Jiddah, yayin da su Saleem ke can nesa a ƙasan wata bishiya suna zaune. Tun daga nesa na hango tahowarsa, kallo ɗaya zaka masa ka fahimci cewa yana taƙama da izza saboda yanayin yadda yake tafiya tamkar mai tausayin ƙasa, duk da shiri ne amma ni da Jiddah mun gaji sosai kallo ɗaya zaka mana kasan mun galabaita. Magana nayi a hankali na sanar da Jidda tahowarsa, ai kuwa tuni ta fara juyi kamar wacce ke naƙuda alhali cikin nata wata 3 ne kacal, ƙamshin turarensa kaɗai ya isa sanar da cewa mai kuɗi ne na gaske, domin indai hancina ya jiyo min ƙamshin nan daidai Abbana yana amfani da kalan turaren nan sanda yake da rai, saboda akwai watarana da na dage sai ya bani kyautarsa shine Mami ke gayamin kuɗin turare yakai dubu ɗari uku. Cikin takun ƙasaita yazo ya wuce ta gefen mu ba ta re da ya kalli ko gefen da muke ba, take naji hawayen rashin nasara sun sauko daga idanuna, har ya ɗan yi nisa naga ya tsaya sannan ya juyo ya nufo inda muke, farin ciki ne ya kamani dakyar na saisaita kaina gudun matsala. "Sannunku bayin Allah" Sautin muryarsa naji ta daki kunnena, zan iya rantsewa tun da nake a duniya ban taɓa jin wata murya mai zaƙi irin tasa ba, mintsilin da Jiddah ta yi min a gefen cinya ne ya dawo da ni da ga duniyar tunanin da na tafi. Cikin sanyi na amsa mai da "Yauwa sannu" na kauda kaina gefe ina matsar kwalla. "Me ya sa kuke zaune anan gurin da babu tsabta haka." "Ƴar uwa ta ce ba lafiya cikinta yana ciwo, kuma akwai ƙaramin ciki a jikinta shiyasa na zauna anan mu ɗan huta ta ce ba zata iya tafiya ba." Na faɗa cikin rauni. "Subhanallah! Taimako ya kamata ke nema a kaita asibiti ai, ciwon cikin masu juna biyu ai ba daɗi." Ya fada da alamun ruɗewa a tare dashi. Bance komai ba illa kwallar da na cigaba da matsa kamar wacce ke cikin wani babban tashin hankali, wata tsadaddiyar waya ya ciro a aljihunshi ya fara dannawa ya ce "Bari na kira ƴar uwata ta taimaka sai mu kaita asibiti." Da "Toh" na amsa mishi. Magana yayi da wani yare da ban fahimta ba sannan ya cire wayar a kunnensa ya tsugunna a gabanmu yana jera ma Jiddah sannu kamar wata matarsa. Ban san cewa na da wani shiri a ƙasa ba domin bata faɗamin ba, ni a yadda muka tsara jami'ai ne zasu zo su kamashi lokacin da ya tsugunna a wajen, sai dai ba zato ba tsammani batare da dukkanmu biyun mun ankara ba Jiddah ta zaro wuƙa mai kaicin gaske da alama ma sabuwa ce, cikin zafin nama ta kwace a jikina sannan ta caka mishi wuƙar nan a gefen ciki, wata ƙara ya kwalla ya dafe gurin, kafin yayi yunƙurin guduwa tuni jami'an sirri da Gwamnatin Enugu ta bamu suka zagayeshi wasu daga ciki kuma suka damƙi hannunsa suka maka mai ankwa, cikin mintuna ƙalilan sai ga motar asibiti, nan aka sashi a motar tare da wasu jami'ai aka wuce da su. Bansan a wani yanayi na tsinci kaina ba lokacin da na ga jami'ai sun kama Alpha har sun saka mishi ankwa, wannan ranar na ɗaya daga cikin ranakun da bazan manta da su ba a tarihin rayuwata, bansan me ya faru ba sai dai bude idona nayi na ganni a gadon asibiti, sai a lokacin Yaya Sadiq ke fadamin wai sumewa na yi, a lokacin ne na fara tariyo abubuwan da suka faru ina daɗa mamakin yadda kama Alpha ya zo min da sauƙi haka tamkar a mafarki, dole na gode ma Allah da ya banj nasara akan makiyina sannan dole zan godewa Almajirata.Lol. Murnar da na shiga a wannan ranar ko runtsawa na kasa yi, kwana nayi ina sallar godiya ga Allah, wannan ranar kadai nake jira dama na ajiye aikin ƴan sanda, ranar da zan kama wanda yayi sanadin mutuwar mutane masu gurbi na musamman a rayuwata, Abbana, Mami, Kakannina, lukutar ƙanwata da kuma rigimammun ƴan biyun ƙannaina, a wannan ranar na ji ni na kammala ba ni da wata sauran damuwa da ta ragemin. Har ƙaramar walimah muka hada a resturant ɗin hotel ɗin da muka sauka, Sadiq ne ya ɗauki wannan nauyin. Washegari kamar yadda ya zo a hukumance tunda Alpha ya amsa laifin da ake tuhumarsa sannan yayi bayanin inda za'a samu Phalmata da yadda za'a kuɓutar da matan da ya ajiye a Alpha Villa, bayan an damƙo Phalmata da sauran masu yi musu aiki ne aka wuce da su Abuja inda anan za'a yanke musu hukunci, yaran nan kuwa kowa an haɗasu da jami'ai domin a sada su da iyaye da ƴan uwansu, gabaɗaya mu ma Abuja muka nufa inda zamu haɗu da su Daddy acan don zasu zo ganin yadda shari'ar zata kasance. Sunayen manyan ƙasar nan da suke da sa hannu a miyagun laifukan da su Alpha ke yi ba zasu kirgu ba, sunan Commissioner na daga farko-farko a cikin jerin mutanen, cikin kwanaki biyu aka cafko kowannensu, masu muƙami kowa tuni Gwamnati ta karɓe abin ta, sai dai mu yi fatan gyaruwar ƙasar mu. Ranar da aka yi zaman kotu
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24