Skip to content

Chapter 9

Chapter 9

Budurwar Mijina Book One Complete Hausa Novel 1,230 words 0 views Progress saved
Download Book

saurin sauke wayar daga kunnesa ya cigaba da goge jikinsa murmushin da bai Kai har zuci ba na sakar Masa Ina "bari na saka Kaya nabika dama na kwana biyu banje gidan ba" "Keda bakida lafiya Lubna Kika je can ma hayaniya kawai ta isheki kiyi kwanciyarki ki huta kawai bazan dade ba Zan dawo" "Aaa nima inaso na dan fita na Sha iska bana san na zauna Ni kadai a gida kamar mayya" Take naga fuskarsa ta sauya ya Kuma kasa min magana na wuce shi na nufi wajen wadrobe na bud'e dan yau zanga iya gudun ruwansa. Bakar doguwar Riga na jawo na fara k'ok'arin sakawa a daidai lokacin da wayarsa ta hau vibrating na juya na kalleshi Ina "Kila hajiyar ce ke kiranka ka fada Mata tare zamu Zo" "Lubna ba dadewa zanyi ba wlh yanzu zan dawo bai dace ma ki hau machine da tsohon ciki ba" Ban ce masa komai ba na saka hijabina na fita Palo dan wlh yau kafata kafarsa inyasan wata bai San wata ba. Mahfuz kuwa rasa yanda zaiyi da lubna yayi,ga Hadeeza sai kiransa take,bazai so yau ma yayi wa Hadeeza laifi ba, dabarar da ta fado masa hakane yasa ya shirya tsaf ya fito Kamar waya yake Yana "Wai da da Lubna ma zamu zo ok to shikenan sai kun dawo" Ya sauke wayar daga kunnesa ya nufi wajen lubna Yana "Kinga ma hajiyar ce ta kira Wai sunje gaisuwar mutuwa sai anjima zasu dawo idan sun dawo sai muje,tunda kin hanani fita bari na fita waje na siyo abu na dawo yace da sauri Yana k'ok'arin yin waje ga wayarsa na vibrating. Yana faramin bayani nima na shirya karyar da zanyi Yana zuwa bakin k'ofa na kwalla ihu tare da dafe cikina Ina wayyo Allah cikina Zan mutu" A guje yayo wajena ni kuwa na cigaba da zunduma ihu. Mahfuz ba karamin rikicewa yayi ba hakane yasa ya ajiye wayarsa akan kujera duk ya dauka da gaske ne banida lafiya Yayi waje da gudu wai zai nemo.mana machine Mai kafa uku Yana fita tsinaniyar na kiransa a waya Aikuwa da sauri na dauki wayar Ina dauka tace cikin shagwaba "Nagaji da jiranka fa haba Mana Nima fa ban karya ba yunwa nakeji Kai nake jira ka karaso muci tare" "Tunda nake ban taba ganin jaka balagaza irinki ba,tom jiya mahfuz ya bani labarin irin nacin da kike Masa yace kuma.ba kaunarki yake ba dan haka kije ki nemi wani, shegiya asarariya ko kunya bakiji ba mutum da matarsa kina wahalar da rayuwarki wajen.masa girki har da sai ya goyaki yazo yaci abinci da Kika girki kamar mijinki" Kit naji ta kashe wayar nayi saurin ajiye wayar na cigaba da zunduma ihu danaji Mahfuz ya shigo. HADEEZA Hawaye ne ya hau wanke Mata fuska ta zubawa wayarta ido...... *mg's skincare* Shin Ina matan suke馃棧锔忦煑o笍馃棧锔弇aza kuhanzarta kumatso kusa kuma kubani aran kunnuwanku domin sanin albishir dawannan shahararran company yazo muku dashi馃槂馃ぉ Hakika tabbas duk macen data amsa sunanta bazataso afita b Koda da kwayar zarra domin hakane wannan shahararren company yazomuku da ingantattun hadaddun kayan gyaran jiki masu matukar gyara fata cikin kankanin lokaci batare da sunyima fata lahani ba domin kayan mg's organic products ne bawai na bleaching ba zasu gyara ma mutum fatane yafiddomashi da ainihin natural beauty din mutum馃憣hakika duk wacce batayi anfani da kayan mg's b anbarta acan karshen bayama kuwa domin Koda sabulunsu kadai kuka dana fatanku seya fita dasauran mata ballentana Kuma kuyi anfani da gbdy beauty kit dinsu wohoho wani abun baa mgn sewanda yajaraba shine zai tabbatar鉂o笍 Shin kinafama da Pimples, black spot,sunburn, stretch mark,acne,black head, wrinkles,knuckles dama duk wani matsalan fata? Shin fatanki tana tattarewane ko kinshafa cream yabatamiki jiki馃槴 Shin inamasu cewa sunjaraba Basu dace b bi'iznillah sister's duk Wanda yayi using mg's sai godiya domin Koda iya herbal whitening black soap din kikayi anfani dashi zakiga ynd fatanki zaiyi clear Yana walwali jikinki zeyi fresh kina glowing my dear bare Kuma ace set dinne gbdy 馃ga amare uk wnd yy using bridal set dinnan baya bukatar kowani gyaranjiki domin yadda jikinki zekoma yazarce misali DNT be left behind Bridal kit:18k Beauty kit:11k Student package:7k Herbal whitening soap:3k Chat 08062991549 07046881166 07067210195 Call 08064532391 Facebook: mg's skincare Instagram:glow_with_mgs Take note pls iya wadannan numbers dinne kawai zakusamu kyn mg's babushi akasuwa馃 Do you guys wanna achieve that milky skin that turns head wherever you go馃ぉ Then @mgs skincare gat you covered 馃挴 Now is time to glow馃槏 Pamper ur skin馃Φ Shine like bride馃懓馃徎鈥嶁檧 Glow馃鈥嶁檧锔� 馃挴 tested nd trusted馃 Guarantee Sannan muna da hadaddun frames masu kyau gamai bukata yayi mgn 07046881166 [6/29, 7:53 AM] Khadija Candy: *BUDURWAR MIJINA* *NA SADNAF* *E.W.F.* *PAID BOOK* *PAGE 2* Bansan tsawon lokacin dana d'auka a durk'ushe a kasa ba,zuciyata Kamar an cinna Mata wuta ban tab'a sanin haka nake da tsananin kishi ba kawai Ina hararo irin so da kaunar da mahfuz yake gwadamin ya fara gwada wa wata,har ta d'auke Masa hankali a kaina akanta ya cemin wawiya Mara hankali waya sani ma ko zance yake zuwa wajen tsininiyar yarinya da ta Kira mahfuz da sugar,har san da yake Mata ya Kai Muna kwance ya baroni a daki ya fito Palo dan kawai yayi waya da ita. Ko dan na samu ciki hallitar jikina ya canza yasa mahfuz ya fara ganin munina Tunanin daya darsu a raina yasa na m'ike a hankali na nufi wajen da mudubi yake na fara karewa kaina kallo tunda ga saman goshina tare da shafa fuskata. Tunda na samu ciki wani irin kananan pimples suka feso a fuska ta suka Sakani Muni,siririn lebbena yayi kauri. Haka hancina da bai fiye tsini ba ya doke nasan cikin nan yasani muni ba kadan ba fari dai na Kara tunda ni fara ce. Baza'a sakani a sahun masu tsayi da kyau sosai ba akan dai mahfuz za'a sakani a sahun masu kyau duk da mace sai ta dan yi kwalliya kyaunta ke Kara fitowa. Kwalliya da nake yi yasa ake ganin kyauna sosai. mutum tara yake bai cika goma ba abinda na rasa shine nono banida cikar kirji Sam idan na ga mace mai kirji sai naji Kamar na sace ko dan mahfuz da sai da muka yi aure na fahimci Yana balain san no-no,kafin na samu ciki indai Muna zaune hannunsa na saman kirjina Yana shafawa wai idan ana yawan shafa shi Yana fitowa. Bansan Yana san nono ba sai da naga ya fara siyomin duk wani cream ko supplement akan na ringa Sha zai taimaka wajen fitomin da nono. Ba abinda banyi amfani dashi dan nono ya girma ko dan na farantawa mahfuz rai amma abin ya gagara daya ga na fara matsawa kaina ya ce min na daina takura kaina duk da haka burina na samu nono na ya girma idan na d'auke nonon ba wani abu a jikina da baya burge mahfuz. Idan ya dawo bashida wajen kwanciya sai a jikina ya gwadamin kaunar daya narkar dani a kogin Sansa burina bai wuce nayi abinda zan faranta Masa ba Koda bana so har na samu ciki banga canji a wajensa ba duk da mitar da nake akan cikin ya sani muni hakan na iya sawa mahfuz ya

Table of Contents

Chapters

26 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26