Skip to content

Chapter 3

Chapter 3

Budurwar Mijina Book One Complete Hausa Novel 1,225 words 0 views Progress saved
Download Book

lokacin da nake amarya. A kan cinyarsa bacci ya d'aukeni Yana ta shafa min kaina Ina jinsa ya d'aukeni dak'yar ya je ya kwantar dani a d'aki bacci mai dadi da nutsuwa yayi awon gaba dani. MAHFUZ Daga sakin munsharin da lubna keyi yasan bacci yayi awon gaba da ita,baisan Mai yasa hankalinsa ya rabu gida biyu ba so yake kawai ya Kira Hadeeza ya riga ya Saba sai sunyi waya ko video call yaji muryarta ta masa shagwaba a hankali ya zare jikinsa daga jikin lubna cikin sand'a ya fito daga d'akin ya fito daga palon ya fita can waje gudun ma Kar lubna ta Kara kamashi. Akan dakalin gidan ya zauna ya fara Kiran Hadeeza da tak'i daga wayarsa hankalinsa yayi balain tashi hakane yasa ya dage da kiranta. LUBNA karar bud'e k'ofar palona yasa na bud'e idona dan banida nauyin bacci ko kad'an Mikewa nayi a hankali na zauna da naga mahfuz baya d'akin. Haka kawai gabana ya Yanke ya fadi Allah yasa ba Kara Kama mahfuz zanyi Yana waya ba. Daga idona nayi na kalli agogon d'akin 12:20am. Saukowa nayi daga Kan gadon haka kawai naji zuciyata na rayamin Mahfuz na palo Yana waya da Yar iskar yarinya Nan da bansan adadin tsinuwar da na mata ba. Kishin daya rufe min ido yasa na fito daga d'akin da sauri sai dai Koda na fito baya palon hakane yasa nayi wajen tsakar gidan dan k'ofar palon a bud'e yake haka ma k'ofar gidan dagani sai sleeping dress na nufi wajen k'ofar a hankali kirjina na bugawa,zuciyata Raya min kawai take na koma Kar naji abinda zai daga min hankali daya zuciyar tawa da bakin kishi na ingizani da gwara na ganewa idona mai mahfuz keyi waje. "Dan Allah kiyi hakuri haba mana na fada miki bada gangan na kashe wayar ba abinda ya sauka a kunne na kenan.... *mg's skincare* Shin Ina matan suke馃棧锔忦煑o笍馃棧锔弇aza kuhanzarta kumatso kusa kuma kubani aran kunnuwanku domin sanin albishir dawannan shahararran company yazo muku dashi馃槂馃ぉ Hakika tabbas duk macen data amsa sunanta bazataso afita b Koda da kwayar zarra domin hakane wannan shahararren company yazomuku da ingantattun hadaddun kayan gyaran jiki masu matukar gyara fata cikin kankanin lokaci batare da sunyima fata lahani ba domin kayan mg's organic products ne bawai na bleaching ba zasu gyara ma mutum fatane yafiddomashi da ainihin natural beauty din mutum馃憣hakika duk wacce batayi anfani da kayan mg's b anbarta acan karshen bayama kuwa domin Koda sabulunsu kadai kuka dana fatanku seya fita dasauran mata ballentana Kuma kuyi anfani da gbdy beauty kit dinsu wohoho wani abun baa mgn sewanda yajaraba shine zai tabbatar鉂o笍 Shin kinafama da Pimples, black spot,sunburn, stretch mark,acne,black head, wrinkles,knuckles dama duk wani matsalan fata? Shin fatanki tana tattarewane ko kinshafa cream yabatamiki jiki馃槴 Shin inamasu cewa sunjaraba Basu dace b bi'iznillah sister's duk Wanda yayi using mg's sai godiya domin Koda iya herbal whitening black soap din kikayi anfani dashi zakiga ynd fatanki zaiyi clear Yana walwali jikinki zeyi fresh kina glowing my dear bare Kuma ace set dinne gbdy 馃ga amare uk wnd yy using bridal set dinnan baya bukatar kowani gyaranjiki domin yadda jikinki zekoma yazarce misali DNT be left behind Bridal kit:18k Beauty kit:11k Student package:7k Herbal whitening soap:3k Chat 08062991549 07046881166 07067210195 Call 08064532391 Facebook: mg's skincare Instagram:glow_with_mgs Take note pls iya wadannan numbers dinne kawai zakusamu kyn mg's babushi akasuwa馃 Do you guys wanna achieve that milky skin that turns head wherever you go馃ぉ Then @mgs skincare gat you covered 馃挴 Now is time to glow馃槏 Pamper ur skin馃Φ Shine like bride馃懓馃徎鈥嶁檧 Glow馃鈥嶁檧锔� 馃挴 tested nd trusted馃 Guarantee Sannan muna da hadaddun frames masu kyau gamai bukata yayi mgn 07046881166 [6/29, 7:53 AM] Khadija Candy: *BUDURWAR MIJINA* *NA SADNAF* *E.W.F* *Bismillahi Rahamanir Raheem* *Page 1* Wai saurin me kake yi ne haka"? Wayar sa ya Kara duba wa tare da Kara sauri Yana "Jirana ake fa karki damu yanzu zan dawo bazan dade ba yace tare da yin waje da sauri. Da ido na bishi har ya fice daga gidan naji karar tashin lifan dinsa. Tagumi nayi tare da bin kulolin da na ajiye a tsakiyar kafet din palon da ido,abincin daren dana dau tsawon lokaci ina yinsa duk sabida na faranta Masa duk da cikin dake jikina ina jin yunwa haka na hakura da cin abincin sabida idan ya dawo muci tare kamar yanda Muka Saba sai gashi daga dawowar sa ya sake wanka ya fice daga gidan da Sunan kawunsa na neman sa. Kwana biyu kenan Yana min haka. Haka na zauna raina a b'ace Ina tsaki kasa kasa ganin idan na cigaba da zama a haka batare da naci abincin ba zan cutar da kaina da abinda ke cikina yasa na zuba abincin na fara ci. Ban wani ci da yawa ba na rufe sauran na jawo wayata na fara chatting abinda kawai zai rage min kadaici da takaicin fitar da mahfuz yayi ya barni ni kadai a gida kamar Mayya. Mahfuz bai dawo ba sai wajen goma na dare zuwa wanan lokacin Raina ya Kai kololuwa wajen b'aci kafa kawai nake girgiza wa Koda ya shigo da sallama ciki ciki na amsa mishi,ya saki murmushi Yana "Afuwan tawan wlh wani waje na raka kawu bansan zamu dade haka ba kiyi hakuri kinji matata" Bansan Mai yasa bana iya dogon fushi da mahfuz ba Yana min murmushi da yar murya zanji na sauko. Ledar daya shigo da ita ya bud'e Yana "Kinga kayan kwadayin dana taho Miki dashi A binka da mai ciki da sauri na wafci ledar ganin alewar Madara da gulisuwa yasa na washe baki dan duk wani Abu Mai Madara da siga Ina so. Sai da na fara Shan alewar Madarar na kalli mahfuz da ya zauna a kasan kafet Yana Danna wayarsa "Baza ka ci abincin bane?" "Wlh kawu ya tilasta min cin abinci a gidansa sai dai gobe ki dumama min kafin na fita" "Yanzu ko cokali daya bazaka yi ba sabida Kai na girka fa" "Ai nace Miki gobe sai kimin dumame wlh yanzu a koshe nake" Badan raina naso ba na cigaba da Shan alewar Madarata shi kuma ya mike kafarsa da hannu bibiyu Yana latsa wayarsa har da dan murmushinsa. Ido na zuba Masa Ina tunanin canjawar da yayi a kwanakin nan,Mahfuz mutum ne da bai wani damu da chatting ba dan sau tari ni nake tilasta Masa yin chatting sabida Ina tura Masa sakwanin ta watsapp,ada idan ya dawo gida ko waiwayar wayarsa baya Kara yi sai dai yayi ta jana da hira Yana bani labarai idan yaga na dauko wayata sai ya kwace yace a hakura da danna wayar nan azo a ji da ni amma a kwanakin nan har da asuba Zan ga Yana latsa wayarsa ban taba zarginsa ba bana Jin Zan Kuma zarge idan na tuna San da muke yiwa juna,ba Kuma mu dade da yin auren ba tunda yanzu shekara biyu da auren mu a yanzu Allah ya azurtani da samun ciki "Wai Mai kake yi a wayar kake ta murmushi haka"? Dagowa yayi da sauri Yana "Da Abdul muke hira fa sai dariya yake bani kinsan halinsa da barkwanci" Murmushi nayi nima Ina "Gwauro ba har yanzu sai ruwan

Table of Contents

Chapters

26 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26