Skip to content

Chapter 13

Chapter 13

Budurwar Mijina Book One Complete Hausa Novel 1,230 words 0 views Progress saved
Download Book

irin Ajiyar zuciya ya sauke daya ga Hadeeza ta bar gidan,shi baiga abin Jin haushi dan ya b'oyeta ba yanzu da lubna tazo ta ritsa ta mai zai ce Mata har ga Allah bai tab'a tunanin zata zo Masa har gida batare da ko tsoro ba,har mamakin confidence dinta yake,Koda ba wani Abu suke yi ba ai bai dace lubna tazo ta ga ya kawota har gida ba, duk wanan munafikar makociyar tasu ce ta jaza Masa Kuma sai ya rabata da Lubnar baiji dadin fushin da Hadeeza tayi ba ya Kamata ta fahimce shi. Mahaukacin bugun da aka yiwa k'ofar yasa shi mik'ewa yayi waje ya ma riga da yasan lubnar ce sai daya je bakin k'ofa ya tuna bai d'auke basket din abincin ba Yana bud'ewa lubnar ta Fada gidan tana hucci Mahfuz kuwa ya hade rai Yana "Lubna daga yau karki sake ki Kara min wanan haukar ke yanzu ko tararki akayi akace miki na kawo mace gidanan sai ki yarda kina nufin zargina kike"? Ko ta kansa ban bi ba na ratsa gefensa nayi cikin gidan sai da na hau napep naji Kamar na rufe kaina da duka da nasani ban Kira shi a waya ba da tahowa kawai nayi da kila na ritsa Yar iskar yarinya,ai nasan dole ma kafin na dawo yasa ta gudu zuciyata ko gezau batayi ba na yarda dari bisa dari itace ta biyoshi har gida dan taga bana Nan, Basket din abincin dana gani ya tsakiyar palon ya Kara tabbatar min da zargina abinci ta kawowa mahfuz har gidan Aurena,kila ma har iskanci sun yi,dandaga muryar ta da naji da goyata da tace ayi nasan yarinya Yar duniya ce Yar iska Basket din na d'auka a daidai lokacin da Mahfuz ya shigo Yana cigaba da bambamin fadan zargin sa da nakeyi. "Mahfuz yanzu dan bana Nan shine zata kawo maka abinci har gida"? "Lubna Nagaji da wanan halin naki ni nace Miki macece ta kawo min abinci tunda kika tafi kabiru abokina yasa ake kawo min abinci wai wanan wane irin Hali Kika tsiro dashi ne?kishi hauka ne"? Ni kadai nasan halin da nake ciki jikina har rawa yake mahfuz na san sakamin hawan jini, palona na fara karewa kallo Ina ganin kamar Zan iya ganinta ma a cikin gidan, Ban bi ta kan masifar da yake ba na Mik'e da basket din a hannuna na Shiga dakina tamkar zan ganta a ciki Koda na Shiga ciki ma har karkashin gado na tsugunna na duba na kurawa gadona Ido naga ko an kwanta a akai shigowar mahfuz d'akin bai hanani cigaba da dube dubena ba Inda yaja wani dogon tsaki ya nufi wajen kayansa ya fara zurawa Na zauna a gefen gadon na zuba Masa Ido hawaye na zubo min "Mahfuz mai na maka dana cancanci haka daga wajenka, mahfuz ko aure zakayi bai Kamata ka kawo budurwar ka har cikin gidanan tazo ta gane min sirrina ba,mahfuz ni nasan ba rageka da komai ba Ina iya kokarina dan naga na faranta maka rai, a yanzu da nake d'auke da cikinka bai Kamata ka daga min hankali ba,wlh Tallahi budurwar ka tazo gidanan,mahfuz palona kamshin turare yake na daban da nida Kai mun San bamu irin wanan turaren har yanzu bamu yi shekara biyu da Aure ba,mahfuz mai kake nema a wajen wata da bani dashi,wlh tallahi yarinya da ta san Mai takeyi bazata ringa dafa maka abinci ba sabida tasan kana da aure, mahfuz bansan yarinya nan ba amma na mugun tsanarta mahfuz na yarda idan ma auren zaka Kara ka kara ka auri koma wacce Banda tsinanniyar yarinya nan da har dan bana nan zata biyoka har gida duk halin da kake ciki da ita nasani mahfuz magana ce kawai banayi,haka zamu kwanta dakai ka fita ka barni kaje kana waya da ita daddare wane irin kallo kake so tayimin shashasha ko wacce bata da matsayi a wajen mijinta?namiji shi yake fara siyawa matarsa mutunci da daraja a wajen budurwarsa,idan har kana min haka kana tunani ko Allah ya kaddara aurenka da ita bazata balain rainani ta ringa min gori ba,Kai kana tunanin idan ka auro mace irin wanan da bata damu da kana da Mata duk abinda ta ga dama shi zatayi da muyi fada da Kar muyi fada ba abinda ya dameta har kana tunanin zamu zauna lafiya idan ka aurota". "Hmm Ke dai kin d'auko wani banzan halin da bansanki dashi ba ni nace miki Ina neman aure ne,ai ko budurwa ma zan kula kinsan dai ba haramun bane Allah ya hallata Mana mu Kara auren ballantana ni bakiji a bakina nace Miki Zan Kara aure ba,amma tunda kin dorawa kanki balain kishi har dasu zargi ke Kika jiyo kizo muje na maidaki gida" Wani mugun kallo na watsa masa na kwanta akan gadon dan na dawo gida kenan,tunda abinda yakeso kenan na bar gidan Ganin na share shi yasa ya fice daga d'akin a daidai lokacin da mahaifiyata ta kirani Ina dagawa na bata labarin duk abinda ya faru na kara da "tunda har dan.bana gidan take kawo Masa abinci har gida gwara na dawo gidana mummy Nagaji yarinya Nan so take ta zautar dani" "Ke dai ba bazaki bi komai a hankali ba Zaki kuwa dorawa kanki hawan jini yanzu ke da kika je kinganta da idonki,a gaskiya kishin naki ya Miki yawa dole ki daura aure da hawan jini kuwa, nace kiringa bin komai a hankali,idan har namiji ya fara kulle kullen nan, wlh baki Isa ki Hana shi ba ko dafa kanki Zaki ringayi kina bashi Yana ci,wanan haukar kishin da kike sai dai yasa ma kifita a ransa kuyita fada dashi,yaji ya daina ma Jin dadin Zama dake a karshe ma ya fara Shirin auren amma tunda kin k'i bin shawara ta shikenan Anjima zan turo miki zainab ta zauna dake har ki haihun Allah dai ya kyauta" Daga haka ta kashe wayar Mahaifiyata bazata Gane halin da nake ciki ba ni nasan wanan yarinya da ta likewa mahfuz idan har banyi dagaske ba idan ni ban hanata shigowa ba fitar dani zatayi. Badan babu kyau zubar da abinci ba naso na zubar da abincin a karshe na bawa almajirai narasa Ina Iyayenta suke suka barta take aikin dafawa saurayi lafiyayyen abinci haka,waya sani ma ko zaman kanta take Yar iskar. Idan ferfesun mahfuz keso nima ya ringa siyowa yaga idan ban masa ba,duk bakin ciki da takaici ya cikani. Koda na Shiga gidan mmn Iman masifa ta hau yi tana "da nasan Zaki Kira mijinki wlh Tallahi da ban kiraki ba,Haka kawai kin zubar min da mutuncina yanzu zai ringa mun kallon munafika,ke sam baki iya ba da so kike ki tabbatar ko ki kamashi,ai da baki kirashi a waya ba da muka gama waya dake sai kizo ki ritsa shi gajen hakurinki ya Miki yawa" "Hmm mm Iman bazaki gane ba,kisa kaina a matsayin kece na kiraki nace ga budurwa ta shigar Miki gida baban iman na Nan wlh abinda nayi zakiyi" "Hmmm ai shikenan Allah dai ya kyauta" "Dan Allah baki ga fitowarta daga gidana ba Naga dai kayan abinci bansameta ba" "Ya zaayi ma kisameta kiringa da kin kirashi tab a gaisheki ni banga kowa ba

Table of Contents

Chapters

26 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26