Skip to content

Chapter 26

Chapter 26

Budurwar Mijina Book One Complete Hausa Novel 1,143 words 0 views Progress saved
Download Book

biyu zuwa k'ofar dakinta na manne a jikin k'ofar da aka turo ban Bari k'ofar tayi Kara ba. "Dan Allah har ki bar gidanan karki yi abinda zata gane mu pls" Shine abinda ya sauka a kunnena muryar mijina uban yata. Wani Duhu ya giftamin ta Ido naji dum akaina. Nidai bansani ba ko Nike da iko da jikina barin bakin k'ofar nayi na zagaya ta bayan d'akin da window yake burina na leka mijina na tabbatar da shi naji muryarsa A tangal tangal din da hawan jinin a wacce ta samu karamin tabin hankali na leka ta window. A kwance take a kirjin mijina ya cusa fuskarsa a tsakiyar kirjinta ta kankame shi tana shashafa shi sai sauke ajiyar zuciya take. Wani duhu ya kara giftamin sai da na dau tsawon lokaci na fara ganin haske "Jeki kitchen ki d'auko ashana ga jarkar fetur can ki cilla musu ki Konasu Lubna" "D'auko wuka ki Shiga har d'akin ki cakawa Ummi shima ki caka Masa" "Jeki kwanta ki dauki mataki Mai kyau" Duk zuciyata ke sakamin har na koma Palo cikin sand'a. Tamkar wacce aka bawa umarni na shige d'akina na kwanta nayi rub da ciki,abubuwa da yawa na dawo min kaina,fuskar Abdul abokin mijina kawai nake gani,Ummi Mahfuz,waye ya Kamata nafi Jin zafinsa. Ina Jin labaran cin Amana Amma nawa yayi Muni budurwar miji har gidana har dakina" Na kasa furta innalillahi wa Inna ilaihi rajiun idona dai kawai a rufe yake. Anya a duniyar cin Amana akwai irin nawa kuwa"? Dole akwai abinda mmn Iman ta Sani bata gayamin ba ta munafirceni,na Zama shashasha Ina bautawa budurwa mijina a gidan Aurena. Ba digon hawaye a idona zuciyata kawai nasan ke zubar jini. Ina kwance a rub da cikin naji shigowarsa a lokacin da ya kashe tv ya shigo d'akin. Ya kwanta a gefena bayan ya Kara gudun fanka. Tamkar huramin wuta ake a jikina haka naji na kasa tunanin mai ya dace nayi, Ki tashi ki d'auko wuka kizo ki caka Masa Lubna Allah sarki Mata da yawa da suke kashe mazajen su waya sani ko cin amanar da aka musu kenan" Tsawon awa uku akwance rabi mutum rabi Mai tabin hankali zuciya da gangan jiki azabar k'una aka Kira sallah asuba alarm ya tashe shi ya mike ya bar gefena kafin naji Ina shakar iska Mai kyau. Idona rufe sai da yayi wanka ya fito ya zura jallabiya ya girgiza kafata Yana tashi kiyi sallah karki makara yayi waje. Karar rufe k'ofar gidan da yayi yasani na mike tsaye. Na nufi kitchen na d'auko katon muciyata Ina fita tsakar gida na kulle k'ofar da mukulli na Kara komawa na dauko wuka Mai kaifi. Wandone dama a jikina. Tura k'ofar dakin nayi tana kwance da santala santalan cinyarta a waje. Sai zuba minshari take. Take yanda na ganta da mahfuz ya fadomin. Jikina rawa yake hannuna damke da muciya. Wani mugun bugu na Mata da muciyar akanta ta kwalla Kara a gigice ta mik'e zaune Kallonta kawai nake Ina wani iirn hucci dama kece BUDURWAR MIJINA,? girgiza min kai ta fara yi da sauri ta gwallo idonta tana kallona Tunda na gansu sai a yanzu hawaye ya zubomin "DAMA KECE BUDURWAR MIJINA KIKA ZO MIN HAR CIKIN GIDA DAN KI GANE MIN SIRRINA ?UMMI DAMA KECE BUDURWAR MIJINA KIKA BIYO MIJINA HAR GIDA,KARUWANCI HAR GIDAN AURENA UMMI"? "AUNTY DAN ALLAH KI RUFAMIN ASIRI KI TSAYA NA MIKI BAYANI" Wani irin ihu nasa kamar sabon kamu nayi kanta na hau hada kanta da bango na damke gashin dokinta da k'arfi Ina ja Ni nasan daga farko layi har zuwa kasan layi ana jiyo muryarta ban damu da jinin dake zuba a kanta ba Kamar wata doki sabida karfin da nake ji a jikina na cigaba hada kanta da bango Ina bugu. "Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun lubna karki kashe yar mutane ki budemin k'ofar Nan naji muryar mahfuz da karfi"...... Dandandan akwai show a gaba akwai Abubuwan daya Kamata a warware Taya Hadeeza ta samu ta rinjayi Mahfuz ya kaita har gidansa?Taya akayi Abdul shima ya yarda ya Kai Hadeeza gidan Lubna? Kallon da Mahfuz yake yawan cewa lubna zaiyi dama d'akin Hadeeza yake tafiya"? Ya kuke ganin zata Kaya tana bude k'ofar?ko ta karfi ake shiga gidan? Mahfuz na auren Hadeeza kuwa? Hmmm kubiyo sadnaf ta Baku labari da dari biyar dinku kacal, Ga wayanda zasu biya yau zuwa gobe karfe dayan rana akwai discount din dari biyu dari uku zaku turo kacal inya wuce gobe dari biyar hanzarta Kar ayi bake馃馃馃馃馃 KAYAN MATA Assalamualaikum kina mace hadaddiya komi kincika ama kinada nakasu tawurin dadadawa miji? Shin kinkai kin isa kina gogayya d sauran mata Amma tafannin ozaroom mishkila tasamu? Shin sanyi y addabeki tayanda Baki iya gamsarda miji kullum kina makalemai yana kauda Ido? Shin minene matsalar? Kinshiga ko Ina kinnemi magani bawani chanji? Tosaurara yar uwata aminiyar arziki, ubangiji yakawo mikini har inda kike,kizo kiji qawata, Inada maganin sanyi me fatattakar kowani irin sanyi duk fitinarshi d izinin ubangiji seyabarki, Munada magungunan mata masu matuqar kyau,hadaddu gangariya kizama t gaban goshi,komi kikace oga yace don, 馃グ kikerewa sa'o'i, kizama abun riritawa abun tarairaya a kudi qalilan,karki cuci kanki kizauna kina cewa ayni nasan kaina,a inadin? Wallahi ko kanada kyau qara d wanka Kisha kiyi qattt kigigita oga, Munada tsumi nau'i nau'i Gumba ta madara,ridi,gyada,dabino,kwakwa,dasauransu Akway ruwan jaraba Ruwan Dadi Hadin minannas Hadin dafa kaza(manta uwa) Hadin yar gaban goshi, Turarukan mallaka. Duk a farashi mesauqi. Senajiku kusiya kuyi godiya Kuma kumin addua鉂わ笍nagodeAn dauko wannan littafi daga shafin www.hausanovels001.com.ng ku ziyarci shafin na www.hausanovels001.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from www.hausanovels001.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel.

Table of Contents

Chapters

26 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26