Chapter 1
Chapter 1
[6/29, 7:53 AM] Khadija Candy: *BUDURWAR MIJINA* An dauko wannan littafi daga shafin www.hausanovels001.com.ng ku ziyarci shafin na www.hausanovels001.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from www.hausanovels001.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via Whatsapp button on website its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT *NA SADNAF* *E.W.F.* *PAID BOOK* *PAGE 3* Sauk'owa yayi daga Kan machine d'in fuskarsa d'auke da murmushi dan yasan fushin zagin da lubna ta mata take yi. D'auke kanta tayi ta maida gefe Mahfuz ya sake sakin murmushi Yana "Kiyi hakuri wlh wanka na Shiga ta d'auki wayar bansani ba" "Jiya ma haka kace wanka ka Shiga ta d'auki wayar ta zageni kaga ma d'aukar wayarka bashida amfani tunda ko na d'auka itace ta bugo dan ta zageni na rasa mai na tare mata inaga baka tab'a bata labarina ba in ba dan kaddara ba tasan bata Isa ta rigani samunka ba" Tace tana Jan siririn tsaki "Kiyi Hakuri hakan bazata sake faruwa ba ki dan saki fuskarki mana sweet dina" Sai a lokacin ta dan saki murmushi tana "Hmm Mahfuz ya zancen namu saura wata biyu naje gida fa"? "Karki damu insha Allahu madam na haihuwa zan yunkuro ki kwantar da hankalinki Sai a lokacin Hadeeza ta saki murmushi tayi wal da Ido ta juya ta koma ciki Bata fi minti biyar da Shiga ba ta fito da wani leda mai dan kyau ta mik'awa mahfuz daya washe baki Yana "Bakya gajiya sweetyna" Ya bude ledar ya dauko dan karamin flasks din potato balls ne a ciki ai sauce din albasa sai kamshi ke tashi har dasu chocolate dasu biscuit. Yana Jin dadin yanda Hadeeza ke hada Masa break fast sabo da girkunanta yasa baya damuwa yaci na gida duk da yasan lubna itama ba a baya bace wajen iya girkin. Bai tab'a tunanin zai dawo da Hadeeza rayuwarsa har ta samu gurbi a zuciyarsa ba. Dan ta wulakanta shi a baya kafin ya had'u da Lubna yaso ya auri Hadeeza sai ta nuna Masa tafi karfinsa,dan zai iya cewa shine mai karamin karfi a manemanta. Yana ji yana gani ya hakura da ita,Allah cikin ikonsa ya hadu da lubna da ta saka shi manta wata Hadeeza har yaji a yanzu yasan ya had'u da wacce take Sansa sabida Allah Tuni ya shafe babin Hadeeza ya manta da ita har Allah yayi aurensa da lubna wata hud'u da aurensa sai ga Kiran Hadeeza a wayarsa koda ya daga a gigice ta jefa mishi tambayar "Mahfuz dagaske ne kayi aure"? Duk da yasan itace cewa yayi "Da wa nake magana"? Kamar zatayi kuka tace "Haba Mahfuz Kamar ya da wa kake magana Hadeeza ce" "Wacce Hadiza wai kimin bayani nagane"? yace Yana hararar wayar dan karfin hali yake gani a wajenta" "Mahfuz dan Allah ka bari nasan kasan wacce take magana so kake kawai ka wulakantani" Tsaki yayi ya kashe wayarsa ya danna lambarta a block dan kallon mai kwadayin abin duniya yake mata ko uban Mai yasa ta kirashi yanzu ko kunya bata ji ba. Kwana biyu a tsakani ta sake kiransa da wani lambar Yana Jin itace ya Kara kashe wayarsa Yana mamakin mai take nema a wajensa. Bata hakura ba ta hau tura Masa message ta watsapp da message ko karantawa baya yi sai ya goge. Bata tab'a fashin kiransa ba Kiran da take masa har da tsakar dare akan dole ya koma kashe wayarsa daddare ranar da abin ya ishe shi Yana d'aukar wayar yace "Wai Mai kikeso a wajena ne Hadeeza naga mun rabu nayi Aurena mai Kuma kike nema a wajen wanda ba ajinki ba"? Cikin muryar kuka tace "Mahfuz yanzu dagaske kayi aure kana nufin ka hakura dani ya kake so nayi da san da nake maka wlh ko a baya Ina kaunarka wlh gwadaka nake daga naje gida na dawo kawai naji labarin aurenka a wajen Abdul (A gidan kanin mahaifinta take a zaune tana karatu Iyayenta suna garin gombe) Tsaki mahfuz yayi yace "Hadeeza ba gwadani kike ba a samarinki da kikeso ki aura aka yaudareki shine yanzu Kika nemoni nidai a yanzu nayi Aurena na auri matar da nake balain so da kauna muna zaune lafiya Dan Allah ki rabu dani ki daina kirana a waya" Daga haka ya kashe wayarsa ko minti biyar ba'ayi ba sai ga message kaca kaca daga wajenta na ban hakuri da irin san da take mishi ya bata dama ta gwada mishi irin san da take masa,ta yarda zata je ata biyu za Kuma tayiwa matarsa biyayya. Ko ta kanta bai bi ba ya danna Mata blocking dan ko mai zata yi bayajin zai saurareta shi da Allah ya bashi finta ma Lubna Mai so da kaunarsa ba abinda ta rage shi dashi. Ga mamakinsa Hadeeza haka ta cigaba da canza lambobi tana kiransa ko da zai gaya mata bak'ar magana hakan bazai saka ta fasa kiransa ba har ta kai message din safe daban na rana daban na dare daban. Bai tab'a bari lubna tagani ba take yake gogewa dadin dayaji lubna bata mai bincike bata damu da taba masa wayarsa ba. A haka ya samu shekara da Aurensu da Lubna watarana yaje
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26