Skip to content

Chapter 6

Chapter 6

Budurwar Mijina Book One Complete Hausa Novel 1,225 words 0 views Progress saved
Download Book

muka isa gida yanda nake langab'ewa Ina matsar kwalla yasa bai motsa daga kusa dani ba sai aikin yimin sannu da yake. Abincin ma sai shi ya shiga kitchen ya dora da wanan na samu na goge Kiran da tayi dazu so nake nayi ta hadasu fada. Sai da ya bani abinci naci na koshi Ina yamutsa fuska ya bani magunguna na Sha. Sanan naga ya dauki wayarsa yayi hanyar palo Na riga nasan Kiranta zaiyi a waya. Fitarsa da minti biyar sai gashi ya shigo bansani ba wayar yayi ko baiyi waya ba,Ya zauna a gefen gadon Yana matsamin kafa da hannu daya Yana latsa wayarsa da hannu daya,Sam fuskarsa ba walwala ba Kuma abinda ya shafeni addua ma nake Allah yasa ta sosoka masa Ashar wlh da wayar zai shigo hannuna text zan Mata na zazzageta. A ranar ma ban bari ya fita waje waya ba dan kwanciya nayi a kirjinsa,ko da bacci ya fara daukana idan na tuna sai nayi sauri na kankame shi. A ranar dai baiyi waya da ita ba duk da naga alamar idonsa biyu ba bacci yayi ba MAHFUZ Tunda suka dawo gida yake gwada lambar Hadeeza yake jinta a kashe,ya dubata ta WhatsApp nan ma Bata hau ba ya rasa duk Mai ke mai dadi,yasan fushi tayi sam bai so yau baije wajenta ba,dan shima ji yayi Kamar ya dade bai ganta ba,burinsa bacci ya dauki lubna ya fita waje ya kirata a waya idan yaji a kashe ya kira Ameera kanwarta,muryrta da zaiji kawai zai saka ya samu nutsuwa sai dai lubna kankame shi tayi taki barin jikinsa abu kadan sai yaga ta bud'e idonta a haka ya kwanta kamar yayi kuka baccin Kuma yak'i daukarsa. Allah Allah yake gari ya waye idan ya fita massallaci ya kirata a waya. Wajen tara yaje gidan nasu. Kiran sallahr asuba a kunnensa hakane yasa ya mik'e da sauri ya fada bandaki ya daura alwala a daidai lokacin da Lubna ta mik'e zaune itama tana yamutsa fuska "sannu ya jikin naki"? "Wlh har yanzu ciwo yake min ga kaina Kamar ya rabe gida biyu dan Allah ka zauna kaja mu sallah ba sai kaje massallaci ba" "Haba Lubna jiya ma fa banje massallaci ba ai ana iddar wa zan dawo bari naje" Yace da sauri tare da yin waje ya jefa wayarsa a aljihunsa. Na tabe baki dan nasan Kiranta zaiyi a waya,yau ma bazan bari yaje ko'ina ba Sai dai mayyar taci kanta,na tsaya ma Ina neman dorawa kaina hawan jini bayan ga hanyoyi nan da Zan bi wajen rabasu,yanzu wayarsa ta kara zuwa hannuna lambarta zan d'auka Bai dawo gidan ba sai wajen shidda da rabi. Daga yanda naga fuskarsa ba walwala nasan ko bai samu yin waya da ita ba ko Kuma ta zazzage shi Kamar yanda nake fata da Addu'a. Ban koma bacci ba na dafe marata na fara wash wash,ya dafe kansa Yana "Lubna wanan wane irin ciwon Mara ne" Ban bashi amsa ba na hau matsar kwalla. Mahfuz kamar ya sa kuka dan bakin ciki,dan Yana ta Kiran Hadeeza a waya bata d'auka ba,karshe sai text tayi Masa da Allah ya hada kowa da rabonsa bazata iya ba tunda matarsa ke controlling dinsa. Ya Kira dan ya bata hakuri Sam taki dagawa,bashida burin daya wuce tara yayi yaje gidan nasu. Sam bazai iya hakura da Hadeeza ba Yana jinta a ransa ba abinda yake Balain so da ita sama da shagwabarta ko ba'a fada ba yasan idan ya mallaketa zai Sha soyayya sai gashi yau ma Lubna na neman hana shi fita. magungunan ta ya d'auko mata ya siyo kayan shayi ya hada mata. Sai dai Koda ta Sha bata fasa ihun ciwo mara ba,Yana ji Yana gani Lubna ta dabaibaye shi bai samu ya fita ba a ranar. Hadeeza kuwa ta Kara cika tayi fam tana ganin wulakanci mahfuz din ke san yi Mata ta dauka da ta Masa text din zai zo gidansu da sassafe sai dai ko keyarsa bata gani ba. Sam ba walwala a fuskar mahfuz har wani tsawa tsawa yake min idan zaiyi magana hannunsa manne da wayarsa nima bakin cikin duk wanan abun akan wata can a waje ya keyi dan kawai bai samu fita wajenta ba,har mamaki yake bani wlh bantab'a zaton haka daga wajen sa ba, banga ta Zama ba ko Ina so ko bana so dole gobe zai fita Kuma yaje gidan nasu sai dai Allah ya kawomin mafita. Daddaren ma ban bashi space ba haka.na manne Masa banga Kuma alamar zai fita waje waya ba sai tsaki da nakeji yanayi akai akai. Washegari kuwa da sassafe ya fice daga gidan kamar akan Kaya yake mahfuz da ni nake tilasta.masa fita sabida kar ya makara sai gashi yau wata ta d'auke masa hankali koma wacce yarinya nan ban yafe mata ba na share hawayen daya zubomin na dauki wayata dan na Kira Mahaifiyata ita kawai zan Kira na samu kwanciyar hankali dan nasan zata bani shawarwari masu kyau. Mahfuz Dak'yar ya samu Hadeeza ta fito dan sai da yayi ta turawa gidansu Tama k'i d'aukar wayarsa. Koda ta fito shi kadai ya hau maganar sa Yana bata hakurin dalilin dayasa bata ganshi ba Lubna ce bata da lafiya kwanan su biyu a asibiti bada gangan yak'i zuwa ba Sai a lokacin Hadeeza ta kalleshi idonta cike da kwalla tana "Mahfuz Ina kaunarka amma ya zama dole na hakura da Kai dan na riga da nasan b'atamin lokaci kake,wlh bazaka iya Aurena ba,bazaka iya rik'e Mata biyu ba,dan kana balain tsoron matarka mahfuz zagi da cin mutunci haka ta zuba min sau uku kenan tana zagina da iyayena har karuwa tace min idan har bata da lafiya zata zageni ne"? "Wlh da gaske Lubna bata da lafiya ko dai wata ce ta kiraki ta zageki matar da bata da lafiya taya har zata kiraki ta zageki"? "Hmm Mahfuz kenan karya Zan Mata kenan wlh Azeem bamu dade da waya da kai ba na sake kiranka ta d'auka ta hau zazzagina har da cemin Kai ba sona kake ba,na like ma Ina ta dafa maka abinci Kamar wata matarka" "Ikon Allah Mahfuz yace tare da d'auko wayarsa ta Shiga call log na ranar asabar din sai dai Sam bai ga Kiran Hadeeza ba dan suna waya yake goge lambar yanzu ya haddace lambar baiyi saving a wayarsa ba har wane lokaci Lubna ta daga wayar tayi zagin bayan yazo fita ta fara ciwon maran "Wlh Kinga banga Kiran naki ba" "To na mata karya Mahfuz" "Ba haka bane bance kinyi karya ba amma kiyi hakuri dan Allah hakan bazata sake faruwa ba insha Allahu" Dak'yar dak'yar ya samu Hadeeza ta hakura Inda yace Mata ta daina kiransa ta bari ya ringa kiranta da kansa gudun sake faruwan hakan da haka Suka rabu akan zata aika Masa abincin Rana,dan ba karya Yana Jin dadin abincin ta sosai. Yana isa office Kiran lubna na shigo wa wayarsa sai daya zauna ya daga wayar yana tunanin ko wani matsalar ne ya taso,ga mamakinsa Yana dauka lubna tambayar sa tayi ko yaje office lafiya dalilin dayasa ta Kira kenan. Murmushi ya saki Suka dan tab'a hira da ita kafin ta Masa sallama. Yana kashewa ta

Table of Contents

Chapters

26 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26