Skip to content

Chapter 4

Chapter 4

Budurwar Mijina Book One Complete Hausa Novel 1,214 words 0 views Progress saved
Download Book

ido yake ya kasa tsayar da budurwar balle mu sha biki" Yana chatting muna hira har zuwa sha daya da rabi na dare kafin mu tafi daki mu kwanta. Fitsarin da nake ji ne ya farkar dani sai da na wartsake na mike zaune ga mamakina mahfuz baya d'akin har Kara shafawa nayi Naga ko dai lumewa yayi a bargon da muka lulluba sai dai bargone kawai baya d'akin. Kasa kunnena nayi naji ko dai Yana bandakin a daidai lokacin da na daga kaina Ina kallon agogo d'akin karfe biyu da minti goma Sha biyar na dare. Mik'ewa nayi a hankali Ina mamakin Inda Mahmud yayi dan nasan baya bandaki tunda banji motsi ba. Sai dana kunna fitilar d'akin na nufi wajen k'ofar dakin da aka dan bud'e idan har zan tab'a k'ofar ba abinda zai hana yayi Kara daga d'akin Ina Jin maganarsa hakane yasa nake so naji mai yake cewa zuciyata fal da mamaki da wa Mahfuz yake magana a tsakar daren nan ya baroni a daki ni kadai. A hankali na samu na fito daga d'akin batare da na bari kofar tayi Kara ba, cikin sand'a na fito na nufi palon da yake akwai siririn corridor kafin a iso palon. Hasken wayarsa kawai nake hango wa yayi rub da ciki fitilar palon a kashe. "Nifa bana ganinki sosai wai me hakane"? Abinda ya sauka a kunnena kenan daya bala'in fadar min da gaba har sai dana dafe cikin jikina sabida motsawar da yayi. Ban motsa ba na tsaya Ina cigaba da Jin hirarsa da macen da nake Jin saukar muryarta a kunnena. "Bana so na kunna haske na tashi Ameera fa Wai yanzu baka ganina" "Rowa kawai zaki min Kisani mafarki a banza" Dariya macen ta kyalkyale dashi Yana shirin magana bansan rike numfashina nayi ba Ina sakin numfashin yayi jifa da wayar da sauri Yana "Lubna" Duk da jikina balain rawa yake Ina hada gumi bansan ya akayi nayi jarumtaka wajen daidaita kaina Ina "Farkawa nayi zanyi fitsari da ban ganka a d'aki ba shine na fito" "Ooo e'e'e motsi naji a waje shine na fito naga waye har waje na fita ma" Yace Yana in'ina ya sunkuya dan ya dauki wayarsa na juya jikina na cigaba da rawa nabi bango na koma d'akin Yana daga bayana Yana fadin Yana tunanin barayi sun adabi unguwar bance Masa komai ba na kwanta tare da Jan bargo dan har wani zazzabi naji Yana neman rufeni. Yana kwanciya a gefena ya fara k'ok'arin jawoni idan har na hana shi rungumeni zai zargi naji maganar da yake yi da mace. Halin da nake ciki yasa ban iya jure rungumar da yamin ba dan gani nake kamar ya manna min garwashin wuta na janye jikina banaso nayi magana sabida Zan iya fallasa halin da nake ciki bana so nayi abinda zanzo Ina nadama inaso na samu nutsuwa nayi tunani Mai kyau. Koda na janye jikina bai Kara jawo ni ba yace tom yau bbyn bayaso a tabaki kenan ya juyamin baya tare da Jan bargo saman kansa. Ido na zubawa bayansa Ina Jin tashin maganarsa a kunnena nifa bana ganinki sosai wai me hakane Rowa kawai zakimin kisani mafarki a banza. Da wa Mahfuz ke video call da tsakar daren nan har ya barni a daki ya tafi palo wacce ce ita,har yaushe Muka yi Aure da mahfuz zai fara kula Yan Mata,Anya ma mahfuz dina ne wanan ko dai mafarki nake yi na mitsini kaina wai dan na tabbatar da ba mafarki nake ba. Zuciyata wani irin zafi yake min na tsananin kishi mahfuz dama Yana da budurwa duk soyayyar Nan da yake min dama zai iya kula wata, mahfuz makota ma sun shaida irin kaunar da yake min. Soyayya mai tsafta muka yi a shekara uku da muka hadu dashi,naje banki zan bude acct shi kuma anan yake aiki,tun ban dauki soyayyarsa da wani mahimmanci ba har sai da ya samu matsuguni a zuciyata,ba Wanda baisani dashi ba a cikin dangina haka ma danginsa,kawayena Kan roki Allah ya basu irin Mahfuz sabida yanda baya iya b'oye san da yake min a gaban kowa, nida kawayena mun Sha hada Kai mu siyi layi dan mu gwada shi,Yana Jin muryar mace zai kashe dan kafin muyi aure Ina balain saka kaina a matan da suka yi sa'a da dace samun nagartace kamar mahfuz ban fuskanci wani matsala ba har mukayi aure zan Kuma iya shaidarsa dan ba abinda yake boye min,a gurin mahaifiyarsa Hajiya Ammi kawai nake ganin ban wani samu karbuwa ba duk da da yawa ance haka take bata fiye sakarwa sirikanta fuska ba,da na auri Mahfuz sai na fuskanci idan kina so ta sakar Miki fuska ki bata abin duniya a ranar zata sakar Miki fuska na Kuma ji halayenta a wajen matar yayyen mahfuz Inda Suka ce Kar na sake duk wani abu da zai hadani da Mahfuz nace Zan Kai kararsa wajen mahaifiyarsa tsana zan janyowa kaina dan bata san laifin yayanta ko kad'an. Daga aurena da mahfuz zuwa yanzu ban wani fuskanci matsala ba duk da kyautata min da yake Yi a waje da bambanci a yanzu da muka yi aure, dama can ba soyayar kudi muka yi ba shiyasa Koda muka yi aure ba wani kudi yake bani ba nima ban damu ba bansani ba ko dan ban Dade bane Zan bukaci kudi a gaba kayan abinci dan abinda bazaa rasa ba ban Kuma damu ba. Zuciyata suya kawai take bacci ya kauracewa idona zuciyata nata sak'a min na tashe shi na tambaye shi da wa yake waya,wata zuciya.kuma na hanani akan nabi komai a hankali. Kiran sallah asuba a kunnena dama Ina rigashi tashi sallah ni nake tashinsa. Haushinsa da nakeji yasa ban tashe shi ba naje.na daura alwala inaga motsin rufe k'ofar bandakin ne ya tashe shi. Koda ya mike Yana Hamma yace "Da ban tashi ba,bazaki tasheni ba kenan"? Ban ma iya bashi amsa ba bama naso nayi magana dan wani abu ne ya tokareni a mak'oshi. Banida burin daya wuce ya tafi massallaci na dan bincike wayarsa dan na tabbatar da zargina. Sai dai yana fitowa daga bandaki ya zura wayarsa a jallabiyarsa yayi ficewarsa. Zuwa yanzu zargin mahfuz nada budurwa ya tabbata dan a kwanakin nan yafara haka,amma baya fita da wayarsa har password dinsa nasani dan sunana ne. Ina zaune ne kawai akan sallaya zuciyata fal da tunanin da mamakin mahfuz dana d'auko so da yarda na dora masa. Mahfuz ba mutum bane da idan yaje massallaci Yake dadewa sai gashi har gari ya fara haske bai dawo gidan ba. Tuni wani irin kishi ya turnike ni jikina har rawa Yake. Har zan fita waje na koma dakina na dauki wayata tare da bin umarnin zuciya ta akan na gwada Kiran wayarsa naji ko dai wayar yake. Ina kuwa kira ya nuna call waiting Wanda hakan ya kara saka kirjina nauyi sabida kishi ban hakura ba na cigaba da kira dan idan har ya daukeni da mahimmaci ya Kamata ace ya dauki wayata tunda nasan dole zai ga kirana sai dai bai dauka ba nima ban fasa Kira ba nasan bazai wuce layin unguwar ba dan gida uku ne tsakanin mu da massallaci da hijabin jikina na fita

Table of Contents

Chapters

26 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26