Skip to content

Chapter 20

Chapter 20

Budurwar Mijina Book One Complete Hausa Novel 1,205 words 0 views Progress saved
Download Book

wayar nace "bakuwa ce fa bai dace nasa ta aiki ba" "Kika dafa Mata Abu ban yafe ba kibari ta dawo tayi kayanta ke ai Yar aiki ma aka kawo miki har girkin Daren ma ki bata tayi" "Lalalala Haram wata tayiwa mijina girki ni zan ma girki da kaina" "Dariya yasa Yana to ayi mana mai dadi Zan aiko da kayan ciki anjima a dan yi Mana ferfesu" "Waw abban Mahfuz kudi Wai ka samu haka kasan kuwa inata shaawar ferfesun kayan cikin nan bana so na maka maganar ne bansani ba ko bakada kudi" "Da kin gayamin ai tunda na Sunan soyewa akayi karki damu Zan aiko anjima bari nayi wani aiki ya sakar min kiss ta wayar nima na mayar Masa ya katse wayar. Bai sabar mun da haka ba hakane yasa na kasance cikin tsananin farinciki Ina adduar Allah ya Kara buda Masa inasan irin rayuwar nan dama ne bansamu ba. Naso nayi girkin amma sabida mahfuz ya hana ni na hakura idan ta dawo nace ta girka abinda take so din. Bacci bacci na fara ji na kwanta a doguwar kujera Mimi bata da rigima ko kad'an ba karamin abu ke sata kuka ba. Baccina ya fara nisa naji an kwankwasa k'ofa na Mike na kalli agogo karfe daya da rabi. Ina bud'ewa naga Ummi ce da fuskarta ke d'auke da murmushi nan da nan ya dishe ta daskare waje daya tana kallona ni na dauka ma wani abin ne na juya dama da haguna na dawo da kallona kanta Ina "Ummi lafiya kuwa"? Nidai a idona sai naga kamar murmushin yake tayi idonta har ya canza kala "Sannu da gida Aunty kinyi kyau" "Anya kalau kike kuwa ummi na ganki wani iri ko duk gajiyar ce"? Gyada min kai tayi a daidai lokacin da ta shigo tana "bana dan Jin dadi ne wlh" "Allah sarki sannu inaga gajiya ce ki watsa ruwa ko zakiji dadin jikinki Kinga ma ban yi girki ba dan bansani ba ko Zan girka abinda bakya so nace bari ki dawo ki dafa abinda kikeso da kanki" "Toh Aunty ngd bari na watsa ruwan" Ta bude d'akin tsakar gidan ta shige. Na koma Palo na zauna na kunna tv na kai tashar Bollywood Ina cikin kallon aka Kara buga kofa naje na bud'e almajirin mmn Iman ne da kula a hannunsa. Karbe kular nayi nace ya mata godiya na koma ciki. Ina bud'ewa naga danwake ne ya sha hadi har da dafaffen kwai gashi da manja tuni yawuna ya tsinke na je kitchen na wanko hannuna har Zan fara ci na ga dacewar yiwa ummi tayi kila tana cin Dan wake. Labulen d'akin na daga da sallama tana waya kasa kasa shigowata yasa ta katse wayar da sauri,nidai a idona Kamar akwai abinda ke damunta duk sai naji ba dadi a yanda na ganta. "Ummi dan wake aka aikomin dashi bansani ba ko kinaci nace bari na miki tayi" "Wlh aunty ban fiye san dan wake ba ngd sosai "Ummi kodai na kawo miki Panadol ki Sha ne"? "Aaa wlh aunty gajiya ce kawai da yunwa yanzu zan fito na dafa ko indomie ne" "Toh sai kin fito" Na juya na koma palo na zauna na fara cin danwake Ina korawa da exotic din mahfuz ya siyo mana jiya saura kiris na cinye duka sabida dadin daya min. Da sallama ta shigo palon na amsa Ina kallon doguwar rigar da ta saka Mai balain kyau yellow ta yafa mayafinsa. "Bari na dafa indomie Aunty" "Akwai komai mai kike bukata a kitchen din" Ta amsa da toh ta shige na cigaba da kallona Ina hararo doguwar rigarta a jikina yamin kyau inama Ina da kudi na siyi irinsa Ina Kuma mamakin Inda ta ajiye hijabin nata,ko saka hijabin dama na bakunta ne. Ta dan jima a Kitchen din kafin ta fito da plate a hannunta sai pure water da ta d'auko da daya hannun har zata wuce nace "kiyi zamanki anan Mana kici kya shige daki ke kadai ki zauna" Murmushi tayi ta dawo ta zauna a kasan kafet ta tankwashe kafafunta ta dago tana "Aunty kizo muci" "Kai cikina a cike yake wlh" Na saci kallon indomie da ke ta zuba kamshin sardine lailai da alama ummi Yar hutu ce da mahfuz bai siyo kifin ba da kila sai dai ta siyo kifin da kudinta,a Raina na ayyana kila ta d'auka haka muke da kayan a ajiye. Tana cin abinci lokaci lokaci muna hada Ido sai muyi wa juna murmushi,bakina ma nauyi yamin a San na dau shawarar mmn Iman Kar na ringa zuba kamar yanda tace amma so nake kawai muyi Hirar. Sai data gama cinye indomie ta kai plate din kitchen ta dawo ta zauna. A daidai lokacin da wayata ta fara ringing ganin mahfuz ne yasa na d'auka cikin murmushi Ina "Abban mimina" "Madam na aiko yanzu zaa kawo kayan cikin" "Tom sai an kawo ya aikin" "Alhamdulillah Ina mimina"? "gata idonta biyu kaci abinci"? "Aa banci ba sai na dawo zanci abincin Mai numfashi da Mara numfashi tunda har Kika tsokano ni" "Lalala badani ba ban shirya yiwa Mimi kanwa ba" "Zaki shiryeni ki tanadeni mallama" Ya katse wayar na sauke wayar Ina dariya na kallo wajen da ummi ke zaune naga ta zuba min Ido muna hada Ido ta d'auke da sauri. Bance Mata komai ba na ajiye wayar nima Ina satar kallonta tana ta cizar yatsarta. Tuna ban gama Shan tsumin da mmn Iman ta kawomin ba yasa na m'ike naje kitchen na d'auko na dawo na zauna na bud'e ta dago ta kalleni ta sakar min murmushi Nima na sakar Mata na Kai gorar bakina. Wani daci naji ya gauraye min baki na furzar da tsumin da sauri Ina "Subhanallahi" "Lafiya kuwa Aunty"? Ban iya bata amsa ba na cigaba da goge bakina dan daci sosai. Sai da na gama nace "wlh daci ne da tsumin nan sosai ke kinji dacinsa" Bata ce komai ba tamin murmushi na fara mita Ina bari na gama aikina na Shiga gidan mmn Iman na fada Mata. Ba'a fi minti goma ba sai ga Wanda mahfuz ya aiko ya kawo kayan cikin. Ummi ce ta bud'e masa kofa ta Kuma karbo ta kawomin nace ta Kai kitchen karfe hudu zan shiga kitchen,Koda ta Kai banga ta fito ba sai buruntun ta kawai na ringaji a kitchen banaso nabi bayanta ta d'auka ko yarda ne banyi da ita ba hakane yasa na cigaba da Zama amma hankalina na kanta. Bayan Yan mintina sai gashi ta fito tana "tayaki dorawa nayi Aunty na dauraya kwanun da naci abinci dashi "Allah sarki na kuwa gode ummi" Har a raina naji dadi bata da san jiki Sam. Koda na Mik'e dan na Shiga kitchen din tashi tayi ta bini Ina tayi zamanta ba sai ta tayani ba amma ta dage sai ta tayani a dole na kyalleta muka yi fried rice na hada coslow. Ga ferfesun kayan cikin shima yayi dadi sosai. Sai da muka gyara kitchen din. Muka fito tayi tsakar gidan ni Kuma na fara hada ruwan da zanyi wa mimi wankan yamma. Tun jiya kamar jinin ya d'auke duk da Wasa yake min inaga anjima nayi wankan tsarkin

Table of Contents

Chapters

26 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26