Skip to content

Chapter 23

Chapter 23

Budurwar Mijina Book One Complete Hausa Novel 1,223 words 0 views Progress saved
Download Book

nayi mata godiya tare da kwashe kayan da dan bokitin cicicibin nayi hanyar kitchen dan a kitchen nake ajiyar irin kayan nan sabida wani zubin mahfuz akwai dube dube,Ina zuwa bakin k'ofa naji muryar ummi tana "Aunty ba abinda zan kama miki a kitchen din"? "Lah tuwone kawai zanyi ba abu Mai yawa ba inada Miya dama ngd ki saki jikinki dan Allah Nan ma gidane ki kunna tv kiyi kallo" Ina daga kitchen din nake Mata maganar na fara k'ok'arin tuka tuwon. Muryarta da naji a bakin k'ofa yasa na juya "Bari na Kama miki wani Abu aunty ki kawo na tuka miki" "Kai haba wlh ki barshi" Dak'yar.na samu ta koma Palon na tuke tuwon na kwashe. Na Kara gyara ciccibin da aka kawomin na dumama na juyo a plate na dauki tsumi daya da na zuba a fridge din kitchen na nufi palon. Tana zaune wanan Karin a saman kujera tana latsa wayarta har yanzu da hijabinta a jikinta har kasa. "Wai bakya Jin zafine ki cire hijabin naki ki Sha iska Mana dagani sai ke a gidan fa kin k'i sakin jikinki" Murmushi tayi bata ce komai ba na kwantar da mimi akan kujera na zauna a kasan kafet na mik'ar da kafafuna sabida naji dadin cin cicibin. Ban taba ci ba na dauka dadi ne dashi ai Ina kaiwa bakina naji daci daci na kwabe fuska Muka hada Ido da ita dama tunda zu Ina Jin idonta a kaina Dak'yar na hadiye Ina "Kai kinji daci kuwa da kina da Aure da kinci kinji" Murmushi ta sake yi wani zubin Ina da surutu na hau zuba "Kinsan mace sai da gyara idan baka dage kayi gyaran nan ba sai namiji ya fara k'ok'arin hango ta waje kuma idan mace ta haihu Salam take komawa dole sai ta zuba gyara sosai zata koma yanda take sai kinyi Aure zaki gane haka,Amma dai kin kusa shiga daga ciki ko"? "Eee" Washe baki nayi Ina "Masha Allah ansa Rana.kenan kice Muna da zuwa Lagos Shan biki dama ban taba zuwa ba Kinga ta silarki sai naje" "Insha Allahu" "Saura wata nawa"? "Saura wata uku" Masha Allah Allah ya nuna mana shima acan Lagos din yake"? "Eee acan yake" "Saurayine ko Mai Mata,kiyi hakuri Kinga Ina ta zuba miki tambayoyi" "Lah ba komai wlh Mai Mata ne" "Kash amma banji Miki Dadi ba auren mijin wata ai bashida wani dadi,ki more aure shine ki samu santalellen saurayi ki aura ku Sha soyayyar ku,kai amma na tausayawa wacce zakije ki tarar nasan tana nan zuciyarta kamar tayi bindiga kishiya ba dadi sam Allahu ya tsare mu da ita ya nisanci mazajen mu da tsinannun Yan matan Nan dake makale wa mazajen mutane,kiyi hakuri fa karki ce da ke nake wlh nima Ina da wata shegiya da ta makalewa mijina sai da nayi da gaske suka rabu matar saurayinki Allah ya bata hakuri da juriya kema dan Allah karki cutar da ita" "Aunty ai har yan matan baa san ransu suke auren mai Mata ba sai dan kawai ya tsago a kaddararsu nima saurayi naso aura Allah baiyi ba toh ya zakayi da kaddara" "Hakane Kam mudai Allah ya rabamu da mumunan kaddara" Ji nayi nama kasa cin ciccibin hararowa nake ni zaa kawo yarinya irin ummi,satar kallonta nayi Muka hada Ido,ta sakar min murmushi ta sunkuyar da Kai Ni kuwa ban d'auke idona ba na zuba Mata Ido,doguwa ce mai zagayyen fuskan hancinta nada tsayi gashin girarta yakusa hadewa waje daya,tana da dan.manyan ido,da karamin baki,bata fiye duhu ba bata fiye haske ba,duk da banga kalar jikin nata ba,daga zaunen da take Ina iya hango tudun kirjinta indai ba ciko tayi ba tana da na fulani manya kiris ya rage ta shiga sahun masu kib'a indai kishiyar tata ba mai balain zafi bace lailai wanan zatayi saurin kwace shi,badan tace an sa Mata rana ba da gidanmu Zan kaita wlh bazan bari ma mahfuz ya ganta ba na ayyana a raina. Kiraye kirayen sallah magriba yayi daidai da tsayuwar machine d'in mahfuz a k'ofar gida. "Aikuwa ga maigidan ya dawo" Mik'ewa tayi da sauri nace "A Ina zakije ki koma ki zauna idan ya shigo ku gaisa" Komawa tayi ta zauna a kasan kafet ta sunkuyar da kanta sai Wasa take da zoben hannunta inasan yanda take da dan kunya. Shigowar mahfuz da sallama yasa na m'ike Ina "oyoyo Abban Mimi" Na karbe ledojin daya shigo dasu Ina ta mamakin ko dai kudi ya samu haka da yawa wanan uban leda haka. Wajen da Mimi ke kwance ya nufa bai ko kalli b'arin da ummi take ba ya d'auki mimi a daidai lokacin da ummi ta Masa sannu da zuwa sai a lokacin ya kalleta ya amsa ya d'auke idonsa daga kallonta a daidai lokacin da ta mik'e ta nufi daya d'akin sai dana tabbatar da ta shige ciki nace "itace wacce Abdul ya kawo bakuwar tamu" "Naganta takura Mana kawai yakeso yazo yayi dan rainin hankali" Kasa yayi da murya ya matso kusa dani yana "Wai kina nufin a wancan d'akin zata zauna"? "Emana da a Ina kakeso ta zauna"? "Lallai bakida hankali,ga dakinmu ga d'akin da take ciki kinsan kuwa duk motsin da akayi a daki ana jiyowa" "Kai jamaa toh Ina kakeso na kaita"? "D'akin tsakar gida amma zamanta anan ai da takura gaskiya" "Haba Mahfuz d'akin tsakar gida sai kace namiji taya zan sauketa a tsakar gida sai nake ganin kamar hakan bai dace ba ko Abdul ne yazo gidanan yaga na ajiyeta a tsakar gida zaiji ba dadi wlh" "Wlh ba abinda ya shafeni nida gidana baza'a a zo a takura min ba a d'akin tsakar gida zata zauna na gama magana" Ya fara k'ok'arin mik'ewa yanda ya had'e rai.yasa ban Kara magana ba na fara bude ledojin daya shigo dasu,gwanwanin Madara ne dasu bournvita har dasu cornflakes, siyayya sosai har dasu kifin gwangwani da balangu bredi mai yanka yanka mamaki yasa nace "A ina ka samo kudi haka mahfuz" "Wlh wani kudi yau aka raba Mana shine nayo Mana siyayya" Tunda na aure shi bai tab'a yo Mana irin wanan siyayyan ba, shiyasa mamaki rufeni farinciki Kuma ya gaza b'oyuwa a fuskata,dan dama ni mayyar cornflakes ce dan sacet nake siyowa "Yeee nima na faso gari mun zama yan gayu Kai wanan bakuwar ta zo da goshi" Bai kulani ba ya nufi daki Yana bari yaje yayi alwala Cikin farinciki na kwashi kayan na Kai kitchen na hau jerawa a dan glass din dake kitchen din har dasu bama ya siyo Mana na kuwa ji dadi sosai. Sai da na gama jerawa na dauki balangun na juye a plate na dibar wa ummi na saka mata tuwo mulmule biyu da Miya na dauki karamin exotic na hada a faranti gabad'aya na Kai Mata har daki a kwance na tarar da ita da alama daga wanka ta fito dan jikinta da lema ta saka karamin t shirt da bakin dogon skirt,sai da gabana ya Fadi dana ga surarta take na karbi shawarar mahfuz na in maidata d'akin tsakar gida tab. Tana ganina ta rarumo hijabi tasa ta tareni tare da karbar farantin hannuna tana "Sannu Aunty" "Yauwa nace Mata cikin murmushi Ina ga abincin ki

Table of Contents

Chapters

26 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26