Skip to content

Chapter 21

Chapter 21

Budurwar Mijina Book One Complete Hausa Novel 1,216 words 0 views Progress saved
Download Book

amma ban shirya daukan wani cikin ba banaso mahfuz ya tabani har sai nayi tsarin iyali. Ban Kara Jin motsinta ba har nima nayi wankar yau shigar kananan Kaya nake ji. Hakane yasa nasaka Riga da wando maroun yayi balain min kyau banida wani tsayin gashi sai cika na gyara gashin nayi parking na Kara gyara ko'ina na turara jikina da turare na kame a Palo. Kamar zan leka ummin Kuma na fasa dan bana so na Kuma ringa shige Mata tunda nice matar gidan. Gab da magriba mahfuz ya dawo. Sai daya shigo har palon naje na rungume shi dak'yar na kwace bakina daga nasa nayi baya yayo kaina Yana "Baki Isa bafa Ina zaune Kika tsokano ni" Dariya na ringa yi sabida zagaye kujerun Palon mukayi tayi,dana ga ya kusa kamani na fita waje da gudu a daidai lokacin daya damkoni jikinsa Yana "Wa na Kama" Karar faduwar bokitin da muka ji yasa mukayi firgigit muka kallo wajen da muka ji karar Ummi ce a tsaye ta sunkuyar da Kai jikinta na dan rawa da alama ruwa zata Kai bandakin rigar dazu ce dai a jikinta bata cire ba. Mahfuz cikani yayi da sauri ya koma ciki. Na nufi wajen ummi Ina "garin yaya bokitin ya Fadi" Bata dago ba tace "wlh subuce min yayi" "Gashi rigar taki kuwa ta jike" "Ee dama wanka zanyi Bari na canzo ta dago ta kalleni. Yanda take kallona daga sama har kasa yasa nace "Yadai" "Kinyi kyau sosai Aunty" Cikin murmushi nace "Kina san fasa min Kai ummi jeki yi wankanki bari nayi sallah Nima. Na juya na shige palon na barta a tsaye tana kallona Nima ko bata fadamin ba nasan nayi kyau inaso ace min nayi kyau Dadi nakeji, idan har mace Yar uwata zata ce nayi kyau inaga mijina. Ina shiga d'akin mahfuz ya fito daga bandaki ya canza kayan jikinsa zuwa jallabiya ruwan kasa Mai zip a gaba. Ya dau carbinsa yayi waje. Bai dawo cikin gidan ba sai da aka iddar da Sallah Isha Yana shigowa na jera Mana abinci a tsakiyar kafet na zubawa ummi na dora Mata akan karamin farantin na d'auka na Kai Mata har daki. Koda na Shiga akan katifa na ganta a zaune ta saka wani vest ja Rabin na fulaninta a waje sai dogon wando. Da murmushi na ajiye abincin Ina "gashi nan" "Tace ngd Aunty" Nayi waje Ina fatan ba abinda zai sake fito da ita,dan sam.bangane Mata ba jiya wuni tayi tana saka hijabi yau Kuma ba hijabin dan ma naga.mahfuz ko kallonta bayayi abinda ya kwantar min da hankali kenan" Koda na koma Palo hankali kwance muka ci abincin mu muna tab'a hira Inda nake ce Masa jibi zanje kitson sallah da kunshi sabida bazan iya bin layi ba,yace Allah ya kaimu ya bani kudin. Karfe goma naji na fara Jin bacci nikam bansan Mai yasa yanzu nake da saurin Jin bacci ba. Ina mik'ewa shima ya mik'e ya d'aukar min Mimi muka Shige daki. Ban bari yayi komai ba sai dabaru da na Masa Nima yamin muka samu nutsuwa dan ce Masa nayi ya bari nayi allura tukunna. A tare mukayi wanka na dauka zai kwanta ne yacemin Palo zaije yayi kallon ball baya Jin bacci. Sama sama ma naji shi dan baccin ne a kaina sosai. Bansan lokacin daya shigo ba. Washegari ma ummi ce ta tayani sharan tayi mopping Ni Kuma na hada mana breakfast mahfuz yaci ya tafi. Itama Tara nayi ta fice na shiga gidan mmn Iman muka yi ta hira anan nake fada mata a cikin tsumin da ta kawomin akwai mai balain daci,tace tana ganin ba tsumin na Sha ba dan duk tsumin ba mai daci ko kad'an nayita mamaki tace na gwada sauran ragowar naji ko da daci sai da na koma gida na dauko mata ta dandana tayi ta mamaki tana ta sha irinsa ba daci ko daya,ban bar gidanta ba sai karfe biyu na koma gida a daidai lokacin. Da ummi ta dawo wanan karon ma ita ta Shiga kitchen ta samawa kanta abu taci. Ta tayani wanke wanke,girkin yau ma ta dage min ita zatayi yanda ta dage yasa na kyalleta tayi girkin. Yau dai ita take Jin hirar hakane yasa nima na biyeta dan nikam inaso naga muna Hira. Yau ma bata saka hijabin ba Kamar na tambayeta na Kuma share. Sai cewa take na iya wanka zata Zo wajena d'aukar course idan auren ya kusa muna burgeta nida mahfuz Tuni na washe baki nace insha Allahu duk zan bata sirrin zamantakewa na aure,na bata labarin irin soyayya da muka zuba da mahfuz kafin muyi aure,kamar zan bata.labarin tsinaniyar yarinya nan data makalewa mijina da irin hawan jinin da ta so doramin na Kuma fasa. Itama ta bani labarin yanda saurayinta ke Santa akanta har fada yake da matarsa. Anan na nuna mata rashin Jin dadina akan bai dace saurayinta yayi haka ba dan itama zai iya mata haka idan ya aureta idan giyar so na kwasar sa yanzu ta ringa Dora shi akan hanya. Godiya tamin wajen shidda ta mike ta tafi d'akin nima na dau mimi dan yau bamuyi wanka da wuri ba. Haka kawai sai na fara gaskata mmn Iman akan bata yarda da ummi ba,dan sau biyu Ina Kamata kamar hararata take idan taga na ganta sai ta wayance da sosa Ido,yau bansan inda mahfuz ya tsaya ba,bai dawo kafin magriba kamar yanda ya Saba ba. Koda na iddar da magriba ban fito daga d'aki ba dan so nake idan akayi isha sai na fito gabad'aya kafin dai ayi sallah Isha na tashi Ina dan gyara kayana dana hargitso. Sallamar ummi da shigowarta har tsakiyar dakina yasa nayi saurin juyawa Ina kallonta. "Tun dazu ake ta kiranki aunty ganin baki fito ba yasa nace bari na kawo miki" Sam banji dadin shigo min d'akin da tayi tana kalle kalle ba hakane yasa na karbe wayar a hannunta fuskata a had'e nace Mata na gode ta juya ta fice tana karewa dakina kallo kamar na bita na gaura mata mari wlh na tsani a shigo min dakina Da alama fuska biyu ne da yarinya nan,dole kuwa na taka Mata birki bana san iskanci dan ko a yanzu ma ba hijabi a jikinta riga da skirt tasa taci kwalliya kenan ma a palona ta zauna da Mahfuz ya shigo ya ganta fa Take naji raina ya b'aci na dauki Mimi nayi hanyar palo. A kasan kafet naganta a zaune tana kallo mugun hade rai nayi dan naga alamar na sake Mata da yawa. Sau daya ta dago ta kalleni tana "kinfito ne Aunty" "Um"kawai nace mata Karar machine d'in mahfuz da naji a waje yasa na kalleta naga ko zata tashi amma Ina zamanta tayi ba alamar zata tashi. "Ko zaki koma ciki ga Abban Mimi ya dawo" Nace fuskata a had'e. Mik'ewa tayi bata ce min komai ba ta fita waje naja tsaki ta juyo ta kalleni ta Kara d'auke kanta ta fice a daidai lokacin da Mahfuz ya shigo na mike da sauri dan nasan ma ya ganta shegiya kawai naji na auna Mata zagi Daga labule Ina kallonsa bai kalleta ba har ya shigo Yanda yaga raina a had'e yasa

Table of Contents

Chapters

26 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26