Skip to content

Chapter 10

Chapter 10

Budurwar Mijina Book One Complete Hausa Novel 1,218 words 0 views Progress saved
Download Book

rage ji dani. Idan na ce masa nayi muni dariya yakemin yace shi bai gani ba ai cikin nan yasa kirjina ya ciciko,bamu tab'a fushi da juna ba,bamu taba sa'insa ba,bai tab'a gaya min bak'ar magana ba sai gashi wata Yar iska tana neman juyar min da kwakwalwar miji bansan adadin tsinuwar da nayiwa macen da ta Kira shi ba. Gajiya nayi da tsayuwa agaban mudubin na koma Kan gado na kwanta Ina sak'e sak'en yanda zan biyowa mahfuz ni nasan idan ya dawo dole ya bani hakuri dan baya iya dogon fushi dani dole na nuna Masa bacin raina na Kuma jawo shi jikina na binciki wayarsa nayi blocking din Yar iskar yarinya da take kiransa,da Wanan tunanin na samu nayi wanka abincin ma da kyar naci sabida b'acin rai,sai duba wayata nake naga ko zai kirani ko zaimin text,har watsapp na hau naga ko ya ajiyemin sako duk shiru,hakan kuwa ya Kara saka min Jin haushinsa na tanadi masifar da zan Masa idan ya dawo. Kamar bazan yi girkin dare ba na daure na dafa jollof din shinkafa na hada Masa zobo. Nayi kwalliya kamar yanda na Saba na zauna zaman jiransa raina a had'e. Mahfuz bai dawo gidan ba sai goma da rabi na dare Ina Jin sa ya shigo da machine dinsa. Ciki ciki yayi sallamar ya hade rai da leda a hannunsa bai Kuma Kalli inda nake ba. Baki sake nabi shi da kallo har ya shige daki mamaki da bakin cikin halin ko inkular da ya nuna min ya rufeni,Mai mahfuz yake nufi dani yamin laifi ya nade tabarma da kunya a zuciye na tashi zan bishi har d'akin. Kafin na isa d'akin na tsaya Ina bin umarnin zuciyata dana watsar dashi zai nemeni da kansa. Da wanan tunanin na nufi daya d'akin da idan ba baki muka yi ba ba Mai kwana a ciki. Nan na shige zuciyata na balain tafasa Duk abinda nayi dan na samu zuciyata tayi sanyi duk a banza kofa kawai nake kallo ko zanga shigowarsa yazo bani hakuri ga yunwa da nakeji amma bana jin cin abincin. Watsapp na hau sabida na samu nayi hira da Yan uwana da muke grp daya ko zan samu na rage bakin ciki dake Raina sai dai Ina hawa na duba mahfuz naga Yana online,wato ba abinda ya dame shi ni nasan da Yar iskar yarinya yake hira. Ban iya hakuri ba na rubuta "Mahfuz yanzu nice abar wulakantawa a wajenka ko,"? Bai bud'e sakon da wuri ba na fara k'ok'arin Kara rubutu naga ya bude ya turo "hmmmmm" Bakin cikin bazai iya bani hakuri ko ya biyoni daki ba yasa na kashe data na wurgar da wayar, Idona akan agogo har karfe daya na dare sai juyi nake ba alamar bacci zai daukeni sai tunani daya cike min zuciya tunda mukayi Aure bamu taba raba shimfida da mahfuz ba sai gashi a sanadin haduwa da wata nayi fushi dashi bai ma kalleni ba. Hawaye kawai ke zubomin Ina tsinewa macen da ke san Shiga tsakanina da mahfuz har ta samu matsayi haka a wajen mahfuz da zai k'i nemana a kanta sai da cikina ya tsufa mahfuz ya fara daga min kafa amma ko yayane sai ya nemeni ko period nake sai na Masa dabaru har hirar na tab'a yi da wata aminiyata take cemin namijin da baya iya daga ma kafa ba karamin gamsar dashi ake ba. Amma mahfuz yamin laifi akan Ina kishinsa bai iya bani hakuri ba,nifa yayi wa laifin nan amma shine ya kasa bani hakuri. Har tunani na Kara yi a tsanake dan naga ko dai zaginsa nayi cikin fushi batare da nasani ba sai dai banda karya tashi da nayi na zagi tsinaniyar da ta kira ban Masa komai ba. Zuciyata raya min kawai yake akan naje d'akin na sameshi wani b'ari na zuciyata na hanani akan shi yamin laifi shi ya Kamata ya nemeni. Haka na kwanta zuciyata kamar tayi bindiga dan bakin ciki sai biyu da wajen rabi na dare bacci yayi awon gaba dani. Ban tashi bude Idona ba sai wajen bakwai da minti goma Sha biyar. Na Mik'e da sauri Ina sallati na tsani naga sallah asuba ta kubcemin. Da balain sauri na fada bandakin na daura alwala na fito. Sai dai banida hijabi a dakin bana san zuwa dakina naga mahfuz sai dai ya zama dole tunda ba hijabi a d'akin. Fuskata a had'e na nufi dakina a hankali na tura k'ofar na shiga. Bangan shi a dakin ba na dai jiyo motsinsa a bandakin da alama wanka yake. A madadin na d'auko hijabi na wajen da na hango wayar sa a saman bedside drawer na nufa da sauri na dauki wayarsa na fita daga dakin na koma daya d'akin na saka key na zauna a saman gado hannuna sai rawa yake. Ko da na bud'e wayar ajiyar zuciya na sauke da naga ba password. Message dinsa na fara shiga SR da na gani ta turo message da bai bud'e ba yasa na bud'e message din jikina na balain rawa Message ta turo.masa wajen biyar na asuba da alama reply ta Masa "Kayi hakuri sugar banga kiranka ba sai yanzu kasan jiya ban kwanta da wuri ba how was your night my love zaka biyo d'in I missed you" Hannuna rawa kawai yake kirjina Kamar ya fado ji nake ma dakin na juya min "Lubna ki bud'e min k'ofar nan sabida Mai zaki zo ki dauki wayata?Wai me yake damunki ne" Najiyo mahfuz a bakin k'ofa Yana jijjiga k'ofar. Rawar da jikina keyi yasa ban ma iya mik'ewa ba na nemo lambar SR na fara kiranta a wayarsa bugu daya ta d'auka murya can kasa tace "Sugar ka iso ne"? "Kutumar bura ubanki tsinanniya ya iso wajen ubanki shegiya laananiya" Kit naji ta kashe wayar na Kara kiranta bata d'auka ba,ban hakura ba na cigaba da kiranta Mahfuz kuwa sai jijjiga kofa yake Yana kwalla min Kira akan nazo na bud'e k'ofar na bashi wayarsa Ganin tak'i d'aukar wayata yasa na m'ike jikina na rawa naje na bud'e k'ofar mahfuz ya fado dakin da sauri ya fusge wayarsa daga hannuna idonsa ya Kada yayi jajjur cikin k'ak'ausar murya yace "Daga yau karki Kara tab'a min waya lubna wlh Kika Kara sai ranki ya b'aci kinji na fada miki" Ya fara k'ok'arin juyawa ya bar dakin na Sha gabansa da sauri hawaye na zubomin "mahfuz mai na maka da na cancanci haka daga wajen ka?Mahfuz jiya baka san a ya na kwana ba amma ka kira wacce ba matarka ba dan kaji lafiyarta Kuma har zaka biya ka ganta kafin kaje wajen aiki, Mahfuz Kaine kamin laifi Ina gefenka ka fita Palo dan kayi waya da mace dan na tambayeka da wa kake waya ka rufeni da fada ka kirani wawiya mara hankali laifine dan nayi kishin ka har yaushe muka yi auren da zaka min haka?Ina duk alkawarikan da kayi min a baya Koda zaka kula mace mahfuz bazaka kwantar min da hankali ko dan cikin jikina ba? kayimin adalci kenan"? Na karashe hawaye na zubomin "Lubna kina da matsala shikenan dan kinji.ina waya da mace sai ta zama budurwa ta,kinsan ya muke da ita da zaki zageta ne?wajen aikinmu

Table of Contents

Chapters

26 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26