Chapter 19
Chapter 19
fatattakar kowani irin sanyi duk fitinarshi d izinin ubangiji seyabarki, Munada magungunan mata masu matuqar kyau,hadaddu gangariya kizama t gaban goshi,komi kikace oga yace don, 馃グ kikerewa sa'o'i, kizama abun riritawa abun tarairaya a kudi qalilan,karki cuci kanki kizauna kina cewa ayni nasan kaina,a inadin? Wallahi ko kanada kyau qara d wanka Kisha kiyi qattt kigigita oga, Munada tsumi nau'i nau'i Gumba ta madara,ridi,gyada,dabino,kwakwa,dasauransu Akway ruwan jaraba Ruwan Dadi Hadin minannas Hadin dafa kaza(manta uwa) Hadin yar gaban goshi, Turarukan mallaka. Duk a farashi mesauqi. Serious buyers call, WhatsApp 07046881166 Senajiku kusiya kuyi godiya Kuma kumin addua鉂わ笍nagode [6/29, 7:54 AM] Khadija Candy: *BUDURWAR MIJINA* *NA SADNAF* *E.W.F.* *PAID BOOK* *LAST FREE PAGE* *PAGE 10* Ina bud'e kofa na yamutsa fuska Ina "Shi bawa bazaa barsa ya huta ba" "Eee baza'a barki ki huta ba wuce muje" Dariya nasa dan muna Yar Wasa da mmn Iman sosai muna Shiga ciki ta zauna a dogon kujera tana kalle kalle nima na zauna a kujera mai kallonta Ina "kefa wani zubin kanki ba dadi Mai kike dubawa ne" "Mai nake dubawa kuwa so nake na tabbatar da ba kowa a gidan kafin nayi magana duk da Naga fitar mahfuz da bakuwarki" " Ba kowa dagani sai Mimi kin samo mai zafi kenan"? Nace Ina maida hankalina gabadaya kanta dan Naga alamar da magana tazo Mai mahimmanci "Eee da magana nazo Kam amma nariga da nasan halinki gajen hakuri baki iya bin komai a hankali ba" Mik'ewa nayi da sauri na koma gefenta na zauna Ina "Mai ya faru mmn Iman bani labari" "Wai ya kuke da bakuwar nan da tazo jiya"? Yamutsa fuska nayi Ina "Wai Ummi"? "Eee" "Ba dangi iya babu na baba Ina Abokin Mahfuz Abdul da nake dan baki labarinsa Yana yawan yi Mana aike har kike cewa idan kina da kanwa da kin bashi" "Eee na tuna shi" "Toh yarinyar yayarsa ce suna zaune a Lagos tazo nan wani program ne na sati daya ko kwana goma yace ne jiya dai da kansa ya kawota,lafiya kuwa kike tambayeni"? Ajiyar zuciya ta sauke tana "Ni yarinya Sam ban yarda da ita bane naga tana ta Abu kamar mara gaskiya,kinsan jiya nan Ina zaune wlh satar kallonta kawai nake ni a idona ma sai naga kamar kallon banza take miki kasa kasa" Dariya na kwashe dashi Ina "Kai mmn Iman abin naki har da sharri yarinya da ko kallona bata iya yi ga kunya" "Kefa dadina dake hauka wlh Ina miki maganar serious shi Abdul din duk wayanda ya sani anan ga gidansu mahfuz Mai yasa bazai kaita can ba sai nan, Taya zaa kawo Miki tsalleliyar budurwa irin wanan haba mana" "Wani kusancin ai yafi wani mmn Iman shiyasa ya kawota nan Allah sarki kawata tsoro kike zaa kwace mun miji ko" Na kyalkyale da dariya mmn Iman ta zuba tagumi tana kallona "Kwantar da hankalinki ba Mai kwace min miji mahfuz Zan iya rantse Miki ba lailai yasan kamaninta ba dan ko kallonta bayayi,itama ba lailai tasan kamaninsa ba dan tana ganinsa take sunkuyar da Kai" "Tom ai shikenan amma nidai ban yarda da ita ba wlh masu shiru shiru da saka hijabin nan wlh munafikai ne,a idona jiya ta Miki kallon banza ke Kuma ga saurin sakin jikin balai name kike wani janta da hira" "Kai mmn Iman bakonka annabinka so kike na hade rai,nifa kinsan ban iya wulakanci ba" Mmn Iman shiru tayi dan ba iya maganar da ya shigo da ita kenan ba,jiya taji mahfuz nata waya a k'ofar gidan ta har makalewa tayi a jikin kofa dan taji Mai yake cewa soyayya yake zubawa a waya da wata taso ta fadawa lubna ta saka mishi ido amma tuna haukar data Mata kwanaki yasa ta hakura" Maganar lubna ya katse Mata tunanin da take "Mmn Iman mun zama yan gayu fa jiya Kinga siyayyar da Mahfuz yayo Mana kuwa zomuje kitchen kigani" Na jawo hannunta mukayi kitchen din Ina bata labarin abubuwan da mahfuz ya siyo Mana jiya. A bakin kitchen ta tsaya na hau nuna Mata ta ringa gyada Kai dan ita dama mijinta na siyo mata nice dai bakuwa da aka siyomin a Karon farko. "Aaa lailai kam kun zama Yan gayu kin huta da siyan kanana Yan sachet nidai ko dan bakuwar aka muku siyayya haka sabida Kar ta Raina ku"? "Ko daya fa tazo dai a daidai ne wani kudi suka samu yayi Mana siyayyan,dazun Nan yake cemin ya bada kudin ragon layya,yau saura kwana biyar fa Mai da me ya Kamata muyi? "Mai kuwa zamuyi daya wuce ayi yanka mu soya ban karya ba mallama zubo Mana dankalin muci" Ta koma Palon na juyo dankalin a plate da kwai flask din tea din na Palo da bredi Muka fara ci "Kiringa Jan class dinki lubna ki daina sakar wa wanan bakuwar taki fuska kina zuba a gabanta haba jiya kin bani haushi wlh banda kin dage da a shawarce kin yiwa mahfuz magana ta koma gidansu wlh tunda akwai Yan mata acan itama sai tafi sakewa" Mmn Iman nifa haka nake wlh ba sakin baki ne dani ba,ni ban iya wulakanci ba Sam,idan taga bana Mata magana ko bana Mata hira ai sai taga dan tazo gidana cin arzikine kinsan Kuma haka ba dadi" "Hakane Kuma toh ki ringa ragewa" Insha Allahu Koda muka ci abinci hirar muka cigaba da yi ta tayani yiwa Mimi wanka kafin ta tafi. Tana tafiya Nima nayi wanka Yau kwalliya da soyaya nake ji dan dazu mahfuz yamin kyau. Kwalliya naci da sabuwar atamfa a irin dinkin da mummy tamin dark purple ce da zanen yellow ta balain yimin kyau,ni kaina na kasa d'auke idona daga Kan mudubin. Shayar wa da nake yasa kirjina ya ciciko ya fito har ta saman rigar dinkin yamun das a ciki,banida burin daya wuce mahfuz yaga kwalliyar nan. Mimi itama purple din kayan kanti na saka Mata wayata na dauko na kira mahfuz a waya bugu daya ya d'auka Yana "Madam yanzu nake Shirin kiranki naji lafiyarku" Wal nayi ido kamar yana gabana nace "idan ba abinda kake yi ka kunna data muyi video call" "Angama" Ya katse wayar Ina kunna data kiransa na shigowa Ina dagawa na sakar Masa murmushi tare da bankaro kirjina Ido ya zuba min sai daya dade baiyi magana ba kafin yace "hmm kin kirani ne dan kawai ki tsokane ni ko?, zan kamaki ne ai" Yace Yana tauna lebbe na Masa gwallo "Ina bakace nayi kyau ba"? "Sai na dawo zakisan kinyi kyau ko bakiyi kyau ba ke kadai ce a gidan"? "Eee wlh ni kadai ce ummi bata dawo ba so nake ma yanzu na tashi na dora abincin rana sabida ita amma idan tani ne cornflaskes Zan Sha" Tab'e baki yayi bai ce komai ba nace "Ko na dafa har da Kai na Aiko maka dashi"? "No ba sai kinyi dani ba karki wahalar da kanki abincin ranar ma karki wahalar da kanki wani dafa Mata idan ta dawo kice ta Shiga kitchen din ta dafa abinda take so da kanta ba yanda zaayi wata gardiya tazo ta samin mata wahala" Abu kad'an ke Sakani dariya gardiyar da yace yasa nayi ta dariya har cikina na neman kullewa ganin zai kashe
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26