Chapter 11
Chapter 11
daya da ita kuma ba komai a tsakanina da ita sai Yar tsokana amma sabida balai kin dorawa kanki kishi,har kina Neman zagina,wane bayani kikeso na miki? Mamakin maganar sa ya sa na kasa motsawa na zuba Masa Ido har ni zai cewa ba budurwarsa bace shi kuwa ganin ban magana ba yace "ba wani abu a tsakanina da ita ke kikesan ki dorawa kanki abinda ba haka ba,abinda yasa jiya ban waiwayeki ba naji Haushin karyatani da kikayi bai dace na miki magana ki karyatani ba har kina neman zagina kina nufin baki yarda dani ba kenan,nidai zanje wajen aikii dan na makara daga haka ya ratsa ta gefena nabishi da ido har ya shige ko minti biyar baiyi ba ya fito daga d'akin ganin Ina hawaye Ina Kuma tsaye ban motsa ba ya iso wajen da nake tsaye yana "Kina nan a matsayin da Kika sanki a zuciyata ba Wanda ya Isa ya kwaceni a wajenki gwara ki kwantar da hankalinki daga haka ya sunkuyo yamin kiss a kumatu ya juya Yana "Sai na dawo" Lumshe idona nayi Dana shaki kamshin turarensa kukan da nake dannewa ya kwacemin har ga Allah ni nasan Mahfuz soyayya yake yi da wata amma yake San raina min hankali Ina balain San mijina dama yarinya nan ta barni da mijina ta nemo wani nayi nadama da ban dauki lambarta a wayarsa ba. Ban tab'a tunanin mahfuz zaimin haka ba A daddafe nayi Sallah na dumama abincin da mahfuz baici ba naci dan yunwa nakeji. Sai da na gyara ko'ina nayi wanka na zauna Ina tunanin hanyar da zan bi na raba mijina da SR dinan da take neman d'auke min hankalin Miji. Kiran aminiyata farinciki rayuwata abokiyar sirrina ce ta katse min tunanin da nake mahaifiyata banida wacce tafita duk duniyar nan ba abinda nake boye mata a haka na taso sabida yanda take jana a jikinta ba Kuma Ni kadai ba haka duk kannena,koda na tashi aure ajiye kunya tayi a gefe ta karantar dani rayuwar aure da yanda zan kula da mijina. Mahaifiyata a waye take dan nurse ce bama na iya boye mata komai. Ina sallama na hau gaisheta bata amsa ba tace "Mai yake damunki Lubna"? Kamar Mai jiran kiris na fashe mata da kuka. Sai da naci kuka na na koshi bata hanani ba ba ta kashe wayar ta ba Jin na tsagaita tace "Ina jinki lubna mai yake faruwa" Tiryan tiryan na kwashe komai na gaya mata ba abinda na cire har yanda mukayi da Sr din da bansan sunanta ba sai da na gama tsaf ta sauke ajiyar zuciya tana "Wlh bansan bakida wayo da tunani ba sai yau,Lubna waye ya gaya miki ana yiwa namiji haka,waye ya gaya miki ana fada da budurwa Miji a waje,salon ki jawowa kanki raini,daga lokacin da Kika d'auko wanan hanyar kin kashe kanki da kanki ai komai dan wayo ne da dabara wlh na raina wa wayon ki Lubna,ai kiyi fushi da mijinki ko kiyi gaba dashi dan kin gano Yana da budurwa ba shine mafita ba dan kin nisanta kanki daga wajensa ne kin kusanta shi da budurwar tasa dan su maza haka suke Abu kad'an ka d'auke musu hankali,daga lokacin da Kika fara wanan haukar fita zaki nayi a zuciyarsa ya fara ganin aibunki,waccen kuwa dama burinta ta samu ta kwace shi, karki sake wanan gangancin yanzu damara zaki daura ki jawo mijinki jikinki cikin kirsa ki rabashi da wancan yarinya cikin ruwan sanyi,ki rubanya kyautatawarki a gare shi. Ai ke mijinki ma Yana shakarki tunda a boye yake Mata waya kinsan akwai mazan da agaban matansu zasu yi wayar sai dai ta hadiyi zuciya ta mutu. Ki nesanta kanki da tab'a wayarsa ko da Kinga an turo masa text an Kira karki sake ki nuna Masa kingani cikin salo zaki rabashi da ita, kiringa kai zuciyarki nesa kishi hauka yake sawa da tarin nadama, kifita a zuciyarsa yaji ma gwara yayi auren kawai tunda kin k'i ki kwantar masa da hankali,ba dai text take tura masa ba kema sai ki dage wajen tura masa,Yana fita ki kirasa kiji lafiyarsa sau uku kafin ya dawo anan zaki ga hankalinsa ya fara rabuwa gida biyu har kiyi nasarar dauke masa hankali akan wacce yarinya ki fito da salo salo na soyayya da bai sanki dashi ba kiga ikon Allah" Sai da muka shafe awa daya mahaifiyata na bani shawara na Kuma ji dadin shawarawarin da ta bani duk da ba k'aramin dauriya zanyi ba dan Ina da tsananin kishi bana iya controlling kaina idan ya motsa min. Koda muka gama waya wacce take min lalle na Kira akan tazo tamin na Sha damara dawo da hankalin mahfuz kaina insha Allahu sai na raba shi da SR dinan MAHFUZ Allah Allah yake ya isa gidansu Hadeeza dan ya bata hakuri tunda ya fito daga gida yake kiranta a waya taki d'aukar wayarsa. Koda ya iso k'ofar gidansu ya cigaba da kiranta a waya bata dauka ba sai da ya mata text akan ya iso Yana waje ta fito Yana jiranta. Sai da aka kwashi mintuna wajen goma Kafin ya fara shako kamshin turarenta daya saka shi lumshe Ido ya bud'e Idonsa a hankali ya zuba Mata tana daga bakin k'ofa a tsaye ta harde hannayenta a kirjinta ta had'e Rai...... *mg's skincare* Shin Ina matan suke馃棧锔忦煑o笍馃棧锔弇aza kuhanzarta kumatso kusa kuma kubani aran kunnuwanku domin sanin albishir dawannan shahararran company yazo muku dashi馃槂馃ぉ Hakika tabbas duk macen data amsa sunanta bazataso afita b Koda da kwayar zarra domin hakane wannan shahararren company yazomuku da ingantattun hadaddun kayan gyaran jiki masu matukar gyara fata cikin kankanin lokaci batare da sunyima fata lahani ba domin kayan mg's organic products ne bawai na bleaching ba zasu gyara ma mutum fatane yafiddomashi da ainihin natural beauty din mutum馃憣hakika duk wacce batayi anfani da kayan mg's b anbarta acan karshen bayama kuwa domin Koda sabulunsu kadai kuka dana fatanku seya fita dasauran mata ballentana Kuma kuyi anfani da gbdy beauty kit dinsu wohoho wani abun baa mgn sewanda yajaraba shine zai tabbatar鉂o笍 Shin kinafama da Pimples, black spot,sunburn, stretch mark,acne,black head, wrinkles,knuckles dama duk wani matsalan fata? Shin fatanki tana tattarewane ko kinshafa cream yabatamiki jiki馃槴 Shin inamasu cewa sunjaraba Basu dace b bi'iznillah sister's duk Wanda yayi using mg's sai godiya domin Koda iya herbal whitening black soap din kikayi anfani dashi zakiga ynd fatanki zaiyi clear Yana walwali jikinki zeyi fresh kina glowing my dear bare Kuma ace set dinne gbdy 馃ga amare uk wnd yy using bridal set dinnan baya bukatar kowani gyaranjiki domin yadda jikinki zekoma yazarce misali DNT be left behind Bridal kit:18k Beauty kit:11k Student package:7k Herbal whitening soap:3k Chat 08062991549 07046881166 07067210195 Call 08064532391 Facebook: mg's skincare Instagram:glow_with_mgs Take note pls iya wadannan numbers dinne kawai zakusamu kyn mg's babushi akasuwa馃 Do you guys wanna achieve that milky skin that turns head wherever you go馃ぉ Then @mgs skincare gat you covered 馃挴 Now is time to glow馃槏 Pamper ur skin馃Φ Shine like bride馃懓馃徎鈥嶁檧 Glow馃鈥嶁檧锔� 馃挴 tested nd trusted馃 Guarantee Sannan muna da hadaddun frames masu kyau gamai bukata yayi mgn 07046881166 [6/29, 7:54 AM] Khadija Candy: *BUDURWAR MIJINA* *NA SADNAF* *E.W.F.* *PAID BOOK* *PAGE 6* Mahfuz duk
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26