Chapter 15
Chapter 15
Yaya dai cikinsa take dauke dashi kulawarsa tafi bukata yanzu. Gaisuwar zainab din da ta mik'e da sauri ya amsa,ta nufi d'akin bakin Ya zauna shima a tsakiyar kafet Yana neman kwayar idon lubnar da ta sunkuyar dakai tunda ya shigo bata daga kanta ta kallesa ba. "Uwar biyu fushin kike dani kenan"? Ko kallonsa banyi ba na janye kafata daya fara k'ok'arin d'anna min, ko ganinsa bana san yi dan na riga da nasan wajen dai budurwarsa yaje da ta fini mahimmanci,a yau ma da na dawo gidana sati biyu rabona dashi,ba dokin zuwana yake ba,ba nice a gabansa ba budurwarsa ce a gabansa,wlh a baya ko fita nayi haka zai ta jera min Kira Yana tambayar na dawo,bazai daina kirana ba har sai na dawo gida hankalinsa zai kwanta,ni nake tilasta masa ya fita ma,yayi ta mitar korarsa nake, soyayya muke yiwa juna mai wahalar fassaruwa,mahfuz yaji dani ya soni,sai gashi lokaci guda ya canza min duk wanan soyayyar Yana neman rushewa a gaban idona, tunanin da nayi yasa hawaye zubomin na share hawayen naji saukar hannunsa a kumatuna ya dago fuskata "Lubna dan Allah ki daina sawa kanki damuwa wlh tallahi Ina kaunarki kina nan da matsayin ki a zuciyata,ki cire komai a ranki ni mahfuz nakine ke kadai" "Mahfuz wlh idan har kana kaunata Kamar yanda kace bazaka so bacin raina ba mai na rage ka dashi dan Allah,dududu yaushe mukayi Aure da zaka fara kula wata mahfuz Ina alkawarikan da kayi min,ko shekara biyu mahfuz har yanzu bamu yi da Aure ba har wata ta d'auke maka hankali akaina baka iya bacci idan baka ji muryarta daddare ba,har abincinta yafi maka nawa dadi, haba Mahfuz a haka kace kana kaunata,sati biyu rabona dakai amma na dawo ko a jikinka ka fice sai yanzu zaka dawo?Mai na maka dana cancanci haka daga wajenka dan Allah"? Na karashe tare da fashewa da kuka ya jawoni da sauri ya rungumeni tunda na fara magana Naga ya kyab'e fuska da alama maganganu na sun shige shi sai bubuga bayana yake Yana bani hakuri na janye jikina daga nasa Ina"Mahfuz Dan Allah wacce ita? "Dan Allah kibar zancen nan" "Dan Allah ka fadamin wacce ita yaushe kuka hadu"? "Tsohuwar budurwa ta ce lubna mun dade da haduwa da ita,Allah ne yayi bantab'a baki labarinta ba dan har ga Allah a lokacin da na had'u dake na shafe babinta a rayuwata" "Mai yasa baka aureta ba Mai ya rabaku"? "Wai Dan Allah Mai ya kawo tambayoyin Nan lubna"? "So nake na san matsayinta a wajenka Mahfuz" "Allah baiyi munyi Aure ba lubna sai a yanzu kaddara ta sake hada mu" Shiru nayi ina jin wani irin abu ya tokare min makoshi bana jin ma zan iya maganar so nake na auna maganganun sa "Wlh Lubna ita ta dawo rayuwata ta nace min na rasa yanda Zan yakice ta" "Kana santa Mahfuz ni ba mahaukaciya bace wlh nacewa juna kukayi,ba itace ta nace maka ba,yanzu aurenta zakayi kenan"? Na zuba masa Ido gabana na faduwa "Lubna mu bar zancen nan kema ko yanzu aka ce miki zanyi Aure ai zaki karyata kin isheni rayuwa" "Na isheka rayuwa kake kula wata yaudarar ta kake ko watsewa kuke idan har ba aurenta zakayi ba Mai amfanin kulata ka b'ata mata lokaci mahfuz"? Lubna dan Allah ki bar zancen nan haba kiji da cikin Nan dake jikinki muyi addua Allah ya saukeki lafiya haba Ina ta kwantar Miki da hankali kin kara dagawa kanki hankali" Yace a d'an tsawace tare da mik'ewa tsaye "Ga abincin ka nan ko kaje wajenta kaci"? "Lubna dan Allah kidaina min maganar wata idan har kina san mu daidaita dake wai wane irin dabia Kika samo haka mara kyau ni nace miki naci abinci" 'toh zauna kaci abincin" Tsaki yayi ya zauna duk da a koshe yake ya bude flasks din ganin faten doya ne yasa ya zuba kad'an ya fara ci yanda ya had'e rai yasa ban sake magana ba har ya gama cin abincin ya kwashe komai ya Kai kitchen. Ya dawo ya taimaka min na Mik'e muka Shige d'akin mu. Koda ba kallonsa nake ba idona na kansa Yana fitowa daga wanka ya kashe wayarsa ya jefa a side drawer ya Kwanta. Nima nayi Shirin kwanciya da maganganu a bakina amma akan dole na hakura na kwanta a gefensa. Ya mirgino kusa dani,muka faranta wa juna bana iya kwanciya ba tare da nayi wanka ba a dadafe nayi wanka sabida baccin daya cika idona Ina kwanciya bacci yayi awon gaba dani. A zababben ciwon Mara ne ya tasheni daga baccin daya daukeni Damko mahfuz nayi Ina sallati Dan ciwon maran haihu daban yake kamar yanda ake bamu labari nasan haihuwa zanyi A gigice ya mik'e Yana tambaya ta lafiya Dak'yar na hada Masa kalmar haihuwa zanyi. Wani irin dirowa yyi daga Kan gado ya kunna fitilar d'akin ya kalli agogo karfe uku da minti ashirin "Bari na leka gidan Hamisu ya taimaka min da aron motarsa Ina kayan naki yake" "Mummy ta riga da hade min shi waje daya kayiwa Zainab magana na karashe Ina Kara sallati dan ciwon gadan gadan ba kaukautawa ga wani abu Mai dumi danaji Yana bin kafata. Mahfuz shi ya taimaka min na saka Riga da zani hannunsa sakale a kuguna kamar Mai koyan tafiya mukayi wajen da Hamisu mijin mmn iman ke jiranmu dan cewa yayi shi zai kaimu daga shi har matarsa suna da balain kirki sun san Kuma darajar makota. Bansan sanda ma aka iso asibiti ba ban iya tafiya ba sai gado suka kawo da taimakon mahfuz suka dorani sukayi d'akin haihuwa dani zainab na biye dani Mahfuz sai sannu yake min hankalinsa duk a tashe. Da shigar mu d'akin da haihuwata baifi minti ashirin ba. Duk Wanda bai haihu ba ba lailai yasan darajar mahaifiyarsa ba Allah ya saka wa iyayenmu da Aljannatul firdausi banyi doguwar nakuda ba amma naci ubana bayana Kamar baa jikina yake ba. Sai da suka gyarani Suka gyara yarinya da ta d'auko kamani na ba Inda ta baroni amma bata kaini haske ba da alama hasken babanta ta d'auko ido kawai na zuba Mata Ina Jin kaunarta har a cikin raina. Muryar mahfuz danaji akaina yasa na d'auke idona daga kanta "Sannu Lubna sannu da k'ok'ari wanan diyar tawa ta baki wahala" Yace tare da daukarta yana murmushi. Nima murmushin na sakar masa. Bakinsa ya kafa a kunnenta Ina kallonsa ya gama ya kwantar da ita a gefena Yana "Sunanki na saka mata Allah ya Raya mana ita sai ki zab'a mata sunan da zamu ringa kiranta dashi" Har ga Allah naji dadi a raina ban manta da Addu'a mai nakuda karbabiya ce hakane yasa na zage nayi addua Allah ya raba mahfuz da tsinaniyar budurwar sa dana tsana tamkar mutuwata. Karfe bakwai na safe aka sallamo mu. Da taimakon kanwar mahaifiyata nayi wanka tayi wa mimi wanka sunan da za'a ringa kiranta dashi,baccin gajiya yayi awon gaba dani duk da ana ta tururwa shigowa yimin barka. Kukan da Mimi keyi yasa na bud'e idona babu ma ruwan nono haka Aunty Sa'a tace na bata no-no tana fita sai ga mahfuz ya shigo sai da ya gama tsokanata yake tambayar Koda wani
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26